Aminiya:
2025-09-17@23:15:45 GMT

Mutanen da suka rasu a ambaliyyar ruwa a Neja sun ƙaru zuwa 151

Published: 31st, May 2025 GMT

Adadin mutanen da suka mutu a mummunar ibtila’in ambaliya a Jihar Neja ya karu zuwa mutum 151.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta sanar cewa mutane 11 sun jikkata, yayin da mutane 3,018 suka rasa matsuguninsu a ibtila’in na ƙaramar hukumar Mokwa a safiyar Asabar.

Kakakin hukumar, Ibrahim Hussaini, ya bayyana cewa ambaliyar ta shafi gidaje 265 da kuma magidanta 503.

Ya ƙara da cewa yankuna uku, da suka hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, sun nutse sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na tsawon sa’o’i da dare a ranar Laraba.

Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno

Wannan lamari ya faru ne watanni biyar bayan Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya sanar da cewa jihar ta samu tallafin dala miliyan 10 daga Bankin Duniya don dakile zaizayar ƙasa a wasu sassan Mokwa.

Gwamnan ya ce an tantance kwararrun ’yan kwangila don gudanar da aikin.

A ranar Juma’a, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a yayin miƙa ta’aziyyarsa, ya umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen aikin ceto da agaji a wuraren da abin ya shafa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliya Mokwa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.

Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.

Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.

A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.

“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.

Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.

Tinubu ya kuma yaba wa  masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.

Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.

Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.

Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.

 

Daga Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000
  • Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250  a Jami’ar Ilorin