Likitocin Iran Suna Ci Gaba Da Samun Nasara Wajen Magance Matsalar Kurmanta Da Na Bebantaka
Published: 31st, May 2025 GMT
Likitocin Iran sun yi bikin murnar nasarar da ta samu na dasa na’urar dawo da ji da inganta shi ga masu matsalar kurmantaka da raunin ji a lardin Khuzestan na kasar
Ƙaunar sana’a, dagewa, da sadaukarwa sune sirrin nasarar kowane aiki da hidimar jin kai. Waɗannan kalaman ne Farfesa Nadir Al-Saki ya fara bude jawabinsa a yayin bikin nasarar da aka yi na aikin tiyatar dashen na’urar magance matsalar Rashin ji da rauninsa sau 1,500 a lardin Khuzestan dake kudu maso yammacin ƙasar.
Bikin dai ya samu halartar likitoci da ma’aikatan jinya da yara da dama wadanda aka yi musu aikin tiyata cikin nasara, tiyatar da ta ba su damar bayyana tunaninsu da yadda suke ji a fagen rayuwa.
Hanyoyin dasa na’urar a lardin sun zama wani dandamali mai karfi ga marasa lafiya na kasashen waje, inda marasa lafiya 36 daga kasashen Iraki, Oman, Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkey da Afghanistan suka samu waɗannan ni’imomi a fagen rayuwar bil-Adama.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.
Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA