Aminiya:
2025-07-23@16:00:10 GMT

Maƙabarta mai shekaru 500 da ta koma maɓoyar ’yan daba 

Published: 31st, May 2025 GMT

Maƙabartar Kuka Bulukiya maƙabarta ce mai daɗaɗɗen tarihi a cikin ƙwaryar birnin Kano, wadda bayanai suka nuna an shafe sama da shekara 500 ana binne mamata a cikinta.

Wannan daɗaɗɗiyar maƙabarta tana da matuƙar muhimmanci musamman la’akari da yawan unguwannin da suka kewaye ta da yawan mutanen da aka binne a cikinta da kuma fitattun mutanen da suke kwance a cikinta.

Maƙabartar Kuka Bulkiya ta yi iyaka da unguwannin Dala da Madabo da Yalwa da Kwanar Taya da kuma Gwammaja, sa’annan akan kawo gawarwaki hatta daga unguwanni irin su Gwauron Dutse da Ƙulƙul da Dogon Nama da Madigawa da Sanka da Makafin Dala da dai sauran su.

Asali dai an sanya mata sunan Bulukiya ne saboda wata bishiyar kuka mai wannan sunan da take tsakiyarta. Tarihi ya nuna hatta Mujaddadi Shehu Usman ɗanfodiyo ya taɓa ziyartar maƙabartar inda ya yi wa mamata addu’a a ƙarƙashin bishiyar.

Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Borno Mun haramta liƙa hotuna ko rubutu marasa ma’ana a A-Daidaita-Sahu —El-Mustapha

Mamallakin tsohon kamfanin sufurin jiragen sama na Kabo Air, Jarman Kano, Marigayi Alhaji Muhammadu Adamu Ɗankabo, ne ya katange ta sama da shekaru 25 da suka shuɗe, lokacin yana raye, kuma shi ma a nan aka binne shi.

To sai dai duk da wannan tarin muhimmancin, a ’yan shekarun nan, wani sashe na maƙabartar ya zama kamar wata mafaka ta ’yan daba, masu yin ƙwacen waya da ma aikata fashi ga masu wucewa ta kusa da ita.

Sun sace allunan kabari da ƙarafan katangar maƙabarta

A yayin ziyarar da wakilinmu ya kai maƙabartar, ya gane wa idanunsa yadda aka ɓalle ƙarafan da suke jikin saman katangar, kuma an shaida masa cewa ɓata-garin ne suka sace ƙarafan. Bugu da ƙari, hatta allunan ƙarfe da ake rubuta sunan da kwanan watan rasuwar mamata a jikin ƙaburburansu, ɓata-garin ba su bari ba, sun yi awon gaba da su.

Ɗaya daga cikin masu haƙan ƙabari a maƙabartar, wanda bai amince a bayyana sunansa ba, ya shaida wa wakilinmu cewa, babbar matsalar da suke fuskanta ita ce ta tsaro, musamman la’akari da yadda ɓata-gari suke fakar numfashin masu wucewa ta kusa da ita suna yi musu ƙwace.

Ya ce akan ƙwace wa masu wucewa kuɗaɗe da wayoyi — har ma da ƙarafan da suka zagaye katangar maƙabartar. A cewarsa, “Lokacin da suka fi yin ƙwacen shi ne lokacin da sawu ya ɗauke, kamar wajen sallar Azahar saboda tsananin zafin rana, ko da daddare ko da sanyin safiya.

“Duk abin da suka samu a jikin mai wucewa daga kuɗi ko waya duk ƙwacewa suke yi. Har babur ɗin hawa an taɓa ƙwacewa a nan wajen. Galibi dai an fi yin ƙwacen nan ta ɓangaren katangar yamma, tsallaken Kwanar Taya, sai kuma nan kan titi.

“An sace yawancin ƙarafan katangar, kodayake ya ce sai da daddare suka fi zuwa ,saboda ai ba zai yiwu ido na ganin ido ba, kafin su cire wani zai gan su ya hana tun da ko ta ina akwai jama’a,” ” in ji ma’aikacin maƙabartar, wanda ya ce, ɓarayin sukan sace hatta allunan ƙaburbura, su sayar wa masu sana’ar gwan-gwan.

Ya ce adadin masu haƙar ƙabari a maƙabartar ya kai 31, amma mutum 16 daga cikinsu kaɗai ƙaramar Hukumar Dala take ba wa alawus. Amma su ma kusan wata huɗu ke nan ba a ba su ba.

Daga nan sai ya yi kira ga ƙaramar hukumar da ta dube su ta tallafa musu wajen biyan alawus ɗin.

Da muka tambaye shi ta yaya suke iya kula da iyalansu da abin da suke samu, sai ya ce galibi sai dai idan jama’a sun zo rufe mamaci sai su nemi taimako a wajensu, abin da aka samu na sadaka kuma sai su raba a tsakaninsu.

‘An ƙwace keken yaron da ya ziayrci ƙabarin mahaifiyarsa’

Shi ma wani daga cikin masu aikin hakan da shi ma bai amince a bayyana sunansa ba, ya ce akwai yaron da ya taɓa zuwa ziyara kabarin mahaifiyarsa da keke, amma ɓata-garin suka ƙwace masa keken. “Haka suka ƙwace keken suka tafi suka bar shi yana kuka, sam ba su da imani,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Ni ma akwai ranar da na zo ina aiki da safe, kawai sai na hango wani daga cikin ’yan daba ya laɓe a bayan wata bishiya a tsakiyar ƙaburbura da adda a hannunsa, sai ya yi min alamar in bar wajen za su yi wani aiki, dole haka na bar wajen tun da ba ni da makamin da ya fi nasa ballantana na hana shi.”

Ya ce da yake yawancin ɓata-garin ’yan unguwannin da ke maƙwabtaka da maƙabartar ne, sun san su a fuska, amma ba su cika yi wa masu haƙan kabarin ƙwacen ba, sun fi yi wa baƙi masu zuwa ziyara ko wucewa.

Na fi shekara 40 ina hakan ƙabari a nan — Malam Garba

A zantawarsa da wakilinmu, shugaban masu haƙan kabari da kuma kula da maƙabartar, Malam Garba Sa’adu, wanda ya ce ya shafe sama da shekaru 40 yana aiki a cikinta. Malam Garba ya shaida masa cwea abin takaici ne yadda ɓata-garin ke zuwa har kusa da maƙabarta suna aikata ta’asa ba tare da jin tsoron Allah ba.

Sai dai ya ce yanzu an samu sauƙin sace-sacen a sakamakon hoɓɓasar da mutanen unguwa da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu suka yi.

Daga nan sai ya yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wajen kai gudunmawar ƙasar ciko da birjin da za a yi amfani da su wajen cike wasu ƙaburburan da sukan rufta saboda ruwan damina.

Malam Garba ya kuma yi kira gare su da gwamnati da su taimaka wa maƙabartar da ma ma’aikatanta don su ci gaba da samun ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Wata 4 babu N5,000 da ake biyan mu a wata — Mai haƙan kabari

Ya kuma yi kira, musamman ga ƙaramar hukumar da maƙabartar take, wato Dala, da su taimaka wa masu aikin hakan domin kula da su.

“Ba a kula da mu da rayuwarmu yadda ya kamata gaskiya, ɗan abin da ake ba mu ƙalilan ne. A ce mutum da ’ya’ya da iyali yana bauta wa al’umma amma sama da shekaru 40 ba abin da gwamnati take yi mana. Wata huɗu ke nan yanzu ma ba a ba mu alawus ba. ɗubu hudu ce, kuma yanzu wata hudu ke nan ma ba a ba mu ba,” in ji Malam Garba.

Wani abokin aikinsa ya ce ko a kwanakin baya sun zauna da wakilan shugaban ƙaramar hukumar Dala, inda ya yi musu alƙawarin ƙarin alawus ɗin daga Naira 5,000 zuwa 10,000, amma har yanzu ba a fara aiwatarwa.

Aminiya ta tuntuɓi Ƙaramar Hukumar ta Dala don jin ta bakinta a kan batun alawus ɗin, sai dai duk ƙoƙarin wakilinmu na jin ta bakin Daraktan Ma’aikata da Gudanarwa na ƙaramar hukumar, Dauda Shehu Zakirai, ya ci tura.

Wakilin namu ya ziyarci je Daraktan amma bai same shi ba, ya kira shi a waya bai ɗaga ba, sa’annan bai amsa rubutaccen saƙon da wakilin namu ya tura masa ba, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Ba mu sani ba, amma za mu bincika — Kwamitin maƙabartu

A cewar mai magana da yawun kwamitin da aka ɗora wa alhakin kula da maƙabartu na jihar Kano, Aminu Yahaya Galadanci, babu wanda ya sanar da kwamitin nasu matsalolin Maƙabartar Kuka Bulukiya, don haka ba su san da su ba.

Sai dai ya yi alƙawarin kai ziyara maƙabartar da kansa don ganin halin da take ciki. A cewarsa, “Kwamitinmu ba shi da wakilci a kowacce maƙabartar da ke Kano, mutum 10 ne kawai a cikinsa. Ba zai yiwu a ce komai muna ciki ba, kullum buƙatarmu ga jama’a ita ce idan wani abu ya faru irin wannan su sanar da mu, sai mu bincika mu ɗauki mataki.

“Amma galibi sai dai mu ji ana ƙorafi a gidan rediyo amma ba a sanar da mu ba, duk da cewa mun bayar da lambobin waya da za a riƙa kawo mana ƙorafi. Amma dai wannan gaskiya ba mu sani ba, amma dai yau ɗin nan in Sha Allahu ni da kaina zan je na bincika domin ɗaukar matakin da ya dace,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan daba Ɓata gari Kuka Bulukiya ƙaramar hukumar da a maƙabartar da maƙabarta Malam Garba ɓata garin

এছাড়াও পড়ুন:

Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh

Kimanin mutum 16 sun rasa rayukansu a ranar Litinin bayan wani jirgin rundunar sojin sama ta Bangladesh ya fadi a cikin harabar wata makaranta a Dhaka, babban birnin kasar.

Haɗarin jirgin saman yaƙin ya kuma yi sanadin jikkatar gommai, wanda ya kasance guda daga cikin haɗɗura masu muni da ƙasar ta gani a baya-bayan nan a fannin jiragen sama.

Jihohin da za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Nijeriya — NiMet Ƙalubalen da ke tattare da sauya sunan jami’a

Wani mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na AFP da ke wurin ya ce ya ga jami’an kashe gobara suna kwasar daliban da suka jikkata yayin da sojoji ke taimakawa wajen zakulo mutane daga cikin baraguzan jirgin da ya fadi.

Fiye da mutane 100 ne suka jikkata a hadarin, inda akalla 83 ke karbar magani a asibitoci daban-daban, in ji wani jami’i a ofishin gwamnatin kasar, Muhammad Yunus.

Bayanai sun nuna cewa waɗanda suka jikkata mafi yawansu ɗalibai na karɓar kulawar likitoci, yayinda wasu yayi munin da sai anyi musu gagarumar tiyatar sauya hallita.

Jirgin na F-7 BJI da aka kera a kasar Sin ya tashi ne da karfe 1:06 na rana (07:06 GMT) kuma ya faɗi mintuna kaɗan bayan da aka saki ɗaliban daga ajujuwansu don fita tara a harabar makarantar mai suna Milestone School and College.

Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda iyayen ɗaliban suka isa filin makarantar a ƙiɗime, don neman yaransu, amma wasu anan suka ci karo da gawargwakin yaransu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Hafsan Sojin Iran Ya Ce: Iran Zata Sanya Duk Wanda Ya Dauki Matakin Wuce Gona Kanta Nadama
  • Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro
  • Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati 
  • Kamfanonin lantarki ya zu katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati 
  • Yunwa na ƙara tsanani a Arewa maso Gabashin Nijeriya — ICRC
  • Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
  • Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Gwamnatin Kano Ta Maida Gidan Marayu Zuwa Cibiyar Gyaran Mata Masu Shaye
  • Gwamna Radda Da Makarrabansa Na Samun Kulawa A Asibiti Bayan Hatsarin Mota A Hanyar Daura
  • MDD Ta Gargaɗi Isra’ila Kan Tilasta Wa Al’ummar Deir al-Balah Na Gaza Tashi