Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900
Published: 28th, May 2025 GMT
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna a ranar Talata ta ci tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da karin wasu mutum biyar tarar Naira miliyan 900.
Kotun dai ta ci tarar tsohon Gwamnan kan laifin kamawa tare da tsare dattawan kabilar Adara da ke jihar a shekara ta 2019.
Da take zartar da hukuncin a ranar Talata, Alkalin kotun, Mai Shari’a Hauwa’u Buhari, ta amince da bukatar Awemi Dio Maisamari da Karin wasu dattawan kabilar ta Adara su takwas wadanda aka kama bayan kisan basarakensu, Dr Raphael Maiwada Galadima.
Kotun dai ta yi fatali da da’awar wadanda ake kara kan cewa ba ta da hurumin sauraron karar, inda duk da haka ta yanke hukuncin.
An dai gurfanar da El-Rufa’i ne a kashin kansa ba a matsayin Gwamna ba, inda kotun ta ce ta same shi da laifi kan bayar da umarnin yin kamen.
Lauyar masu shigar da karar, Gloria Mabeiam Ballason Esq, ta bayyana hukuncin a matsayin wani babbar nasara kan masu amfani da kujerar mulkin ta hanyar da ba ta dace ba.
An dai kama tare da tsare dattawan na kabilar Adara ne a shakara ta 2019 yayin wani taro da El-Rufa’i ya gayyace su a shekara ta 2019, jim kadan bayan sacewa da kuma kisan da aka yi wa basaraken.
A yayin taron, rahotanni sun ce El-Rufa’i y aba jami’an tsaro umarnin kama Maisamari, wanda shi ne shugaban Kungiyar Ci Gaban Adara, inda ya bayyana shi a matsayin barazanar tsaro a yankin Kajuru.
Dattawan da aka kama dai sun hada da tsohon Kwamishina kuma tsohon jami’in dan sanda, inda aka tsare su har na tsawon watanni, kafin daga bisani babban lauyan gwamnati ya bayar da umarnin sakin su tun da ba a tuhume su a kotu ba.
To sai dai lauyoyin wadanda ake kara sun ki su ce uffan a kan hukuncin kotun.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babbar Kotu
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Labarai Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda October 31, 2025