Iran Tana Gudanar Da Ayyukan Cibiyoyin Makamashin Nukiliyarta Bisa Maslahar Kasarta Ne
Published: 25th, May 2025 GMT
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya bayyana cewa: Suna yin aiki ne bisa maslahar kasa, kuma ba su yarda da karbar umarni daga waje ba
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, ya ce Iran tana dogara ne kan manufofinta na kasa da kuma manufofinta na koli, kuma ba zata yarda wasu kasashen waje su tsara mata ko bata umurnin abin da zata yi ba.
Kalaman na Islami sun zo ne a lokacin da yake halartar wani taron juyayin tunawa da shahadar marigayi tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian a jiya Asabar, wanda ya samu halartar manyan jami’an siyasa da na diflomasiyya.
A cikin jawabin nasa, Islami ya jaddada cewa asalin kasa da dabi’unta sune abubuwan da zasu tsara tafarkin al’umman Iran, kuma ta hanyar su ne suke neman samun hadin kai don gudanar da hidimar kasa da biyan bukatun al’ummar Iran.
Ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman ci gaba da rike matsayinta a duniya ta hanyar da ta dace da ta samo asali daga manufofinta na kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Yace Huldar kasar Iran Da IAEA Zai Ci Gaba Ne Idan Ta Daina Fuska Biyu
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya fadawa shugaban majalisar tarayyar Turai Antonio Costa, kan cewa huldar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA zai kasance tare da sharudda. Saboda hukumar ta yi watsi da ayyukanta na asali ta koma siyasa. Ta fita daga bangaren kwararru ta zama tana bin bukatun wasu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar ta IAEA a da can ta zuciya guda ce, bata boyewa hukumar wani abu a cikin ayyukanta na makamashin Nukliya. Amma a halin yanzu mun gano cewa hukumar ce take bawa HKI bayanai dangane da ayyukammu na Nikliya ta kuma bada sunaye dadireshin masana fasahar Nukliya na kasar HKI ta zo ta kashesu kai tsaye ko kuma ta yi amfani da wakilanta a cikin Iran don yin wannan aikin.
Banda haka Hukumar ta rufe idanunta kan shirin makaman Nukliya na HKI gaba daya. Daga karshe yace Iran zata sauya yadda take hulda da hukumar a lokaci guda tana bin hanyar diblomasiyya don warware matsalolin da suke rage tsakaninta na hukumar.