Sulhu da ‘Yan Bindiga Ya Fi Zubar Da Jinin Ɗan Adam A Kaduna – Uba Sani Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa

Kazalika, wasu kwararrun, sun ayyna larurar, a matsayin cieon da ke yiawa mutane, kisan mummuke, musamman duba da cewa, bata nuna wasu alamu, idan an kamu da ita, sai dai kawai, ta ci gaba da zama barzana ga lafiyar ‘yan Adam, kamar kamuwa da masu larorin da suka hada da; mutuwar barin Jiki, lalata Koda da kuma rashin iya gani.

An kiyasta cewa, a daukacin fadin duniya, sama da mutane, biliyan 1.3 ke fama da ciwon, wanda kuma rabin adadin wannan alkaluman ne kacal, aka yi masu gwaji aka kuma duba lafiyarsu, yadda ya kamata.

Ciwaon na karuwa, musamman saboda yawan shekarun wadanda suka manyanta kuma larurar, ta karade daukacin fannin tattalin arziki da shafar kudin shiga.

Wani rahoton wani bincike na kiwon lafiya na duniya, ya nuna cewa, za a iya samu karuwar ciwon daga kaso 15 zuwa 20, inda wannan adadin, zai iya kai wa zuwa biliyan 15, a 2025.

Kungiyar da ke wayar da kai kan Hawan Jini ta duniya wato, WHL, ta sanya ciwon a cikin jiren cututtukan da ba a iya yada su.

Hakazalika, Kungiyar Gudanar da Bincike da Tsare-Tsare ta duniya kan kula da kiwon lafiya ta duniya, ta sanar da cewa, ciwon na daga cikin larurorin da ke ci gaba da zama kalubale ga rayuwar wadanda suka kamu da shi wanda kuma Nijeriya na daya daga ciki.

Wani abin tausayarwa shi ne, aka shafe shekaru, kan yadda ciwon ke kara yaduwa, wanda  karuwar aka kiyasta ta kai daga kaso 22 zuwa kaso  44, wanda hakan karuwar ta sha ban ban da a yankunan da ke kasar.

Taken taron na bana, yazo ne tamkar kan gaba ga kasar nan, musamman duba irin yanayin abincin da ake ci a gidajen kasar, kusan a shekaru biyu da suka gabata zuwa yanzu.

Bugu da kari, gidaje da dama a kasar, musamman na talakawa, na ci gaba da fuskantan matsin rayuwa ciki har da aukuwar hauhawan farashin kayan abinci, wanda hakan ya kara zafafa talauci da kuma fuskantar matsalolin rashin lafiya.

An dai shafe shekaru, Nijeriya na ci gaba da fuskantar dimbin kalubale na samun kulawar kiwon lafiyar ‘yan kasar yadda ya kamata, da kuma wawagegen gibin da ya auku a tsakanin mazauna Birane da na Karkara, wajen samun ababen more rayuwa da yin inshorar kiwon lafiyar su.

Koda yake dai, an dan samu wasu nasarori, amma duk da haka, wasu kalubalen, na nan kamar yadda suke a wasu guraren, kamar na wahalar samun magunguna kan farashi mai sauki.

Duba da irin halin fatara a kasar, musamman a tsakanin talakawa, magungunan kula da ciwon, na da matukar tsada, hatta magunnan kula da wasu larorin kamar dai,  ciwon Suga, ba kasafai, masu wannan larurar za su iya sayen magungunan ba, har da, kanannan ma’aikatan a kasar, da ke karbar  sabon mafi karancin Albashin ma’aikatan kasar na Naira 70.

Kazalika, tsadar magungunan, wani babban nauyi ne, akasari ga masu larurar wanda hakan ke tilasata su, dai bin ka’idojin da aka gindaya masu, na ci gaba da kula da lafiyarsu.

Wani rahoto ya bayyana cewa, tsadar magungunan ciwon a kasar nan, ya sha ban ban a wasu sassan kasar, misali, ma’aunin da ke yin gwaji ciwon Suga, ya karu, inda farashinta a yanzu, ya kai kimanin daga Naira 30,000 zuwa Naira 6,000.

Hakazalika, Hukumar Inshorar Kiwon Lafiya ta Kasa, na fuskantar karancin masu shiga cikin tsarin Inshora, duba da cewa, kusan kashi biyar a cikin dari na ‘yan kasar ne, kacal, suka shiga cikin tsarin.

Bugu da kari, ana ci gaba da samun karancin wayar da kan alumma kan ciwon, duba da cewa wasu alkaluma a 2021 sun bayyana cewa, kaso 29 na mutanen da aka yiwa gwajin ciwon, inda kuma kaso 12, aka dora su, kan shan magani wanda kuma kaso uku ne kawai, aka ci nasara na dakile ciwon.

Muna goyon bayan tunawa da ranar ciwon na duniya wadda kuma aka mayar da hankali, mai-makon ayi mata magani kawai, hatta da yadda za a kare aukuwarta da kuma karfafawa jama’a Guiwa kan yadda za su kula da lafiyarsu da kuma zuwa yin gwaji, kan lokaci, domin a gano, ko sun kamu da ciwo tare da kuma yin dubi, ga irin nau’in abincin da suke ci.

Ya zama wajibi, a mayar da hankali, wajen wayar da kan alumma, musaman ta hanyar zuwa yin gwajin  kiwon lafiya game da larurar wanda ta hanak ne, kawai za a iya dakile yaduwarta.

Wasu kwararu, sun bayar da shawarar cewa, ya zama wajbi, mutane sun rinka sanin irin abincin da ya kamata su ci, rage yin amfani da Gishiri, motsa jiki rage shan Barasa da kuma daina shan Taba Sigari.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Hawan jini kiwon lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci

Yadda kasashen yammacin duniya suka ki sauke nauyin dake wuyansu, ya danne wa kasashe masu tasowa hakkinsu. Misali, a lokacin da ake samun bazuwar annobar COVID-19, dimbin kasashen yamma sun yi ajiyar alluran rigakafi a gida, inda suka hana fitar da su zuwa ketare, da musayar fasahohi masu nasaba da su. Sai dai a lokacin, hukumomi masu kula da harkokin kasa da kasa, kamar su Hukumar Lafiya ta Duniya, da Majalisar Dinkin Duniya dukkansu sun kasa tilasta musu sauya manufofinsu. Wannan tsarin kasa da kasa, idan mun bar shi haka ba tare da wani sauyi ba, to, wata rana za mu ga an koma tsarin zalunci na zamanin mulkin mallaka, wanda zai yi barazana ga hakkin rayuwa, da raya kai na al’ummar kasashe masu tasowa. Ta haka za mu san cewa gyara ya riga ya wajaba.

Saboda haka, shawarar inganta jagorancin duniya ta zama wani abun dake biyan bukatun dake akwai a duniyarmu. Wannan ya sa ta samun karbuwa a tsakanin kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka. Inda shahararren dan jarida a Najeriya Lawal Sale, ya rubuta a cikin wani sharhinsa cewa, “Wannan shawara za ta haifar da karin kwanciyar hankali, da tabbas a duniyarmu mai cike da tashin hankali, musamman ma a nahiyar Afirka.” Kana a nasa bangare, Paul Frimpong, wani shehun malami dan kasar Ghana, ya ce shawarar nan “tana tabbatar da cewa tsarin jagorancin duniya ba zai ci gaba da zama karkashin mallakar wasu kasashe masu karfi ba.” Kana dan jaridar kasar Lesotho, Silence Charumbira, ya ce shirin na baiwa kananan kasashe damar zama masu hakikanin ‘yancin kai.

Ta wannan shawara ta inganta jagorancin duniya, za mu iya kara fahimtar halayyar kasar ta Sin. Ko da yake wani yanayin da duniyarmu ke ciki shi ne dishewar tauraron kasashen yamma, amma duk da haka, kasar Sin ba ta neman yin koyi da kasashen yamma wajen yin babakere a duniya. Tana neman gyara, da inganta tsare-tsaren kula da harkokin duniya, ta yadda za ta tabbatar da moriyar dukkan kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa, maimakon kafa wani sabon tsari da ya saba wa tsarin kasa da kasa na yanzu. Dalilin da ya sa haka shi ne babban burin kasar Sin ta fuskar diflomasiyya, shi ne kafa al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil’adama, da kokarin tabbatar da ci gaban harkokinsu na bai daya.

Yayin da karin kasashe ke nuna goyon bayansu ga shawarar kula da al’amuran duniya da kasar Sin ta gabatar, tabbas za mu shaida hadin gwiwar karin mutane a duniya don neman wanzar da adalci, abin da zai haifar da damar tabbatar da daidaito da adalci a duniyarmu. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa  Kisan Kiyashi A Gaza
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000