A kwanan baya, tsohuwar firaministar kasar New Zealand, Madam Jennifer Shipley, ta yi hira da wakilin CMG, inda ta ce, ya dace a koyi ingantattun dabarun kasar Sin a fannin raya kasa.

Ta ce yadda kasar Sin ta gabatar da shawarar tabbatar da ci gaban duniya, da bai wa sauran kasashe dabaru da fasahohin da ta samu na da ma’ana matuka.

Saboda kasar tana kan gaba a duniya, a fannin raya al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

A cewar Madam Shipley, ya kamata a dora muhimmanci kan basirar kasar Sin, saboda an samu isassun shaidun dake nuna cewa, idan an yi amfani da dabarun Sin yadda ya kamata, to, za a samu nasarar raya aikin ilimi, da samar da guraben aikin yi, da rage talauci, da kyautata yanayin rayuwar jama’a.

Sa’an nan, dangane da shawarar hadin gwiwa a kokarin raya “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar, Madam Shipley ta ce, burin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya sanya gaba, na hade nahiyoyi daban daban ta hanyoyin sufuri daban daban, wata babbar gudunmowa ce ga ci gaban duniya. Wannan buri ya bullo da kyakkyawan tunani kan muhimmancin samar da taimako ga sauran mutane, yayin da ake kokarin raya kai, in ji Madam Shipley. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa, wata gobara ta ƙone wani shagon Adidas Sports da ke cikin rukunin babban kantin nan na sayar da kayayyaki na Jabi Lake Mall, Abuja da tsakar daren Alhamis.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shagon ne kaɗai gobarar ta shafa.

An kuma samu rahoton cewa, an baza jami’an kashe gobara daga Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da na Kamfanin Berger da na hukumar kashe gobara ta Abuja da kuma jami’an ’yan sanda zuwa wurin.

Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29

A lokacin da Wakilin Daily Trust ya kai ziyara da safe zuwa wurin, an shawo kan gobarar.

Wani ma’aikaci a shagon ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na tsakar daren ranar Alhamis.

Ya ce, ba a samu asarar rai ba a wurin. Ya kuma tabbatar da cewa, “Shagon sayar da kayan Wasannin Adidas ne kawai gobarar ta shafa.”

Mai magana da yawun Hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya, Ibrahim Mohammad, ya tabbatarwa da majiyar da faruwar lamarin, amma ya ce ƙarama ce.

Ya ce, an shawo kan lamarin kuma an dawo da zaman lafiya.

Ita ma da take mayar da martani, kakakin rundunar ’yan sandan Birnin Tarayya, Josephine Adeh ta ce an tura jami’an ’yan sanda wurin da lamarin ya faru domin kare yankin da kuma hana sace-sacen jama’a.

“Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:40 na asubahi, nan take muka tura mutanenmu wurin domin su tsare wurin da kuma hana duk wani abu da ya saɓa wa zaman lafiya,” in ji ta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
  • Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya
  • Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja
  • Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata