Aminiya:
2025-11-03@08:00:48 GMT

Faransa ta haramta shan sigari a cikin jama’a

Published: 30th, May 2025 GMT

Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a.

Kasar ta ce wuraren da haramcin ya shafa sun hada da makarantu da tashoshin mota ko na jirgi, wuraren shakatawa, wuraren wasanni ko kasuwanni saboda kada yara kanana su gani.

Yadda ambaliyar Neja ta ci mutum 12 ’yan gida daya NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025

Ministar Lafiya da Iyali na kasar, Catherine Vautrin ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ta ce, “Dole a daina shan sigari a wuraren da yara suke.

“’Yancin shan sigari ya kare ne a inda ’yancin yara na shakar tsaftatacciyar iska ya fara,” kamar yadda ministar ta shaida wa jaridar Ouest-France ta kasar.

Kazalika, dokar za ta hana dalibai shan sigari a gaban makarantu, kuma duk wanda aka samu ya karyata zai iya fuskantar hukuncin biyan tarar da ta kai Dala 154, kusan Naira 250,000 ke nan.

A cewar alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), fiye da kaso 35 cikin 100 na mutanen kasar Faransa na ta’ammali da sigari.

 

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Faransa Sigari shan sigari a

এছাড়াও পড়ুন:

UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza

Kakakin hukumar kula da kanana yaran ta majalisar dinkin duniya  tess ingram ta bayyana cewa yanayin da yara ke ciki a yankin gaza yayi muni sosai, inda sama da yara miliyan daya dake gaza suke bukatar taimakon gaggawa na ruwan sha da kuma abinci

Ingram ta fadi a wata hira da aka yi da ita cewa dubban yara a falasdinu suna kwana da yunwa kusan kowanne dare,  kuma akalla yara 650,000 ba su koma makaranta ba duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimamma a baya –bayan nan tsakanin bangarori biyu,

Har ila yau ta bayyana batun dakatar da bude wuta a matsayin labari mai kyau, da ya kawo karshen ci gaba da lugudan wuta da israila ke yi kowanne lokaci da ya ci rayukan dubban yara kanana, sai dai ta jaddada cewa yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba za ta wadatar ba dole ne sai an kawo karshen yunwa da kuma samar da ruwan sha ga sauran iyalai  yankin gaza.

A ranar 10 ga watan okotba ne yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta fara aiki a gaza  amma duk da haka yanayin da ake ciki ya kara tsananta baka iya zuwa wasu yankuna da dama a yankin saboda ci gaba da kasancewar sojojin isra’ila a wajen.

Isra’ila tana ci gaba da keta yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar Hamas, tana ci gaba da kai hare-hare da  harbe harbe kuma tana hana shigar da kayan agaji da ake bukata zuwa yankin na Gaza, kuma kashi 2 cikin 3 na adadin wadanda aka kashe mata ne da yara kanana.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta yi Watsi Da Zargin Da Amurka Tayi Mata Kan Batun Motocin Agaji A Gaza November 3, 2025 El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai November 3, 2025 Iran Ta Karbi Sako Kan Batun Komawa Teburin Tattaunawa Ba Kai Tsaye Ba November 3, 2025 Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan: Mayakan RSF Sun Kashe Mata 300 Da Yi Wa 25 Fyade A El Fasher November 3, 2025 Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne November 2, 2025 Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran November 2, 2025 Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani November 2, 2025 Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza November 2, 2025 Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza
  • Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan: Mayakan RSF Sun Kashe Mata 300 Da Yi Wa 25 Fyade A El Fasher
  • Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
  • Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda