’Yan bindiga sun kashe makiyaya 2, sun sace shanu 320 a Kaduna
Published: 29th, May 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga sun kashe wasu makiyaya biyu da suka haɗa da: Mudda Shannon da Suleiman Bello, yayin da suka raunata ɗaya a ƙauyen Kurmin Lemu da ke ƙaramar hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.
Wani ɗan unguwar Kurim Lemu mai suna Shuaibu Ibrahim ya ce, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 12:07 na tsakar dare.
Ya ce, ’yan bindigar da suka zo adadi mai yawa tare miyagun makamai sun mamaye sansanin makiyayan inda suka buɗe wuta, inda suka kashe biyu daga cikin makiyayan nan take.
Ya ce, ɗaya daga cikin makiyayan ya tsallake rijiya da baya, amma ya samu raunukan harbin bindiga, inda ya ce ’yan bindigar sun je kai tsaye inda shanun ke da sansani suka kwashe su zuwa cikin dajin.
Ibrahim, ya ce daga baya an kai makiyayin da suka jikkata zuwa asibiti a garin Kagarko, inda yake jinya, kamar yadda ya ce an sanar da sojojin da ke Kagarko.
“An sanar da wasu sojojin da ke Kagarko, tun kafin su isa sansanin ’yan fashin sun tsere da shanun,” in ji shi.
Wani shugaban unguwar yankin da ya nemi a sakaya sunansa, shi ma ya tabbatar wa wakilinmu afkuwar lamarin ta wayar tarho.
Ya ce, ya samu rahoto daga ɗaya daga cikin shugabannin makiyaya na unguwar cewa ’yan bindiga sun kai hari sansanin makiyaya tare da kashe mutum biyu.
“Da safiyar yau ma na samu rahoto daga wani basaraken Fulani daga ƙauyen Kurmin Lemu cewa, wasu ’yan bindiga sun kai hari sansanin makiyaya inda suka kashe wasu Fulani biyu sannan suka yi awon gaba da shanunsu.” In ji shi.
Shugaban Unguwar ya bayyana cewa, ya kuma sanar da sojojin game da harin, duk da cewa ya ce an binne gawarwakin makiyayan biyu da suka mutu.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur ya zuwa yanzu bai tabbatar da faruwar lamarin ba, domin har zuwa lokacin da ake haɗa rahoton bai amsa kiran da aka yi masa ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kagarko Makiyaya yan bindiga sun
এছাড়াও পড়ুন:
New York Times: Harin A Sansanin Udaidai Ya Jaza Wa Amurka Asarar Dala Miliyan 111
Mujallar New York Times ta Amruka ta ce, harin da Iran ta kai wa sansanin sojan Amurka na Udaid, ya jazawa Amurkan asarar kudin da sun kai dala miliyan 111.
Mujallar ta kuma ce; harin ya sa Amurka ta koyi darussan akan abinda zai iya faruwa idan har fada ya barke a tsakaninta da China ko Korea Ta Arewa.