2025-05-24@13:03:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4117
«masu neman aikin gwamnati»:
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sallami ma’aikata da dama a majalisar tsaron kasar Amuka saboda gazawarsu wajen magance wasu al-amuran tsaro da siyasa a kasar. Tashar talabijin Ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Rauters yana cewa ma’aikatan maimakon su magance al-amuran tsaro da suka shafi tsaron kasa, sai sun zauna suna jiran abinda shugaban zai fada don su yi aiki a kansa. Labarin ya kara da cewa shugaban ya dauki wannan matakin ne don ya mika wasu ayyukansu ga Pentagon da FBI da wasu ma’aikatun tsaro don magance wasu matsaloli masu muhimmanci a cikin sauri.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Iran bata amince da kafa kasashe biyu a matsayin hanyar warware rikicin Falasdinawa ba, saboda kafa kasashe biyu ba zai bawa Falasdinawa hakkinsu ba saboda matukar akwai ikon da HKI take da shi a yakin Falasdinawa ba zasu taba samun hakkinsu ba. Bil’hasali ma kasashe biyu a fahintar mu zai kara wahalar da Falasdinawa ne fiye da hadda suke sha a halin yanzu. Ministan ya bayyana haka ne a lokacinda ya kai ziyara birnin Vatikan na kasar Italiya inda ya gana da Cardinal Pietro Parolin a jiya Jumma’a. Aragchi ya kara da cewa an dade ana maganar raba gardamar ta hanyar kasashen biyu. Al-hali ba wanda ya amince da kafa kasashen biyu...
Gwamnatin kasar Saudiya ta bukaci a amince da samuwar kasar Falasdinu mai zamanta ne kawai hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudiya ya nakalto majiyar Saudia na fadar haka a MDD a jiya Jumma’a. Ta kuma kara da cewa Falasdinawa ba zasu taba amincewa a koresu daga kasarsu ba kamar yadda wasu yahudawa da magoya bayansu suke so. Labarin ya kara da cewa wannan bukatar na zuwa ne a dai-dai kasashen ta Saudia da Faransa suke kokarin gudanar da gagarumin Taro a cikin watan Yuni mai zuwa don bunkasa wannan ra’ayin ta kafa kasashe biyu. Wannan ra’ayin yana kara samun goyon baya a wannan makon musamman bayan da HKI ta kara yawan...
Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka JohnKerry ya bayyana cewa HKI bata isa ta wargaza cibiyoyin makamacin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dilancin labaran IP na klasar Iran ya nakalto Kerry na fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa babban al-amari a cikin duk wani kokari na kauda cibiyoyin Nukliyar kasar Iran ita ce yakin da zai biyo bayan wannan kokarin, Kerry yana magana ne don maida martani ga maganar cewa HKI tana shirin kai hare-hare ko yiyuwan ta kai harehare kan cibiyoyin nukliya kasar Iran idan ta ki amincea ta dakatar da tashe makamashiun uranium a cikin gida a tattaunawan da take da Amurka kan shirin nata. Labarin ya kara da cewa wannan yana tabbatar da...
Samun Gurbin Shiga Jami’a Da Sauran Manyan Makarantu Samun damar shiga jami’a a Nijeriya na da matukar wahala a koda-yaushe, sai ga shi wannan shekara ta 2025 ta bullo da wasu sabbin kalubale. Daga kura-kuren da aka samu yayin yin rajista da kuma gwajin kwamfuta, don rage yawan masu shiga jami’ar, tsarin ragewar na wannan shekarar ya fi na kowace shekara. Sama da dalibai miliyan 1.9 ne suka rubuta jarrabawar a wannan shekarar, wanda hakan yasa ta zama jarrabawa mafi girma a tarihin hukumar shirya jarrabawar. Wannan karuwar, ta nuna karuwar yawan al’umma da kuma karuwar bukatar neman ilimi a tsakanin matasan Nijeriya. Har ila yau, wannan na nuni da cewa; adadin guraben da ake da su a jami’o’in kasar...
Rayuwa ta yi wa Talatu atishawar tsaki (ba sunanta na asali ba ne) tun daga shekarar 2018, bayan ta fada harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi a lokacin da ƙawarta ta ƙwaɗaita mata yadda lamarin yake. Ta kasance yarinya mai hazaka mai kimanin shekara 29, kuma ta yi karatu a Jami’ar Kwatano har ta yi aiki a banki na tsawon shekaru biyu kafin ta yi aiki da Kamfanin NNPC da wasu manyan wurare. Sai dai harkar shaye-shaye ta sa ta siyar da motocinta guda biya da kwamfiyuta da wasu abubuwa masu mahimmanci. Halin da wakilin Aminiya ya tsince ta a ciki ke nan a Lungun Gurguwa da ke Lagas Street, Garki Abuja. Ta shaida masa cewa, sam ba ta jin dadin wanna...
“Fanin na kuma taimaka wa wajen samar da ayyukan yi da samar da abinci mai gina jikin Dan’adam da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, musamman duba da wayar da kai da ake yi na samar da abinci mai gina jiki,“ in ji shi. Shi ma, a nasa jawabin a wajen taron, Daraktan Cibiyar Bunkasa Samar da Takin Zamni ta Kasa da Kasa (IFDC) da ke kasar nan, Dakta Yusuf Dramani ya bayyana cewa; cibiyar na aiki kafada da kafada da Hukumar NIRSAL, musamman don cike gibin da ake da shi a kasar, wajen samar da rancen kudaden noma ga manoman kasar. “Duk da cewa, fannin aikin noma na kasar nan, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin...
Wata mata da ta yi wa masu neman aikin gwamnati damfarar kudi sama da Naira miliyan 250 ta shiga hannun jami’an tsaro. ’Yan sanda sun cika hannu da wannan mata mai suna Iyabode Oluwafemi ne a Jihar Ondo bisa zargin karbar kudaden ta hanyar yaudarar mutane da ta yi wa alkawarin sama masu ayyuka a ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban-daban. A yayin da da yake magana kan wadda ake zargin a ofishinsa da ke Akure, babban birnin jihar, Kwamishinan ’yan sanda a jihar, Wilfred Afolabi, ya ce jami’an runduanr sun yi nasarar kama Iyabode Oluwafemi ne bayan yawan korafin da mutanen da ta damfara suka yi. Ya bayyana cewa da zarar sun kammala bincike za su gurfanar...
Ministan ya kuma zayyano jerin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta kirkiro da nufin zaburar da matasa rungumar kiwon dabbobi, musamman don samun riba ciki har da sama musu hektar noma 51,000, a karkashin hadaka da shirin fitar da kaya na ‘Gulf’ na jihohi da kuma shirye-shiryen farfado da guraren kiwon dabbobi 417 a daukacin fadin kasar nan. “Muna da abubuwan da za mu yi amfani da su a kasar nan, domin yakar yunwa a fadin kasar baki-daya,” in ji Ministan. “Akalla a kasar nan, muna da Shanu kimanin miliyan sha biyar da Tumakai miliyan 60 da Kaji da miliyan 600 da Akuyoyi da miliyan 1.4 da Rakuma miliyan 700,000 tare kuma da kasar noma, amma sai dai har yanzu, kasar...
“Wannan ci gaban zai kuma taimaka wajen kara habaka tattalin ardikin da ke a yankin na Arewa maso Gabas, wanda hakan ya zame mana wajbi, mu sake dawo wajen yin aikin domin aikin ya ci gaba da tafiya,” A cewar Ojulari. Kan batun rikicin da yaki ci, yaki cinyewa a tsakanin Kamfanin na NNPCL da kuma rukunomin Kamfanin Dangote Ojulari ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokari domin a kawo karshen rikicin. “Dangote ya bayar da gagarumar gudunmawa wanda kuma, ya cannaci a yaba masa, za mu kuma yi hadaka domin mu tabbatar da, mun ci gaba da samar da wadataccen Man Fetur ga ‘yan kasar nan,” Inji Sabon Shugaban. “Ana samun masalaha kan komai ne, ta hanyar tattaunawa...
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa; MDD ba za ta shiga cikin duk wani tsari da ba zai girmama dokokin kasa da kasa ba a Gaza. Bayanin nasa dai ya zo ne a matsayin mayar da martani akan maganar da ta fito daga HKI na cewa tana aiki tare da Amurka domin raba kayan agaji a Gaza. Babban magatakardar MDD ya kuma kara da cewa; kaso 80% na yankin Gaza, ko dai yana karashin mamayar Isra’ila da kuma wanda aka bai wa mazaunansa umarnin su fice daga cikinsa.” Antonio Guterres ya yi gargadin cewa matukar ba a bude iyakoki ba, aka kuma shigar da kayan agaji, to mutanen Gaza za su rasa rayukansu.” Babban magatakardar MDD ya tunawa...
Jaridar “Maariv” ta buga labarin da yake cewa; Tattauanwa a tsakanin “Isra’ila” da kasashen Afirka akan yadda za su bayar da dama ga mutanen Gaza da su yi hijira zuwa can, ta yi isa sosai. Rahoton jaridar na jiya Juma’a ya ci gaba da cewa; Tattaunawar ana yinta akarkashin damar da za a bai wa Mutanen Gaza su yi hijira cikin zabin kansu, zuwa wasu kasashen na Afirka, kuma Amurka tana cikin wadanda ake tattaunawar da ita da wadannan kasashen na Afirka. Haka nan kuma jaridar ta ‘yan sahayoniya ta ce, kasashen da ake tattaunawa da su, sun nuna amincewarsu a matakin na farko ka karbar bakuncin mutanen Gaza. Tattaunawar dai ta kunshi yadda za a gina matsugunan Falasdinawan da...
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Arakci wanda ya gana da takwransa na fadar Vatican ya yi kira da a kawo karshen laifukan da ‘yan mamaya suke tafkawa akan Gaza da gaggawa a kuma shigar da kayan agaji zuwa yankin. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya je kasar Italiya domin tattaunawar bayan fage da Amurka akan Shirin kasarsa na Nukiliya, ya ziyarci fadar Vatican, inda ya gana da ministanta na harkokin wajen Cardinal paul Gallagher, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar Fafaroma Farancis sannan kuma da murnar zabar sabon Fafaroma Leo na 14 Abbas Arakci ya yi wa shugabannin fadar ta Vatican bayani akan matsayar Jamhuriyar musulunci ta Iran dangane da shirinta na Nukiliya na zaman lafiya, da...
Dan majalisar Amurkan mai suna Randall Adam Fine wanda yake wakiltar jam’iyyar “Republican” ya sake tunanowa duniya da yadda kasarsa Amurka ta jefa wa biranen Nagasaki da Hiroshima bama-baman Nukiliya a karshen yakin duniya na biyu, ta hanayr yin kira da a jefa wa zirin Gaza irin wadannan makaman na kare dangi. Kungiyoyin Falasdinawa mabanbanta sun yi tir da wannan irin kira na ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kare dangi, suna masu yin kira ga ita kanta majalisar Amurka da ta fito da yi Allawadai da wannan kira wanda yake cike da kiyayya.” Kungiyar Hamas ta bayyana abinda dan majalisar na Amurka ya yi da cewa, ya keta dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva, kamar kuma...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, hadin gwiwa a bangaren ilimi tsakanin Sin da Amurka na moriyar juna ne, kuma Sin ta kasance mai adawa da siyasantar da hadin gwiwar bangaren ilimi. Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Juma’a, lokacin da aka nemi jin ta-bakinta kan matakin gwmnatin Trump na hana jami’ar Harvard daukar dalibai daga kasashen waje. A cewar Mao Ning, ire iren wadannan matakai da Amurka ke dauka za su lalata kima da darajar kasar, tana cewa, Sin za ta nace wajen kare hakkoki da muradun dalibai da malaman kasar dake kasashen waje. Ta kuma jaddada adawar Sin ga bata sunanta da takalarta ba gaira ba dalili, tana mai...

Kamfanoni Masu Jarin Waje Sun Ci Gajiyar Tsarin Kasar Sin Na Samar Da Rangwamen Gwamnati Ta Musayar Sabbin Kayayyaki Da Tsofaffi
Alkaluman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta samar a kwanakin baya sun shaida cewa, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da tsarin samar da rangwamen gwamnati ta musayar sabbin motoci da tsofaffi, yawan bukatun da aka mika na yin musayar tuni ya wuce miliyan 10, matakin da ya yi matukar rage kudin da masu sayayya suka biya, baya ga kuma karuwar motocin da kamfanonin sai da motoci na gida da waje suka sayar. Lamarin hakan yake ma ga kasuwar sai da Kayayyakin laturoni na amfanin yau da kullum a gidaje. In mun dauki misali da dandalin sai da kayayyaki na Suning.com, tun bayan da aka fara aiwatar da tsarin samar da rangwamen gwamnati ta musayar sabbin kayayyaki...
Onyemekara ya sanar da cewa, rahoton na karya da kafar yada labaran ta wallafa kan zargin cin hancin na biliyoyin Naira, na kanzon Kurege ne, wanda kuma bai da wata tushe, ballantana wata makama. Kazalika, ya bayar da tabbacin cewa, NPA kamar yadda ta saba, za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa gaskiya da rikon amana, musamman kan abinda ya shafi, ayyukan kashe kudade. Onyemekara ya kuma yi watsi da batun zargin badakalar hada-hada a ofishin Hukumar NPA da ke a Birtaniya, inda ya sanar da cewa, babu wani batun wata hada-hadar ayyuka a ofishin makamancin haka, da aka gudanar a ofishin. Ya yi kira ga kafafen yada labarai na kasar nan, da su tabbatar da suna tuntubar...
Kasashen Sin da na ASEAN sun kammala tattaunawa game da kafa yankin ciniki cikin ‘yanci na Sin da ASEAN (CAFTA) karo na 3, wanda ke aikewa da sako mai karfi na goyon bayan gudanar ciniki cikin ‘yanci da hadin gwiwa mai bude kofa. A cewar Mao Ning, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, hakika wannan labari ne mai dadi, tana cewa, wani muhimmin mataki ne na rattaba hannu kan yarjejeniyar daukaka yankin a karo na 3. Ta kara da cewa, Sin da kasashen ASEAN, dukkansu masu goyon bayan dunkulewar tattalin arzikin duniya ne da cudanyar bangarori da dama, haka kuma yankin na CAFTA na 3, zai taimakawa Sin da kasashen wajen kara zurfafa budewa juna kofa da samun ci gaba...
“Haƙiƙa muna alfahari da Dr. Sani Dauda Ibrahim da wannan ajin naku, musanman cewa akan ku na fara koyarwa a jami’a, kuma haɗin kan ‘yan wannan ajin ya zama na daban a cikin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, musanman saboda ayyuka da kuka gabatar na ci gaban ilimi a jami’ar Bayero da yadda kuke damuwar da al’amuran ilimi” cewar Dr. Almajir. Taron ya samu halartar Dr. Maimuna Isma’il da ke koyarwa a sashen da sauran mambobin ƙungiya da ‘yan uwa da abokan arzikin Dr. Sani Dauda Ibrahim da aka karrama a wajen taron. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
An gudanar da taron kolin bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari na duniya na shekara ta 2025 jiya Alhamis 22 ga watan nan a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A gun taron, mai taken “rungumar zamanin digital, da samar da ci gaba cikin hadin-gwiwa”, an yi musanyar ra’ayi mai zurfi, tare da cimma matsaya daya kan batutuwa da dama, da bullo da shawarar Beijing ta taron kolin bunkasa kasuwanci da zuba jari na duniya na shekara ta 2025, inda aka yi kira da a fadada hadin-gwiwa a zamanin da muke ciki, da nufin samar da ci gaba da wadata tare. Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai Dan Asalin Jihar Kano...
PDP na fama da rikicin cikin gida mafi muni a tarihin jam’iyyar. Tun lokacin da jam’iyyar ta rasa shugabanci a 2015, ta ci gaba da fuskantar matsaloli wajen magance rikicin da take fama da shi. Ko wani zabe yana zuwa da nashi kalubalan, yana bayyana cin amana na cikin jam’iyya. Zaben 2023, jam’iyyar ta bai wa Atiku Abubakar takarar shugaban kasa, wanda shi dan Arewa ne, inda lamarin ya haifar da fushi na masu ruwa da tsaki daga kudancin kasar nan, musamman daga wajen ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike. Haka ma a daidai lokacin da ake kara fuskantar zaben 2027, wannan yanayi na sake kara bayyana adaidai lokacin da Atiku ke kokarin samun tikitin jam’iyyar. A lokaci guda, Wike...
Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya bayyana shirinsa na ficewa daga Jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ya umarci duka Kwamishinoninsa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da su sauya sheƙa tare da shi ko kuma su sauka daga muƙamansu. Da yake bayani a Uyo babban birnin jihar ranar Alhamis, gwamnan ya ce ba zai yi aiki da waɗanda ya naɗa su, su yi aiki da wata jam’iyya ba. An kama yarinya kan kashe jariri a sansanin ’yan gudun hijira Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Borno Gwamna Eno ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP ba ta da taswirar da za ta tabbatar masa da tafiyarsa cikin kwanciyar hankali a zaɓuka, yana mai cewa yana da yaƙinin cewa...
A yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da shugaban gwamnatin kasar Jamus Friedrich Merz, bisa gayyatarsa da aka yi. Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin da Jamus suna raya dangantakar dake tsakaninsu bisa girmama juna, da amincewa da bambance-bambance, da hadin gwiwa don samun moriyar juna, kuma akwai bukatar bangarorin biyu su yi kokari tare don tabbatar da raya dangantakarsu yadda ya kamata. Ya ce, da farko dai, ya kamata a yi imani da juna a fannin siyasa tsakanin kasashen biyu. Na biyu kuma, ya kamata a kara inganta dangantakarsu, wato ci gaba da hadin gwiwa a fannonin da suka riga sun hada hannu kamar su kera motoci, da injuna, da kuma masana’antar sinadarai...
An dai fara goyon bayan tazarcen Tinubu a wurin taron lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce babu wani gurbi a fadar shugaban kasa a 2027. Barau ya ce, “A bayyane yake a 2027, za mu sami gagarumar nasara, In Sha Allah. Don haka, mu ci gaba da hanyar da muke kai. Mu hada kai da juna, mu yi aiki tare da shugaban kasa, mu yi aiki tare da kowa, mu hada kai a tsakaninmu don samun nasarar da ake bukata.” Sanata Barau ya ci gaba da cewa sauya shekan wasu shugabannin jam’iyyun adawa zuwa APC ya kasance sakamakon aikin Shugaba Tinubu a cikin shekaru biyu kawai da ya shafe a kan karagar mulkin Nijeriya. Kazalika, Ganduje...
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wata yarinya ’yar shekara 15 bisa zargin jefa gawar wani jariri a cikin wani banɗaki da ke sansanin ’yan gudun hijira a Monguno. A cewar wata majiyar ’yan sanda a ranar 22 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 9:15 na safe, an bayar da rahoton cewa, a safiyar wannan rana da misalin ƙarfe 6:00 na safe, an tsinci gawar wani jariri da aka haifa a yashe a ɗaya daga cikin banɗaki da ke sansanin. Kotu ta bai wa EFCC izinin binciken sayar da filin musabaƙar Alƙur’ani na N3.5bn a Kano Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Borno Majiyar ta ce, wacce ake zargin mai suna Yafalmata Alhaji Mustapha mai shekara 15, da...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kara Haske kan Batun Inganta Sinadarin Uranium Da Zamanta Da Amurka
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ana gudanar da zagaye na biyar na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin tawagar Amurka da na Iran a cikin yanayi na kwarewa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana a yau Juma’a cewa: Tattaunawar tana gudana cikin kwarewa da kwanciyar hankali, yana mai cewa abin da ake yadawa a kafafen yada labarai hasashe ne da baya da tushe ko inganci kuma baya da bambanci da shaci fadi. A yau Juma’a da yamma ne aka fara shawarwarin da ba na kai tsaye ba karo na biyar...
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar, Mr. Xi Jinping, a kwanakin baya ya yi muhimmin bayani game da aikin raya harkoki masu nasaba da wayewar kai a kasarsa, inda ya ce, ci gaban dukkanin fannonin samar da ababen more rayuwa da kuma wayewar kai, muhimmiyar alama ce ta zamantarwa mai salon kasar Sin. Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a karfafa hadin kan jama’a bisa tunanin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin na sabon zamani, da mai da hankali kan wayar da kan al’umma, da sa kaimin raya al’adu da kuma da’a a tsakanin al’umma, sa’an nan kuma a karfafa ayyukan ba da jagoranci, da zurfafa yin gyare-gyare...
Majiyoyin watsa labaran Iran sun musanta da’awar cewa: Amurka ta bukaci ziyarar cibiyoyin sojojin Iran Wasu majiyoyi masu tushe sun musanta ingancin da’awar jita-jita na baya-bayan nan game da bukatar Amurka ta neman ziyartar cibiyoyin sojojin Iran, tare da bayyana su a matsayin maganganu marasa tushe. A cewar kamfanin dillancin labarai na Tasnim, rahoton da ya shafi bukatar Amurka na ziyartar wuraren soji, cibiyar makamashin nukiliya da kuma wuraren bincike na Iran cikin makonni masu zuwa, labarai ne marasa tushe ballantana makama. Haka zalika majiyoyin sun musanta ikirarin da ake dangantawa da ministan harkokin wajen Iraki na cewa “ya yi kira ga Iran da ta fice daga Iraki,” suna masu jaddada cewa ba a taba yin irin wadannan kalamai ba....
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Matsayin Amurka a cikin ɗakin tattaunawa da Iran ya bambanta da abin da suke shelantawa a waje Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Kalamai da matsayar da jami’an Amurka suka dauka a cikin dakin tattaunawa da Iran suna shan bamban a fili da abin da suke bayyanawa a bainar jama’a, yana mai cewa wannan sabani yana dakushe kwarin gwiwar bangaren Iran da kuma yin barazana ga makomar shawarwarin. A wata hira da ya yi da mujallar Der Spiegel ta Jamus, Takht-Ravanchi ya bayyana kin amincewar da Iran ta yi da bukatar “samar da sifili na Uranium da take sarrafawa”, yana...
Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta zargi shugaban gwamantin kasar Siriya al-Julani da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta bayyana shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Abu Muhammad al-Julani a matsayin azzalumi wanda ya sayar da addininsa tare da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai. Ta yi kira ga ‘yan kasashen waje da ke cikin jami’an tsaron Siriya da su tuba su yi watsi da hidimar da suke yi wa azzalumi. A cikin wani sako na addini, a kokarinta na jan hankali masu saurarenta wadanda ta kira su “masu hijira saboda Allah,” kungiyar ta’addanci ta ISIS ta fitar da wani kira na farfaganda ga wasu ‘yan kasashen waje da kuma sabbin hukumomin...
Don haka, ya zama dole kasashen Global South su hada kansu su dauki matakan dakushe duk wani radadi da matakin harajin da Amurka ta dauka zai haifar, ciki har da bunkasawa da inganta cinikayya tsakanin wadannan kasashe,ta hanyar hada kansu domin rage dogaro da tattalin arzikin Amurka ko na kasashen yammaci, wannan yunkuri zai bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin Global South. Kasashen na Global South suna sake zayyana tsarin tattalin arzikinsu ta hanyar bayar da fifiko ga bunkasuwar tattalin arzikinsu da bayar da dama ta bai daya ga kowace kasa wajen taka rawa a harkar kasuwanci. Domin kuwa kasashen sun hade kansu wajen nuna turjiya ga wannan tsarin haraji na Amurka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a S.M. Shuaibu ta ƙi amincewa da buƙatar wasu mambobin Kwamitin Musabaƙar Alƙur’ani da ke son a hana EFCC bincike kan yadda aka sayar da wani fili mai darajar Naira biliyan 3.5. Filin da ake magana a kai yana bayan titin Ahmadu Bello Way, kuma yana da faɗin hekta biyu. Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Borno An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya Tsohon Gwamnan Sojan Kano, Kanal Abdullahi Wase ne, ya bayar da filin don a gina katafaren waje da za a riƙa gudanar da musabaƙar Alƙur’ani duk shekara. Amma daga baya sai wasu mambobin kwamitin suka ga an gina gidaje 38 a filin ba...
Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
Kazalika ya kara da cewa, idan za a iya tunawa, Seyi ya kewaya kusan dukkanin jihohin Arewacin kasa nan tare da tallafa wa al’umma da kayan abinci da kudade, musamman a watan Ramadana da ya gabata. A karshe, Sanusi ya yi kira ga matasa maza da mata, kada su bari a bar su a baya a wannan tafiya, domin kuwa kungiya ta kowa da kowa ce, duk mai bukatar yin rajista; kofa a bude take, domin kuwa suna da ofisoshi a kowace jiha, ciki har da babban birnin tarayya Abuja da suke shirin bude kwanan nan ga masu bukatar shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
“’Yan kwanakin da suka gabata, na yi wata ganawa da Babban Hafsan Sojin Kasa, inda ya bay-yana min cewa; yana neman akalla jirage marasa matuka kimanin 32, domin kawo karshen wannan ta’addanci, wanda kuma abin da ya fada din gaskiya ne. “Kowane jirgi maras matuki, na kai wa kimanin dala miliyan 5.5, don haka, me yasa ba za mu iya hada karfi da karfe wuri guda mu sayi jiragen ba, don bai wa harkar tsaro fifiko? Har wa yau, ya bayyana kwarin gwiwar cewa; tare da bin tsarin da ya dace da hadin kai a tsa-kanin dukkanin bangarorin gwamnati, za a iya magance wadannan tashin hankula cikin gagga-wa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
’Yan Najeriya daga kowane ɓangare daban-daban sun caccaki jam’iyyar APC bisa yanke shawarar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da cewa shekararsa biyu kacal da hawa mulki. Wasu na ganin matakin ya nuna rashin tausayi da rashin damuwa da halin ƙuncin da al’umma ke ciki. Cutar lamoniya ta kama alhazai 99 ’yan ƙasar Indonesiya a Saudiyya NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC Jagororin jam’iyyar APC, gwamnoninta da ’yan majalisa ne suka fito suka nuna goyon bayansu ga Tinubu. Amma jama’a na ganin hakan na nuna burin ci gaba da riƙe madafun iko ne kawai, ba wai taimakon talakawa ba. Ra’ayoyi daga sassa...
“Idan ka yi kwao sosai, babu abin da za ka ji tsoro. Idan ba ka yi kwazo ba, za mu biyiya. Idan ba ka yi komai ba, za ka bar mana aikinmu,” in ji shugaban kasa. Masu ruwa da tsaki sun ce wasu ministoci, musamman a cikin muhimman sassa, suna cikin bincike yayin da Tinubu ke shirin yanke hukunci a kan inganta majalisar ministocinsa. A yanzu dai ana zuba ido a gani ko dai Tinubu zai gudanar da sauye-sauye a majalisar ministocinsa cikin gaggawa ko kuma zai jinkinta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin kasar Amurka tana takurawa JMI ne don ta dakatar da shirinta na makamashin nukliya. Don haka ne Amurka take barazana ga Iran a kan cewa idan bata amince a cimma yarjeniya da ita a kan shirinta na makamashin Nukliya ba to ba abinda ya rage sai zabinb soje don wargwaz cibiyotyin makamashin nukliya na kasar Iran. Wannan bukatar itace HKI ta yi ta nanatawa a MDD a kuma duk inda jami’an gwamnatinta suka yi jwabi shekara da shekaru. A halin yanzu Amurka na bin wannan Shirin sau da kafa. Wata majiya ta shaidawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa, a zagayen tattaunawa har 4 wadanda kasashen biyu suka gudanar za’a fahinci cewa Amurka tana bukata a...

Iran: Inda Makiya Kasar Sun San Cewa Zasu Sami Nasara A Kan Iran A Yaki Da Tuni Sunn Farmata Da Yaki
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa da Amurka da HKI sun san cewa zasu sami nasara a kan kasar Iran da yaki da tuni sun fadawa kasar sun kuma mamayeta. Amma saboda wannan tsoron ne suka zabi tattaunawa da ita a kan shirinta na makamshin nukliya. Sannan Shirin makamacin nikliya ma daya ne kacal daga matsalolin da ke tsakanin Iran da HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka. Ya ce akwai matsaloli da dama, tana jirin ta kamala da gudu don ta bullo da wata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya da yamma ya kuma kara da cewa, manufar Iran ta shiga tattaunawa da Amurka ita ce,...

Limamin Masallacin Jumma’a A Nan Tehran Ya Yi Magana Dangane Da Kwatar Garin Khurramshar Daga Sojojin Sadam
Mataimakin limamin Jumma’a a nan Tehran Sheikh kum Hujjatul Islam Kazen Sadiki bayan yayio Magana a kan al-amuran tsaron All..da kuma yadda bayin All..da kuma shidanun mutane zasu mutu da kuma yadda sakamakon ko wannansu a gaban All…/ Ya kuma ya gamanar fatahin garin KharramShahr dake kudancin kasar Iran kuma kan iyaka da kasar Iran, wanda dakarun kare juyin juya halin musulunci tare da sauran sojoji da mayakan sa kai suka kwace wannan garin daga hannun sojojin Sdam Hussain a rana irin ta yau wato 2 ga watan Khordod. Banda haka lamamin yana Magana kan littafan da aka buga dangane da wannan gagarumin fatahin da mutanen Iran suka sami a kan wannan garin. Wanda kuma daga wannan nasarar ne ta...

Jam’iyyar APC A Najeriya Ta Tabbatar Da Tinubu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar A Shekara Ta 2027
Jam’iyyar ‘All Progressives Congress” (APC) mai Mulki a tarayyar Najeriya ta tabbatar da shugaban Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar Jam’iyyar a zaben shugaban kas ana shekara ta 2027 mai zuwa. Shafin yada labarai na Afrika ya bayyana cewa a jiya Alhamis ce a taron Jam’iyyar wanda aka gudanar a Abuja, kuma wanda ya zo dai-dai da cika shekaru biyu da zagayensa na farko na shugabancin kasar Jam’iyyar ta nada shi Shugaba Bola Ahmed Tinubu dan shekara 73 a duniya a matsayin dan takararta a zaben na shekara ta 2027, don ya sami damar kamala shirinsa nag yare-gywaren tattalin arzikin kasar da y afara. Shugaban Tinubu dai ya kara farashin man fetur a ranar da ya hau kan kujerar...
Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Umar Iliya Damagun, ya yi Allah Ya isa ga masu zargin da yi wa jam’iyya mai mulki, APC, aiki. Wasu masu ruwa da tsaki a PDP na zargin cewa Damagun da yi wa jam’iyyar zagon ƙasa APC, shi ya sa yake rura wutar rikicin cikin gida da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a PDP. Amma a yayin wata hira da ya yi da BBC, Damagun ya yi fatali da zargin, yana mai cewa Allah Zai saka masa tsakaninsa da masu yi masa wannan ƙazafi. “Allah Ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan ƙazafi, kuma Allah Zai yi mana shari’a,” in ji shugaban na PDP, wanda ake zargi da zama ɗan-amshin-shatan...
Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa. Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa. ‘Yan mata suna cikin hadari, galibi ana tilasta musu auren wuri ko aikin gida ko aikin jima’i maimakon a ba su damar koyo. Wata kwararriyaa fannin ilimi da ke zaune a Jos, Jihar Filato, Misis Peace Pernam, ta ce, “Ilimi wata hanya ce ta rayuwa mai muhimmanci da ke kawar da fatara, rage matsalar tsaro, da samar da ci gaban kasa, duk da haka, ga miliyoyin yara a yankin Arewa...
Matakin da Gwamnatin ta dauka, na son yin amfani da Gidauniyar TETFund, domin yin wannan aikin, babban abin jinjinawa ne, wanda idan har ba a samu wata gazawa ba, kamar a sauran ayyukan baya, musamman duba da cewa, Giduaniyar ta samu shedar cewa, ba a santa da gazawa, wajen wanzar da ayyukan da shirye-shiyen da ta sanya a gaba, kan batun ganin an inganta karatu a jami’oin kasar. Kazalika, Ministan ya ce, daukacin aikin shi ne, domin a dakile yawan ficewar da kwararrun Likitocin kasar ne yi ne, zuwa ketere domin neman aiki, wanda hakan zai sanya, a ciki gaba da raike su a kasar nan, domin su yi aki a cikin kasar. A karkashin aikin, za a kuma tabbatar...
Babban Mashawarcin Tsaro na Kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa an kashe ’yan ta’adda sama da 13,000 a fadin Najeriya daga lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hau mulki a watan Mayun 2023 zuwa yanzu. Ribadu, yayin da yake jawabi a taron Koli na Jam’iyyar APC a zauren taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ya bayyana cewa duk da an samu ci-gaba mai sosai wajen magance matsalar rashin tsaro, yanayin sarƙaƙiyar tsaro ya sa a mafi yawan lokaci jama’a ba sa iya gane waɗannan nasarori nan take. Ribadu ya bayyana cewa an kashe jimillar ’yan tada kayar baya da ’yan fashin daji 13,543, yayin ayyuka daban-daban da sojoji da sauran hukumomin tsaro suka gudanar a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Me sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya ɓangaren adawa suka zaɓi inuwar Jam’iyyar ADC domin haɗa hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC daga mulki? Da daren Talata ne dai manyan ’yan adawar, waɗanda suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma ɗan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a ƙarƙashin inuwar ADC din. Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya riƙe wannan haɗaka? Shin waɗannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Me sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya ɓangaren adawa suka zaɓi inuwar Jam’iyyar ADC domin haɗa hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC daga mulki? Da daren Talata ne dai manyan ’yan adawar, waɗanda suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma ɗan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a ƙarƙashin inuwar ADC din. Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya riƙe wannan haɗaka? Shin waɗannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da...
Kimanin kwanaki biyu ke nan ana jita-jitar cewa sojoji a sun yi nasarar hamɓarar da gwamnatin Shugaba Kasar Kwadebuwa, Alassane Ouattara. Jita-jitar ta fara yaɗuwa ne tun bayan jin ƙarar harbe-harbe a yankunan ƙasar da dama musamman a babban birnin ƙasar na Abijan. Ba mu tilasta wa kowa ya koma APC ba — Tinubu Jami’an tsaron Zulum sun buɗe wa Boko Haram wuta a Maiduguri Wasu rahotanni na nuna cewa an samu ɓarkewar rikici ne a cikin birnin na Abijan, lamarin da ake hasashen ya yi sanadiyar masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Ouattara kimanin mutum 33 cikin kwana biyu. Sai dai har ya zuwa yanzu babu wani tabbataccen rahoton daga majiya mai ƙarfi da ke bayyana hakikanin abin da ke...
Ganduje ya ce, baya ga samun nasara a jihohi 22 a cikin 36 da ke kasar nan, karin gwamna daya na kan hanyarsa ta komawa jam’iyyar nan ba da dadewa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Masanan Najeriya Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Tinkarar Kalubalen Harajin Kwastam Na Amurka
Wasu masana a tarayyar Najeriya sun jinjinawa yadda Najeriya da Sin suka daga dangantakarsu zuwa huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni a bara, matakin da ya tabbatar da goyon bayansu ga kokarin tinkarar kalubalen karin harajin kwastam da Amurka ke dora musu bisa radin kai. Kwanan baya, an gudanar da taron tattaunawa kan yadda za a tinkari harajin kwastam da Amurka ke kakabawa sauran kasashe a birnin Abuja hedkwatar Najeriya, inda babban darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Najeriya Charles Onunaiju ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da Najeriya bisa dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka, da shawarar “ziri daya da hanya daya” da dai sauransu, ba ingiza bunkasuwar manyan ababen more rayuwa a Afirka kadai...
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya caccaki masu cewa gwamnatinsa na ingiza ’yan Najeriya wajen bin tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa ba za ka iya zargi mutane kan zaɓar jam’iyya ba. Da yake jawabi a wajen taron ƙoli na jam’iyyar APC karo na farko da aka yi a ranar Alhamis, da ya gudana a fadar shugaban ƙasa a Abuja, shugaban ya ce “jam’iyya ɗaya ce ke mulki”. Jami’an tsaron Zulum sun buɗe wa Boko Haram wuta a Maiduguri An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe “Ga waɗanda har yanzu suke tunanin fita daga jam’iyyarsu, ƙasar nan taku ce, ku riƙe ta, ga masu maganar tsarin jam’iyya ɗaya, jam’iyya ɗaya ce ke...
Modric, ya lashe kofuna 28 da suka hada da gasar zakarun Turai 6 da Laliga 4 tun lokacin da ya koma Real daga Tottenham a shekarar 2012. “Na zo ne a shekarar 2012 tare da fatan sanya rigar yan wasan da suka fi fice a duniya da kuma burin samun manyan nasarori, Real Madrid ta canza rayuwata a matsayina na dan wasan kwallon kafa da kuma mutum, ina alfahari da kasancewata a daya daga cikin mafi kyawun kulob a tarihi” inji shi. Real za ta bude gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa da Al-Hilal ta Saudi Arabiya a ranar 18 ga watan Yuni, sannan kuma za ta kara da Pachuca ta Mexico da RB Salzburg ta...
A gun taro karo na 28 na kwamitin madatsar ruwa na duniya da ake gudanarwa, an bayyana cewa kasar Sin ta cimma nasarar gina madatsun ruwa masu kunshe da fasahar zamani da dama, kuma ci gaban da take samu a bangaren kirkire-kirkire, da nasarorin da take samu a fannin gudanar da harkoki masu masaba da hakan na jawo hankalin kasa da kasa. Ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta kyautata aikin na’urorin sa ido kan kananan madatsun ruwanta dubu 51, da zummar kafa tsarin taurarin dan Adam, da jiragen sama marasa matuka, da na’urar rada, da tasoshin doron kasa, da na’urorin karkashin ruwa, da na’urorin sa ido bai daya. Ban da wannan kuma, Sin ta fara aikin gwaji a wurare...
Arewa Tech Fest, taron koli ne na fasaha da kirkire-kirkire na kwanaki uku, wanda ke tattaro ’yan kasuwa, kwararru masu fasaha, masu zuba jari, da masu tsara manufofi don bunkasa fasahar kere-kere a Arewacin Nijeriya. El-Rufai ne da kansa ya shirya bikin. Minista Tijani, wanda ya gabatar da jawabi mai mahimmanci, ya yi magana a kan sauye-sauye na zamani da kirkire-kirkire a sassan gwamnati da masu zaman kansu na Nijeriya. El-Rufai ya isa wurin taron ne a makare, inda ya nemi afuwar mahalarta taron tare da bayyana cewa ya samu jinkiri saboda wani muhimmin taron siyasa da aka gudanar a yammacin jiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Ko shakka babu, ba wani tsari ko salon ciyar da al’umma gaba da za a iya cewa zai dace dari-bisa-dari da dukkanin sassan duniya bai daya, amma duk da haka, daukacin kasashen duniya za su iya koyi daga kwarewar kasar Sin, da tsawon lokacin da ta shafe tana gwada dabarunta na ci gaba wadanda suka haifar da da mai ido. Yayin da a nasu bangare sassan kasa da kasa ke da damar tsara manufofi daidai da burikansu da yanayin da suke ciki. Wasu masharhanta na ganin kwarewar da Sin ke samarwa duniya, tamkar sabon zabi ne ga sassa masu fatan gwada wani salo na bunkasa kasashe masu tasowa, wanda ya sabawa na yammacin duniya, don haka sassa daban daban ke...
Jami’an tsaro da ke raka ayarin motocin Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum sun buɗe wuta kan ’yan Boko Haram a hanyarsu daga Gamboru Ngala zuwa Maiduguri bayan wani rangadi na kwanaki uku. Kodayake ba a san dalilin ’yan ta’addan ba, amma jami’an tsaron ayarin motocin sun bi su inda suka yi ta musayar wuta na kusan rabin sa’a tsakanin ƙarfe 12:50 na rana zuwa ƙarfe 1:30 na rana. An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin ne sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin. Wata...
Jami’an tsaro da ke raka ayarin motocin Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum sun buɗe wuta kan ’yan Boko Haram a hanyarsu daga Gamboru Ngala zuwa Maiduguri bayan wani rangadi na kwanaki uku. Kodayake ba a san dalilin ’yan ta’addan ba, amma jami’an tsaron ayarin motocin sun bi su inda suka yi ta musayar wuta na kusan rabin sa’a tsakanin ƙarfe 12:50 na rana zuwa ƙarfe 1:30 na rana. An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin ne sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin. Wata...
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa. “Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su. Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida. Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39. Sanarwar ta MDD ta ci gaba...
Jaridar ‘yan sahayoniya ta “Ma’ariv’ ta buga labarin da yake cewa; Isra’ila tana fuskantar matsalar diplomasiyya saboda ci gaba da yakin Gaza. Jaridar ta kuma ce; A halin yanzu “Isra’ila” tana fuskantar abinda ta kira “Tsunami Na Diplomasiyya” saboda yakin da take ci gaba da yi a Gaza. Haka nan kuma jaridar ta soki gwamnatin Netanyahu tare da bayyana ministan harkokin waje Gadion Sa’ir wanda ta ce, ba abinda ya dame shi kamar ci gaba da zama akan kujerarsa, da cewa; Ba ya fahimtar girman musifar da take tunkaro Isra’ila.” Har ila yau, jaridar ta yi suka ga ministar sufuri Miri Rigiv da cewa saboda ta’annuti, ta ki yin furuci da cewa Isra’ila tana karkashin takunkumin zirga-zirga ta sama, kuma...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci Sin da Faransa su kasance karfi abun dogaro wajen tabbatar da odar duniya da inganta ci gaban duniya da jagorantar hadin kai tsakanin kasa da kasa. Da yake zantawa ta wayar tarho da shugaba Emmanuel Macron a yau Alhamis, Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Faransa da su hada hannu wajen kare matsayi da ikon MDD da kare ka’idojin cinikayya na duniya da odar duniya da kuma tabbatar da cudanyar bangarori daban daban. Ya kara da cewa, kasar Sin tana daukar Turai a matsayin mai zaman kanta a duniyar dake da kasashe daban daban masu karfi. Ya ce, Sin na goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta karfafa cin gashin kanta...
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; Daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 50. Kididdigar ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta bayyana cewa a cikin sa’oi 24 da su ka wuce an kai shahidai 107 zuwa asibitoci daga cikinsu da akwai wasu shahidai 3 da aka fito da su daga cikin baraguzai; haka nan kuma wasu mutanen da adadinsu ya kai 247 sun jikkata. Ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada tun daga ranar 7 ga watan Oktoba 2023 zuwa yanzu, sun kai dubu 53,762. Sai kuma wadanda su ka jikkata sun kai 1222, 197. Daga sake dawo da yaki akan alummar Gaza, a ranar 18 ga...
A karo na biyu sojojin kasar Yemen sun sanar da kai hari akan filin saukar jirgin sama na “Ben Gorion” a matsayin ci gaba da taimakawa Falasdinawa da sojojin HKI suke yi wa kisan kiyashi. Sanarwar ta sojojin na Yemen ta kuma ce; Makami mai linzamin da su ka harba, wanda ya fi sauti sauri ne, kuma ya sauka a inda aka harba shi, wato filin jiragen sama na Yafa dake karkashin mamaya, da ake kira da “Ben Gorion.” Harin ya tilastawa miliyoyin ‘yan sahayoniya guduwa zuwa Mabuya sanadiyyar gittawar makami mai linzamin da aka harbo daga kasar Yemen. Haka nan kuma an dakatar da zirga-zirgar jirage a filin na Ben Gorion. Da safiyar yau ma dai kakakin sojan kasar...
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta sanar da samun nasarar kuɓutar da wata mace mai shekara 22 da aka yi garkuwa da ita tare da kama wasu mutum biyu. An kama mutum biyun ne da ake zargi da alaƙa da wani mummunan hari a ƙauyen Tashan Randa da ke ƙaramar hukumar Fika. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce samamen da aka gudanar tare da haɗin gwiwar mafarautan yankin, ya nuna wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarin da rundunar take yi na yaƙi da rashin tsaro a jihar. An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Dangote ya sake rage farashin man fetur Sanarwar...
Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana. A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa. Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa. A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa. Dangote ya sake...
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mai suna Mohammed Umar mai shekara 19, mazaunin wata unguwa da ake kira hanyar Abuja a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu bisa laifin sanya tufafi da shigar mata. Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Ngoruje, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya bayyana cewa, mutumin yana ta kai-kawo a cikin harabar cocin Ngurore Lutheran Church of Christ Nigeria. Dangote ya sake rage farashin man fetur An yi Jana’izar Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a Zariya “Kamen matashi ya biyo bayan rahoton da wani mazaunin garin (da aka sakaya sunansa) ya kai hedikwatar ’yan sanda ta Ngurore, bayan ya lura da sintirin wanda ake zargin a cikin harabar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamfanin Dangote wanda ya mallaki matatar mai ta Dangote ya sanar da sake sabon ragin farashin man fetur na N15 a gidajen da ke hulɗa da shi. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce a sakamakon wannan ragi, ‘yan Najeriya za su sayi man fetur a kan farashi kamar haka: Naira 875 kowace lita a Legas; Za a sayar Naira 885 kowace lita a yankin Kudu maso Yamma; A Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya za a sayar kan Naira 895 kowace lita; yayin da za a sayar da shi kan Naira 905 kan kowace lita a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, da Arewa maso Gabas. Waɗannan farashin za su yi aiki ne...
A jawabinsa yayin Kaddamar rabon kayan Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya bayyana cewa “Komawar mu jam’iyyar APC ya nufin kawar da adawa don samar da ci gaba a jihar Kebbi, kuma zamu yi hadin gwiwa da gwamnatin, Gwamna Nasir Idris don amfanin mutanenmu ga irin ayyukan da ya gudanar a dukkan kananan hukumomin 21 na jihar, Wanda shi ne muke kira a ko da yaushe cewa a samar da cigaba ga jama’ar da muke shugabanta,” Inji Sanata Muhammadu Adamu Aliero. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ma’aikatar Tsaro ta fitar da cikakken rahoton nasarorin da ta cimma daga watan Agusta 2023 zuwa Afrilu 2025, inda ta danganta nasarorin da manufofin kamfen din Shugaba Bola Ahmed Tinubu na “Sabuwar Fata.” wato (Renewed Hope). Wannan rahoto ya samu hadin gwiwa daga Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsare-tsare da Hadin Kai tare da Cibiyar Tsare-tsaren Aiki ta Gwamnati (CRDCU). Daya daga cikin manyan nasarorin da rahoton ya nuna shi ne hadin gwiwa da Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (ONSA) don kirkiro da aiwatar da sabuwar manhaja ta hadin gwiwa tsakanin sojoji da fararen hula (CIMIC). Wannan manhaja na da nufin inganta fahimta da aiki tare tsakanin jami’an tsaro da al’umma, musamman a yankunan da...
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana muhimman nasarori da ta cimma a fannin noma da tabbacin isasshen abinci, karkashin shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope. Rahoton rabin wa’adi na aiki daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025, wanda Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsare-Tsare da Hadin Gwiwa ya fitar, ya bayyana ayyukan da Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci ta gudanar domin cika alkawurran yakin neman zaben shugaban kasa. Daya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a rahoton shi ne sabunta da inganta dakunan ajiya na abinci na kasa, wanda ya taimaka wajen rage karancin abinci da daidaita farashi a kasuwanni. Ma’aikatar ta kuma kaddamar da ayyukan gina hanyoyin ban ruwa da tafkunan ruwa domin kara...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gaggawar kulla alaka da kasar Siriya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: A halin yanzu babu wata alaka tsakanin Iran da Siriya, kuma Iran ba ta gaggawar kulla alakar. Ya ce: “Lokacin da gwamnatin Siriya ta ga irin yadda alaka da Iran za ta iya taimakawa al’ummar Siriya, a shirye mahukuntan Iran su amsa bukatar ta.” A wata hira da tashar talabijin ta Al Sharq, Araqchi ya jaddada dimbin damammaki, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gaske take yi wajen kulla kyakkyawar huldar makwabtaka da yankin da ke kewaye, kuma Iran ta bi ta wannan hanya.” Ya kara da cewa: “Iran ta...
Iran ta sanar da lokaci da kuma wurin da za a yi sabon shawarwari tsakanin Iran da Amurka Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: A gobe Juma’a ne za a gudanar da zagaye na biyar na shawarwari tsakanin Iran da Amurka a birnin Roma. A lokacin da ya isa birnin Shiraz don halartar taron yankin kan harkokin diflomasiyya na cikin gida, Araghchi ya bayyana cewa, gudanar da wannan taro da ya fi mayar da hankali kan diflomasiyyar tattalin arzikin yankin, ya shiga cikin tsarin manufofin makwabtaka na Iran, yana mai jaddada cewa, ko shakka babu za ta yi tasiri. Araqchi ya kara da cewa “Za a gudanar da tattaunawar zagaye na biyar ranar Juma’a a Roma...
An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu a birnin Washington na Amurka Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa: An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu bayan da aka harbe su a wajen dakin adana kayan tarihi na Yahudawa da ke birnin Washington D.C. na Amurka. Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito sakataren tsaron cikin gida na Amurka na cewa: An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu a kusa da gidan adana kayan tarihi na Yahudawa da ke birnin Washington, inda ake gudanar da taron kwamitin Yahudawa na Amurka (AJC). Jim kadan bayan harbin, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa an kama wanda ake zargin. Kamfanin dillancin labarai na NBC ya bayar...
An dakatar da ayyukan sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Lod na Isra’ila sakamakon makami mai linzami da aka harba daga Yemen Kafofin yada labaran yahudawan sahayoniyya sun tabbatar da harba makami mai linzami daga kasar Yemen, lamarin da ya tabbatar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa da kuma tashi daga filin jirgin sama na Ben Gurion da ke Lod. Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Yedioth Ahronoth ta rawaito cewa: An dakatar da sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Lod tare da jinkirin jirage masu saukar ungulu, inda aka ce sama da yahudawan sahayoniyya miliyan guda ne suka tsere zuwa maboyar karkashin kasa sakamakon makami mai linzami da aka harba daga Yemen. A...
Shuwagabannin Amurka da Afirka ta Kudu sun yi arangama kan zargin kisan kare dangi a Afirka ta Kudu Fadar White House ta shaida wata zazzafar musayar wuta tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ya musanta zargin da ake masa na cewa Pretoria na cin zarafin ‘yan kasar fararen fata. An yi ganawar ne mako guda bayan da Trump ya yi zargin cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na yin kisan kiyashi ga ‘yan kasarta ‘yan asalin Turai. A yayin tattaunawar da ta samu halartar jami’ai daga bangarorin biyu, shugaban na Amurka ya bukaci ma’aikatansa da su nuna masa faifan bidiyo da ke da alaka da zargin kisan kiyashin, sannan Ramaphosa ya kuma mika...
Daraktan Cibiyar Nazarin Al’adu da Ƙirƙirar Ƙirƙira, Jami’ar Ilorin, Farfesa Olutoyin Ogunade, ya ba da shawarar a bayyana kowace Litinin a matsayin Ranar Al’adu a harabar jami’ar. Farfesa Ogunade ya bayyana hakan ne a lokacin babban bikin ranar al’adu na jami’ar, mai taken “fayyace kyawawan Al’adun mu” a Ilorin. Ya ce wannan shiri zai karfafa wa ma’aikata da dalibai kwarin gwiwar sanya tufafin nasu na asali. A cewarsa, “Tsarin al’adu ba salo ba ne kawai, abin tunawa ne na kakanni da aka tsara. Farfesa Ogunade ya bayyana cewa yin suturar al’ada ita ce bayyana ainihi, tunawa da kuma tsayayya da mamayar al’adu”, ya kara da cewa irin wadannan ayyukan sun tabbatar da tasiri a wasu wuraren...
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da Kamfanin Bayar da Lamuni a Najeriya (CREDICORP), wani muhimmin shiri a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin rage radadin talauci da bunkasar tattalin arziki ta hanyar fadada hanyoyin samun lamuni. Da yake jawabi a wani gangamin wayar da kan al’adu a Kano, Shugaban Kamfanin na CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya jaddada bukatar sauya ra’ayi game da lamuni, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su dauke shi a matsayin wani makami na bunkasa maimakon akasin haka. “CREDICORP, wacce aka kafa a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wata cibiya ce ta kasa da ke aiki don tabbatar da dimokaradiyya ta hanyar samun lamuni ga duk ‘yan...
Kotun ta bayyana cewa mutanen sun aikata laifin sakaci da kuma jawo asarar dukiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Sanata Muhammad Adamu Aleiro, ya raba wa al’ummar mazabar sa kayan tallafi da nufin ba su damar dogaro da kai. Kayayyakin sun hada da babura 150 (Keke NAPEP), babura 114, firiza mai zafin rana guda 302, injin nika 750, famfunan ruwa mai amfani da hasken rana 500, injin dinki 800 da kuma buhunan taki 3,400. Da yake jawabi a wajen bikin raba kayayyakin a karamar hukumar Aleiro ta jihar Kebbi, Sanata Adamu Aleiro, ya ce hakan na daga cikin romon dimokuradiyya ga al’ummar mazabarsa kadai, har ma da jihar. Sanata Aleiro, ya lissafo wasu ayyukan da ya aiwatar a matsayin aikin mazabu a kananan hukumomi takwas na mazabarsa da suka hada...
Kotun ta bayyana cewa mutanen sun aikata laifin sakaci da kuma jawo asarar dukiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Iran ba za ta tattauna ba kan batun inganta sinadarin Uranium din ta a tattaunawar da ta ke da Amurka ba, kuma ba za ta yi watsi da wannan hakki ba a kowe irin dalili. “A halin yanzu muna fuskantar wani matsayin Amurkawa marasa ma’ana wanda ya saba wa hankali. Ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada cewa Iran ta shiga tattaunawa don tabbatar da hakkokin al’ummar kasar, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba a kan wadannan hakkokin. “A ra’ayinmu, batun inganta [uranium] kwata-kwata ba abu ne da za a iya sasantawa ba,” in ji shi. A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata na bayar da amsa karara, kuma...
BudgIT ta buƙaci gwamnati da ta riƙa bin gaskiya da adalci wajen tsara kasafin kuɗi, domin a tabbatar kuɗin gwamnati na yi wa jama’a amfani kai tsaye. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Manyan kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa da dama sun tsawaita dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye, a daidai lokacin da kasar Yemen ta sha alwashin daukar mataki kan kasar. Kamfanin jirgin sama na Air France ya sanar cewa, bayan dakatarwar da aka yi na tsawon watanni, zai ci gaba da dage zirga-zirgar jiragensa zuwa yankunan Falasdinu da aka mamaye har zuwa ranar 24 ga watan Mayu. Da farko Air France ya yi niyyar dawo da zirga-zirgar jirage a wannan makon, amma ya zabi karin jinkirta hakan. Kamfanin Lufthansa da SWISS, Austrian Airlines, Brussels Airlines da Eurowings, su ma sun tsawaita dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa yankunan da aka mamaye. “Saboda halin da ake...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa jarirai dubu 14 a Gaza kan iya rasa rayukansu muddin Irsa’ila ta ci gaba da killace Zirin da hana shigar da kayan agaji. Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher na maida martini ne kan matakin gwmanatin Isra’ila na kyale manyan motoci hudu na agaji su shiga Gaza inda ya ce wannan tamkar”digo ne a cikin teku.” “Akwai jarirai 14,000 da za su mutu a cikin sa’o’i masu zuwa idan ba za mu iya kaiwa gare su ba inji shi. Ya ce motocin agajin da ke dauke da kayan abinci na jarirai da abinci mai gina jiki, suna cikin Gaza amma ba su kai ga farar hula ba saboda gwamnatin Isra’ila...
Rukunin ƙarshe na mahajjatan Jigawa 368 ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi zuwa Saudiyya don aikin hajjin shekarar 2025. A wata hira da aka yi da shi a Radio Nigeria kafin tashinsu a daren Laraba, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa rukunin ƙarshe na mahajjatan 368 sun fito ne daga ƙananan hukumomin Birnin Kudu, Buji, da Taura na jihar. A cewarsa, wannan rukunin ƙarshe ya haɗa da Amirul Hajj na jihar, malamai masu wa’azi, wasu jami’an shiyyoyi da cibiyoyi, da kuma wasu jami’an hukumar. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa, jihar ta kammala aikin tantance mahajjata cikin nasara ba tare da wata tangarda ba. Ya yabawa Gwamnan jihar, Malam Umar...
A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya ce soke hakkin wanda ya shigar da kara ya sabawa ka’ida, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukuncin ba shi da tushe balle makama. Karaye ya ci gaba da cewa, sanarwar kwace shaidar mallakar filin a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 3, 2021, daga ofishin kula da filaye na jihar Kano, an yi ta ne ba tare da an yi shari’a ta adalci ba, wanda hakan ya saba wa tanadin dokar amfani da filaye. Alkalin ya ci gaba da bayyana cewa, takardar shaidar mallakar fili ta asali mai lamba LKN/COM/2017/116 [wacce aka sake shedawa a matsayin LPKN 1188], MLKN01622,...
Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.” Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.” Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko,...
Duka kungiyoyin biyu sun kasa tabuka abin azo agani a wannan kakar a gasar Firimiya Lig, inda Manchester United ke matsayi na 16 Tottenhma na bi mata, amma wannan nasarar da yaran na Postecoglu suka samu ya sa sun samu gurbi kai tsaye a gasar Zakarun Turai ta badi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Duka kungiyoyin biyu sun kasa tabuka abin azo agani a wannan kakar a gasar Firimiya Lig, inda Manchester United ke matsayi na 16 Tottenhma na bi mata, amma wannan nasarar da yaran na Postecoglu suka samu ya sa sun samu gurbi kai tsaye a gasar Zakarun Turai ta badi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Duka kungiyoyin biyu sun kasa tabuka abin azo agani a wannan kakar a gasar Firimiya Lig, inda Manchester United ke matsayi na 16 Tottenhma na bi mata, amma wannan nasarar da yaran na Postecoglu suka samu ya sa sun samu gurbi kai tsaye a gasar Zakarun Turai ta badi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur ta zama zakarar Gasar Europa bayan doke Manchester United da ci ɗaya mai ban haushi. Tottenham ta kafa tarihi a yau Laraba na lashe kofi tun bayan shekara 17 da ta lashe wani babban kofi. Zargin Satar Fasaha: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar BBC Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum Ƙungiyar ta samu nasara ne ta hannun ɗan wasan gabanta, Johnson a minti na 42 kafin tafiya hutun rabin lokaci. Ƙungiyoyin biyu sun kara da juna ne a daren ranar Laraba a filin wasa na San Mamés da ke ƙasar Sifaniya. Hakan na nufin Manchester United ta ƙare kakar wasa ta bana ba tare...

Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar Biliyan ₦2.6bn
A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya ce soke hakkin wanda ya shigar da kara ya sabawa ka’ida, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukuncin ba shi da tushe balle makama. Karaye ya ci gaba da cewa, sanarwar kwace shaidar mallakar filin a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 3, 2021, daga ofishin kula da filaye na jihar Kano, an yi ta ne ba tare da an yi shari’a ta adalci ba, wanda hakan ya saba wa tanadin dokar amfani da filaye. Alkalin ya ci gaba da bayyana cewa, takardar shaidar mallakar fili ta asali mai lamba LKN/COM/2017/116 [wacce aka sake shedawa a matsayin LPKN 1188], MLKN01622,...
Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.” Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.” Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko,...
Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a yau Laraba, inda jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar da ke da ruwa da tsaki ya bayyana cewa, aiwatar da matakan da suka dace bisa “Ayyuka guda goma” na hadin gwiwa da Afirka, ya haifar da sakamako mai kyau, wanda ya zuba babban kuzari ga hadin gwiwar Sin da Afirka. Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, an riga an tattauna tare da kasashen Afirka sau da dama, an kuma amince da tsarin “Kasa daya, manufa daya” wajen tsarawa da aiwatar da matakai. Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo Za A Gudanar Da Baje Kolin...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta ce, a ranar 19 ga wannan wata, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya yi bayani game da yanayin tafiyar tattalin arzikin kasar Sin a watan Afrilu, inda kafofin watsa labaru na kasa da kasa suka yi amfani da kalmomi kamar “wuce zaton da aka yi” da kuma “ da karfi” wajen yabawa tattalin arzikin kasar Sin. Mao Ning ta bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Laraba, inda ta ce, bisa yanayin tinkarar harajin kwastam mai yawa, kasar Sin ta tabbatar da bunkasar cinikayyar kasa da kasa. A farkon watanni 4 na bana, yawan kudin kayayyakin shige da fice na kasar Sin...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi tattalin arziki zamantakewa ysaro da sauransu, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe kuma mu ji ra’ayin masana dangane da su. Dafatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///…Masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da tattaunawa tsakanin JMI da kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Wanda ya zuwa yanzu an gudanar zagaye na 4 na tattaunawar. Har zuwa wannan lokacin dai dukkan bangarorin suna fadar cewa ana samun ci gaba a tattaunawar. Amma bayan kwanaki da ...