‘Yar Majalisar Dokokin Ireland Ta Yi Suka Kan Shugabannin Turai Tare Da Neman Afuwa Daga Falasdinawa
Published: 25th, May 2025 GMT
‘Yar majalisar dokokin Ireland ta yi kakkausar suka kan shugabannin Turai tare da neman afuwa daga Falasdinawa
Tana jaddada cewa: Muggan makaman gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da lakume rayukan fararen hula a zirin Gaza. Sannan a wani sabon kisan kiyashi, an kashe Falasdinawa 7 a wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza.
A wani kisan kiyashi kuma jami’an tsaron farar hula a Gaza sun sanar da mutuwar yara tara da suka kone kurmus a wani harin da sojoji mamayar Isra’ila suka kai kan Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza da aka killace. An kuma kashe wani Bafalasdine tare da raunata wasu a wani harin da aka kai kan wata tanti da ke dauke da ‘yan gudun hijira a yankin Al-Mawasi da ke yammacin Khan Yunis.
A wani bangare na yakin yunwa, ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar da mutuwar wani yaro sakamakon yunwa da kuma killace yankin da aka yi domin hana aikewa da kayan agajin jin kai. A baya dai ma’aikatar lafiyar ta Gaza ta bayyana cewa: Yara da tsofaffi 29 ne suka mutu sakamakon matsalar yunwa, sannan kuma wasu dubbai na cikin hadarin mutuwa ta dalilin haka.
Hukumar samar da abinci ta duniya ta tabbatar da cewa dubun dubatar yara na fuskantar matsanancin rashin abinci mai gina jiki. Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya kuma yi gargadin cewa jarirai 14,000 na iya mutuwa ba tare da shigar da agaji yankin ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu
Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan sahayoniyya kan kasar Iran
Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren.
Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari.
A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a ranar talata mai taken “Hanyar Haramtacciyar kasar Isra’ila kan Iran: Abubuwan da za a samu a nan gaba,” Sajjadpour, yayin da yake magana kan halaye da matsayin Turai a yakin kwanaki 12 da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Iran, ya ce: “Turai na goyon bayan gwqwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila a kodayaushe, kuma shiru ko goyon bayan da wasu kasashen Turai suka yi kan zaluncin Isra’ila za su kasance da sun mummunar tasiri a cikin zukatan Iraniyawa.”