Koshin Lafiyar Yaran Kasar Sin Na Kara Inganta
Published: 31st, May 2025 GMT
Babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarun baya bayan nan koshin lafiyar yaran kasar Sin na kara inganta. Jami’ar wadda ta bayyana hakan ga wani taron manema labarai a yau, ta ce a shekarar 2024, alkaluman mace-macen jarirai a kasar ya ragu zuwa jariri hudu cikin duk jarirai 1000, yayin da na yara ‘yan kasa da shekaru biyar ya ragu zuwa yara 5.
Shen Haiping ta kara da cewa, idan aka nazarci wadannan alkaluma, za a ga cewa cikin sama da shekaru goma da suka gabata, a duk shekara, matsakaicin adadin mace-macen jarirai a Sin ya ragu zuwa matsayi na uku a duniya, kana adadin mace-macen yara ‘yan kasa da shekaru biyar a kasar shi ma ya ragu zuwa matsayi na hudu a duniya, musamman cikin jerin kasashe 53 dake sama-sama a matsakaicin samun kudin shigar al’ummunsu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ya ragu zuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Libya Ta Tasa Keyar Baƙin Haure Yan Kasar Sudan 700 Zuwa Kasarsu
Gwamnatin Libya ta tasa keya daruruwan baƙin haure ‘yan ƙasar Sudan 700 zuwa ƙasarsu da yaƙi ya ɗaiɗaita, A cewar mahukuntan, waɗannan mutanen sun yi hijira zuwa Libya ne domin gujewa yaƙi da talauci, inda suke neman hanyar tsallakawa zuwa Turai.
A cewar huƙumar kula da baƙin haure, an kori mutane 700 daga Libya da aka kama a tsakiya da kudu maso gabashin ƙasar, inda aka tura su zuwa Sudan a ranar Juma’ar da ta gabata ta ƙasa.
Bayanin ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda aka korar na ɗauke da cututtuka masu yaɗuwa kamar su hepatitis da cuta mai karya garkuwar jiki, wasu kuma an tura su ne saboda laifuffuka ko kuma dalilan tsaro.
Korar ta zo ne a lokacin da mahuƙuntan ke ci gaba da yaƙi da safarar mutane a gabashin Libya, wanda ke ƙarƙashin ikon kwamandan sojoji Khalifa Hiftar.
A makon da ya gabata, masu tsaron gaɓar teku a gabashin Libya sun kame wani jirgin ruwa da ke ɗauke da baƙin haure 80 da ke neman zuwa ƙasashen ƙetare, a gabashin birnin Tobruk.
Yaƙin da hukumomin ke yi sun haɗa da kai hare-hare kan wuraren da ake safarar mutane a gabashi da kudancin Libya. A farkon wannan watan, an ƙwato baƙin haure ‘yan Sudan 104, ciki har da mata da yara, da aka tsare a gidan da ake tara mutane da ake fataucin su a birnin Ajdabiya, mai nisan kilomita 800 daga babban birnin Tripoli, a cewar ƴan sa kai na yankin.
Libya ta zama hanyar wucewa ga mutanen da ke guje wa yaƙi da talauci a yankunan gabas ta tsakiya da Afirka, inda suke neman rayuwa mai kyau a Turai.
Masu safarar mutane sun ci gajiyar rashin kwanciyar hankali a Libya tsawon shekaru goma, inda suke shigar da baƙin haure ta iyakokin ƙasar da suka haɗa da ƙasashen Chadi da Nijar da Sudan da Masar da Aljeriya da kuma Tunisiya.