Aminiya:
2025-09-17@23:17:12 GMT

Zazzaɓin Lassa da sanƙarau ya kashe mutum 366 a jihohi 24 – NCDC

Published: 30th, May 2025 GMT

Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutane 366 a sakamakon zazzaɓin Lassa da cutar sanƙarau a ƙasar, lamarin da aka bayyana da ƙalubalen kiwon lafiyar ga al’umma sanadin waɗannan cututtuka.

Daga ranar 1 ga Janairu zuwa 18 ga Mayu, 2025, NCDC ta tabbatar da ɓullar cutar zazzaɓin Lassa guda 733 daga mutane 5,118 da ake zargin sun kamu da cutar a faɗin jihohi 18 da ƙananan hukumomi 95.

Shekaru 6: Don amfanin matasa mun inganta ilimi da noma — Gwamna Buni  An gano gawar direba a cikin mota a Bayelsa

A cikin wannan lokacin, ƙasar ta sami rahoton mutuwar mutane 141 masu nasaba da zazzaɓin Lassa, wanda ke nuna adadin waɗanda suka mutu ya kai kashi 19.2 cikin 100.

A gefe guda kuma, tsakanin 30 ga Satumba, 2024, zuwa 6 ga Afrilu, 2025, NCDC ta tabbatar da kamuwa da cutar sankarau 192 daga cikin 2,911 da ake zargi da kamuwa da cutar da ta shafi jihohi 24 da ƙananan hukumomi 173. A wannan lokacin, cutar sankarau ta yi sanadiyar mutuwar mutane 225.

Dangane da sabon rahoton yanayin zazzaɓin Lassa da NCDC ta fitar, an samu ƙaruwar masu kamuwa da cutar a cikin mako na 20 na annobar cutar, inda aka samu ƙarin mutane 13 da suka kamu da cutar a jihohin Edo da Ondo da Benue – daga uku kacal a makon da ya gabata.

“A dunƙule a cikin mako na 20, a 2025, an samu rahoton mutuwar mutane 141 tare da adadin waɗanda suka mutu ya kai kashi 19.2 cikin 100, wanda ya zarce wannan lokacin a shekarar 2024 (kashi 18.3 cikin 100). A cikin duka adadin don a 2025, jihohi 18 sun sami aƙalla ɗaya aka tabbatar a cikin ƙananan hukumomi 95, “in ji rahoton.

Ya kuma bayyana cewa kashi 72 cikin 100 na waɗanda aka tabbatar sun kamu da zazzaɓin Lassa sun fito ne daga jihohi uku: Ondo (kashi 30 cikin 100), Bauchi (kashi 25 cikin 100), da Edo (kashi 17 cikin 100). Sauran kashi 28 cikin 100 na ɓullar cutar sun bazu a wasu jihohi 15.

Yawan shekarun mutanen da suka fi shafa shi ne shekaru 21 zuwa 30, tare da matsakaicin shekaru 30.

Hukumar NCDC ta lura da raguwar waɗanda ake zargi da kuma tabbatar da kamuwa da cutar zazzaɓin Lassa idan aka kwatanta da na lokaci guda a cikin 2024. Ba a sami sabon kamuwa da cutar a tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya a cikin makon da ake nazari ba.

Don daidaita rahotannin, tsarin haɗin gwiwa da yawa na yaƙar kawar da zazzaɓin Lassa na ƙasa, a kowane matakai na aiki tuƙuru.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hukumar Yaki da Cutuka Masu Yaduwa NCDC zazzaɓin Lassa kamuwa da cutar mutuwar mutane

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano

Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano.

Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman.

Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono

Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar.

“Mun fara wannan shiri fiye da shekara guda da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai. Yanzu mun zo nan don fara na ɓangaren jarirai. Mu za mu biya kudin kulawar gaggawar yaran sannan mu tabbatar an kula da su har su samu ingantacciyar lafiya,” in ji Dr. Sikiru.

Ya kuma ce a karkashin shirin, yara da ke fama da matsalolin gaggawa kamar rashin numfashi, amosanin jini, cutar shawara da yaran da aka haifa bakwaini da ma cututtukan da ke buƙatar tiyata za su samu kulawa kyauta.

Ya ce asibitoci za su fara ba da kulawa da zarar an kawo yara, sannan su tura adadin kuɗin kula da yaran a kowanne mako ga NHIA don a biya su.

Daraktan ya kara da cewa duk yaran da ya sami kulawar gaggawar kuma, za a saka shi cikin shirin inshorar lafiya na NHIS, inda hukumar za ta ci gaba da biyan kudin inshorar don tabbatar da samun kulawar lafiya mai inganci.

“Kafin yaro ya ci gajiyar shirin, dole ne a tantance shi a a tabbatar yana da rauni da kuma ba zai iya biyan kuɗin asibiti ba. Haka nan dole ne yaro ya mallaki Lambar Shaida ta Kasa (NIN) don tabbatar da gaskiya da shigar da su cikin tsarin,” in ji shi.

Dr. Sikiru ya kuma ce, “Shiri ne kula da marasa lafiya cikin gaggawan. Da zarar sun zo, za a duba su. Asibitin sai ya turo mana jimillar adadin kudin, mu kuma mu biya.”

Ya ce wannan shiri wani bangare ne na kudurin gwamnatin tarayya na rage mace-macen jarirai da tabbatar da cewa babu yaron da ya rasa kulawar asibiti saboda rashin kudi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • Burkina Faso: Masu Ikirarin Jihadi Sun Kashe Fararen Hula 50 A Cikin Watanni Hudu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara