Kungiyar agaji ta red crescent ta iran da kuma kungiyar red cross ta kasar Saliyo sun cimma yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu.

An cimma wannan ne a yayin ziyarar da babban daraktan kula da lafiya na kungiyar agaji ta Red Crescent na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai Saliyo tare da gudanar da tarurruka da dama da shugaban kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar.

Bayan taron, an rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kungiyar agaji ta Red Crescent ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kungiyar agaji ta Red Cross ta Saliyo a ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Saliyo.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kungiyar agaji ta Red

এছাড়াও পড়ুন:

Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji, da shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Huning, sun gana da shugaban majalisar dattijan kasar Madagascar Richard Ravalomanana.

Yayin ganawar, Zhao Leji ya bayyana cewa, Sin tana fatan yin kokari tare da Madagascar, don sa kaimi ga raya hadin gwiwa, da sada zumunta a tsakaninsu, da samar da gudummawa ga raya kyakkyawar makomar Sin da Afirka a sabon zamani. Kana yana fatan hukumomin kafa dokoki na kasashen biyu, za su kara yin mu’amala, da hadin gwiwa da juna, don taimakawa wajen raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Madagascar a dukkan fannoni.

Yayin ganawar tsakanin Wang Huning da Ravalomanana, Wang ya bayyana cewa, Sin da Madagascar hakikanin abokan juna ne, yayin da ake zamanintar da kasashen. Kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, na fatan yin mu’amala tare da majalisar dattijai ta kasar Madagascar, wajen taimakawa raya dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, Ravalomanana ya bayyana cewa, majalisar dattijan kasar Madagascar, na fatan yin kokari tare da kasar Sin, wajen inganta mu’amala a tsakanin hukumomin kafa dokokin kasashen biyu, don sa kaimi ga raya hadin gwiwar kasashen biyu, a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da zuba jari, da harkokin kananan hukumomi kasar da sauransu. Kana yana fatan kara yin mu’amala da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, a fannin sarrafa harkokin kasa, da kuma sa kaimi ga daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masu Zuba Jari Na Kasa Da Kasa Sun Gamsu Zuba Jari A Sin Dama Ce Ta Cimma Nasarar More Riba A Nan Gaba
  • Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Uranium A Cikin Kasarta
  • Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Nukiliyar Iran Ya Yi Kama Da Tabuwa
  • Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
  •  Kungiyar Malaman Musulmi Ta Yi Fatawar Wajabcin Kawo Karshen Killace Gaza
  • Fizishkiyan: Batun Kare Hakkin Bil’adama Ba Komai Ba Ne Sai Karya
  • NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Ministocin Tsaron kasashen Rasha Da JMI Sun Hadu A Birnin Mosco