An gano gawar direba a cikin mota a Bayelsa
Published: 30th, May 2025 GMT
An gano gawar wani direban da yake tuƙi ƙarƙashin kamfanin sufuri da har yanzu ba a tantance shi ba a yankin Samphino na Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.
Daily Trust ta ruwaito cewa, an gano gawar direban matashin mai matsakaicin shekaru da sanyin safiyar Juma’a a cikin motarsa a mahaɗar Samphino da ke unguwar Kpansia a unguwar Yenagoa.
Wasu shaidun gani da ido da mazauna wurin da suka gano mutumin a wurin, an bayyana cewa, sun sanarwa da jami’an tsaro lamarin inda suka yi gaggawar ɗaukar mataki a wajen tare da killace wurin.
Mazauna yankin sun ce mai yiwuwa wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne suka harbe direban, a yunƙurin ƙwace motarsa ko wasu kayayyaki masu daraja.
Kodayake har yanzu ba a samu cikakkun bayanai ba, rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun nuna cewa, mai yiwuwa maharan sun kira direban ne ta tikitin tafiya ta hanyar amfani da manhajar wayar salula ta Bolt, dabarar da ta ƙara nuna damuwa kan tsaron lafiyar direbobin da ke aiki da manhajar na direbobi a jihar.
Lamarin ya haifar da wani sabon tashin hankali a tsakanin mazauna garin da direbobin masu ɗaukar fasinja a Yenagoa, sa’o’i 24 bayan gwamnatin Jihar Bayelsa ta ba da gudummawar motocin sufuri aiki 31 ga jami’an tsaro daban-daban domin ƙarfafa ƙoƙarin yaƙi da miyagun ayyuka a faɗin jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Musa Muhammad, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
A ranar Alhamis ne Gwamna Douye Diri ya gabatar da sabbin motocin aiki guda 31 ga kwamandojin jami’an tsaro na jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bayelsa
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.
Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.
Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.
A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.
“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.
Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.
Tinubu ya kuma yaba wa masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.
Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.
Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.
Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.
Daga Bello Wakili