Kofin Duniya: Kasar Saudiyya Za Ta Sassauta Dokar Hana Shan Giya A Wuraren Yawon Bude Ido 600
Published: 26th, May 2025 GMT
A cewar jami’ai, za’a tsara yadda tsarin fitar da barasar zai kasance ta hanyar tabbatar da cewar an ba da horo ga masu sayar da ita da kuma basu takardar lasisin sayar da barasar. Hakazalika, za a tsaurara ka’idoji akan sayar da barasa a kasar, gwamnati ta jaddada cewa ana gabatar da sauye-sauyen ne cikin taka-tsantsan tare da kula da al’adun al’ummar kasar.
“Manufar ita ce, maraba da duniya ba tare da rasa asalin al’adu ba, sanya Saudiyya a matsayin mai ci gaba, duk da haka mai mutunta taswirar yawon shakatawa na duniya,” in ji hukumomin Saudiyya a cikin wata sanarwa.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Saudiyya ke neman yin gogayya da kasashe makwabta kamar Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain, inda a bisa ka’ida ake samun barasa a wuraren yawon bude ido.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp