Ƙungiyar Gwamnoni Sun Yi Ta’aziya Kan Rasuwar Ƴan Wasan Kano 21
Published: 31st, May 2025 GMT
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin ciki da alhini kan mummunan haɗarin mota da ya yi ajalin wasu ‘yan wasa daga jihar Kano, yayin da suke dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala a jihar Ogun.
Shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya fitar da wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a yau Asabar, yana mai miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da gwamnatin jihar Kano.
“Muna miƙa ta’aziyyar ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar Kano da kuma ɗaukacin ma’abota wasanni a faɗin kasar nan,” in ji sanarwar.
Gwamna AbdulRazaq ya ƙara da cewa: “Muna rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansu da rahama, Ya kuma ba da haƙura da ƙarfin gwuiwa ga iyalansu da duk wanda abin ya shafa a wannan lokaci mai wahala.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Wasa Yan wasan Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
A yau, 17 ga watan Satumba, Shugaba Tinubu ya ɗage dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba wa al’ummar jihar Ribas biyo bayan rashin jituwa da yaƙi ci yaƙi cinyewa da ya dabaibaye ɓangaren zartarwa da na dokokin jihar. Cikakken bayani na nan tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp