Sojojin Sudan Sun Fatattaki Dakarun Kai Daukin Gaggawa Daga Sansaninsu Da Ke Birnin Omdurman
Published: 27th, May 2025 GMT
Sojojin Sudan sun yi nasarar fatattakan ‘yan tawayen kasar na kungiyar Rapid Support Force daga sansanoninsu da ke kudancin Omdurman
Hukumomin sojin Sudan a birnin Omdurman na jihar Khartoum, sun sanar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun tsare sun bar makamai da alburusai da dama da suka hada da haramtattun makamai da aka hana amfani da su a dokokin kasa da kasa, bayan da suka sha kashi a yankin Al-Saliha da ke kudancin birnin.
Yakin baya- bayan nan da sojojin Sudan suka yi da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces a yankin Al-Saliha da ke kudancin Omdurman ba abu ne mai sauki ba. An kwashe sama da wata guda ana gwabza fada. Babban dalilin shi ne mallakar manyan makamai da Dakarun kai daukin gaggawa suka yi, wanda ya janyo bullar tambayoyi da dama kan yadda dakarun da ba su da isasshen horo don amfani da irin wadannan makaman za su iya mallakar su, sai dai idan suna samu goyon baya daga waje.
Suleiman Abdo Ali, kwamandan rundunar soja ta Takht Omdurman, ya ce: “Alhamdu lillahi, an fatattaki makiya sun bar kayan aikin soja, da a ce sun kasance sojoji ne na yau da kullun ko kuma sojoji ne masu manufa ko wata akida da su tsaya a fafata da su.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Dakarun kai daukin
এছাড়াও পড়ুন:
Tashin Hankali A Gaza Bayanda HKI Ta Bude Rumbun Ajiyar Kayakin Agaji A Rafah
Falasdinawa da dama ne suka ji rauni a jiya Talata a lokacinda yahudawan Sahyoniyya suka bude rumbunajiyar kayakin abinda ga Falasdinawa a garin Rafah na kudancin gaza.
Shafin yanar gizo na Afirka News ya bayyana cewa dubban Falasdinawa wadanda suka yi kwanaki 90 basu sami abinci ba saboda rufe kofar shiar da abinci zuwa gaza.
Wannan dai yana daga cikin walakanci mafi girma wanda sojojin HKI suka yiwa Falasdinawa a Gaza, tun bayan fara yakin. An kiyasta cewa falasdinawa kimani dubu 180 ne suka fito don karban agajin HKI da Amurka.
Sannan jiragen yakin HKI sun yi barin wuta a sama don tsorata falasdinawa masu neman agaji. A yayinda sojojin yahudawa suna harbi a sama don tsoratar da su. Duk da haka wasu sun dawo hannun rabbana basu sami abincin ba.