Yahudawan Sahyoniyya Sun Shiga Masallacin Al-Aksa Tare Da Rakiyar Sojoji
Published: 27th, May 2025 GMT
Duk tare da yakin da suke fafatawa a Gaza, dimbin yahudawan sahyoniyya masu bauta sun kutsa cikin masallacin Al-aksa da ke birnin Qudus inda suka gudanar da bukukuwan addinu a jiya Litinin.
Shafin yanar Gizo na labarai ‘Arab News’ ya bayyana cewa, bakin na addini, farin ciki ne da kwace gabacin birnin Qudus daga hannun falasdinawa a yakin shekara 1967 tsakanin yahudawan da kuma larabawa.
Yahudawan dai su na ganin dukkan birnin Qudus wanda ya hada har da inda masallacin Al-aksa yake mallakinsu ne kuma su na da shirin rusa masallacin don gina wurin bautansu a inda masallacin yake.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 30 A Katsina
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp