Ministan Harkokin Wajen Iran Yayi Tir Da Jakadan Burtaniya A Amurka Dangane Da Tashe Uranim A Kasar
Published: 28th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya tir da kalaman jakadan Burtaniya a Washington, Peter Mandelson, wanda yayi kira ga Amurka kada ta taba barin Iran ta tashe makamashin Uranium a cikin kasar. Ministan ya kara da cewa Mandelson yana son ya karkatar da tattaunawan da Iran take da Amurka.
Ya kuma kara da cewa Iran ce take sanar da kasashen turai yadda tattaunawa tsakanin Amurka da ita ke tafiya, tun Amurka ta waresu daga tattaunawar. Yace, idan har haka ne tunanin kasar Burtaniya wacce take cikin kasashen da suka sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu, yana ganin mai yuwa Iran ta dakatar da sanar da su abubuwan da ke tafiya a tattaunawar.
Ya zuwa zagaye har 5 wadanda Amurka da Iran suka tattaunawa dangane da shirin Nukliya na Iran dai, Iran ta nuna mata cewa hanata tace uranium a cikin gida, jan layi ne wanda ba zata amince da shi ba, kuma ya sabawa yarjeniyar NPT wacce ta bawa Iran wannan damar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi: “Ba ma wasa game da batun inganta uranium, wanda hakkin al’ummar Iran ne”
Ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ba za ta amince da duk wata tattaunawa kan dakatar da shirinta na inganta makamashin Uranium gaba daya ba.
Ya bayyana hakan ne a gefen ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Oman, inda ya jaddada cewa, bai kamata tattaunawa da Amurka za ta hada da batun ba wanda Tehran ba za a amince da shi ba.
Araghchi ya ce, ana ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma batun tace uranium shi ne ya kasance babban abin da ake samun sabani.
Ya kuma kara da cewa, an yi shawarwari da ministan harkokin wajen Oman game da shirya wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da Amurka.
Ministan ya jaddada cewa Iran na daukar tace sinadarin Uranium a matsayin wani hakki na kasa wanda ba za’a iya tauye mata ba, kamar yadda yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta tanada.