Sin Za Ta Kara Zurfafa Dunkule Rawar Yankunan Raya Tattalin Arziki Da Fasahohi A Fannin Janyo Jarin Waje
Published: 28th, May 2025 GMT
Mataimakin ministan ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin Ling Ji, ya ce gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa dunkule rawar da yankunan raya tattalin arziki da fasahohi mallakin gwamnati ke takawa, a fannin janyo jarin waje, a gabar da kasar ke kara fadada matakanta na bude kofa ga kasashen waje.
Ling Ji, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan yayin wani taron manema labarai da ya gudana, ya ce a halin yanzu yanayin hada-hadar tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa na cikin wani halin ha’ula’i, kuma sakamakon haka, matsayar yankunan raya tattalin arziki da fasahohi na muhimmin jigon daidaita hada-hadar cinikayyar waje, da zuba jari na kara bayyana a fili.
Ya zuwa shekarar 2024, adadin irin wadannan yankuna ya kai 232 a sassan kasar Sin, inda suka samar da darajar GDPn da ya kai kudin Sin tiriliyan 16.9, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.35. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Ta Kammala Samar Da Fasfo Sama Da 200,000 Da Suka Yi Jinkiri
Kan batun gyaran gidajen yari kuwa, ministan ya nuna damuwa kan halin da gidan gyaran hali ke ciki, inda ya bayyana cewa fiye da fursunoni 4,000 na tsare ne saboda gazawarsu na biyan tara kamar Naira 50,000.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp