HausaTv:
2025-05-29@17:46:54 GMT

Trump Ya Gargadi Natanyahu Kan Kokarin Hana Tattaunawa Da Iran Tafiya

Published: 28th, May 2025 GMT

Shugaban kasar Amurka Donal Trump a tattaunawa ta wayar tarho da firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bukace shi ya daina shiha a cikin tattaunawar da Amurka take da JMI. Kafin haka dai firai ministan ya sha barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran a dai-dai lokacinda ake tattaunawar.

Wanda kuma yake tasiri a cikin abubuwan da ake tattaunawa tsakanin kasashen biyu.

Sishshigin da HKI suna zama manya-manyan labarai a kafafen yada labarai na duniya, wanda kuma yakan sa JMI ta maida martani. Don haka kutsawar da HKI take yi yana rikita tattaunawar, wasu suna fadar cewa HKI ce take fadar abinda wakilin Amurka zai fada a tattaunawar.

Ya zuwa yanzu dai Washington da Tel Aviv suna da sabanin kan yadda zasu yi mu’amala da iran a wannan tattaunawar. HKI bata son a yarjewa kasar Iran ta tashe Makamashin Uranium ko kadan. A yayinda Amurka kuma tana son ta tabbatar da

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Batun Dakatar Da Sarrafa Uranium Ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta daina sarrafa sinadarin Uranium a kowane hali ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya tabbatar a wata hira da tashar CNN ta Amurka cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da hakkinta na tace sinadarin Uranium a kowane hali ba.

A yayin da yake mayar da martani game da kyakkyawan fata na shugaban Amurka Donald Trump game da shawarwarin nukiliyar da aka yi tsakanin gwamnatinsa da Iran da kuma yadda yake kallon ci gaban da aka cimma, Baqa’i ya ce: Idan manufar Amurka ita ce tabbatar da cewa shirin makamashin nukiliyar Iran ba zata yi amfani da shi wajen karfin soji ba, to yana ganin za a iya cimma hakan cikin sauki. To amma idan har Amurka tana son tauye wa Iraniyawa ‘yancinsu na samun cikakken fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya da lumana ne, to yana ganin hakan zai zama babbar matsala, ta yadda Iran za ta kalubalanci dukkan tsarin.

A lokacin da wakilin tashar CNN ya tambaye shi: Shin ko suna tsammanin gwamnatin Trump da mai shiga tsakaninta, Witkoff, sun gane kuma sun fahimci hakan? Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya mayar da martani da cewa: Kasancewar Iran tana ci gaba da tattaunawa ya zuwa yanzu tana nufin cewa ta san akwai wani matakin fahimtar da Iran ba za ta iya ba a kowane irin yanayi ta yi watsi da haƙƙinta na mallakar fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya da lumana da suka haɗa da inganta sinadarin Uranium.

Amurka

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Rashin Ɗaukar Wani Maniyyaci Ya Hana Jirgi Tafiya Har Sai Da Ya Dawo Ya Ɗauke Shi
  • Shugaban  Iran na ziyarar aiki a kasar Oman
  • Amurka za ta hana ‘’visa’’ ga daliban dake sukanta a shafukan sada zumunta
  • Araghchi: “Ba ma wasa game da batun inganta uranium, wanda hakkin al’ummar Iran ne”
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Yayi Tir Da Jakadan Burtaniya A Amurka Dangane Da Tashe Uranim A Kasar
  • Kasar Ireland Ta Yi Dokar Hana Shigar Da Kayan Da Aka Kera A ” Isra’ila” Cikinta
  •  Arakci: Idan Birtaniya Ta Ci Gaba Da Batun Dakatar Da Tace Uranium A Iran, Za A Dakatar Da Tattaunawa Da Ita
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Batun Dakatar Da Sarrafa Uranium Ba
  • Ko Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Trump Ya Gujewa Yaki Da Yemen Har Ya Kai Ga Fusata Kawayen Amurka