2025-05-24@20:09:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3436
«ubangiji Allah ya»:
UNICEF ta gabatar da asusun abinci na yara don karfafa zuba jari a cikin manufofi da shirye-shirye. UNICEF ta jajirce wajen yin hadin gwiwa da gwamnatin Jihar Kwara don yaki da rashin abinci mai gina jiki, musamman a lokacin kwana 1000 na farko na rayuwar yara. “Kalubalen shi ne, yawan yara fiye da kashi 40 cikin 100 suna da gwannan matsala kuma kusan yara 300,000 suna fuskantar samun kulawar gaggawa don magance wadannan matsaloli.” Ta danganta dalilan rashin abinci mai gina jiki ga sakamakon talauci, canjin yanayi, rashin samun abinci, da kuma matsalolin tsaro. A nasa jawabin, Gwamna Jihar Kwara, AbdulRaman AbdulRazak, wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Jubril Shaaba Mamman, ya bayyana cewa, tasiri mai kyau game...
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami ya ce duk wanimataki da Tehran ta dauka ya dogara ne kan manufofi da muradun kasar. “Muna ci gaba bisa ga manufofinmu da bukatun kasa,” in ji Eslami Babban jami’in nukiliya na kasar Iran ya jaddada cewa daya daga cikin muhimman nasarorin juyin juya halin Musulunci shi ne yadda kasar ke tsara tafarkinta da kuma yanke hukunci bisa muradun kasa. Eslami ya bayyana cewa, a halin yanzu Iran tana matsayi mai kyau a fannin kimiyya da fasaha na masana’antu, daidai da kasashen da suka ci gaba da suka zuba jarin miliyoyin daloli. Kafin hakan dama Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a ranar Talata ya bayyana cewa “ba...
Kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu ta yi kakkausar suka kan kalaman baya-bayan nan da dan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican Randy Fine ya yi, wanda ya yi kira da a kai wa zirin Gaza hari da makamin Nukiliya. Kungiyar Hamas, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana kalaman dan ‘majalisar a matsayin “laifuffuka” da kuma nuna wariyar launin fata na wasu sassan Amurka. Kungiyar ta bukaci hukumomin Amurka da na majalisar dokokin kasar da su fito fili su yi Allah-wadai da irin wadannan kalamai. Hamas ta jaddada cewa furucin dan majalisar Republican na nuni ne karara ta keta dokokin jin kai na kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva, kuma yana nufin tunzura kai tsaye don amfani...
Ofishin yada labaran Gaza ya bayar da rahoton mutuwar Falastinawa 299 da suka fada cikin mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki, da karancin kayan masarufi da magunguna. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera na cewa, taimakon jin kai na cikin hadarin rubewa saboda haramcin da gwamnatin sahyoniyawan ta kakabawa na shiga Gaza a yayin da al’ummar zirin ke fama da yunwa. Ofishin yada labarai na Gaza ya kara da cewa: Gwamnatin Sahayoniya ta yi ikirarin cewa ta ba da izinin shigar da ayarin motocin agaji yayin da manyan motoci 300 ne kawai suka shiga zirin Gaza. Gwamnatin mamayar ta tilasta wa ayarin motocin agaji bin hanyoyin da ke da hatsarin gaske. Har ila...
Afrika ta kudu ta karyata ikirarin da shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kan cewa kasar ta aikata kisan kiyashi kan manoma fafaren fata a Afrika ta Kudun. Ministan ‘yan sandan Afirka ta Kudu, Senzo Mchunu, ya yi fatali da ikirarin naTrump, yana mai cewa bai da tushe balle makama, in ji jaridar Daily Maverick ta Afirka ta Kudu. Ministan ‘yan sandan Afirka ta Kudu ya fada jiya Juma’a cewa babu wani abu da ya yi kama da hakan a game da ikirarin da Trump na kisan kiyahsin fararen fata a yayin ganawarsa da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa. Trump dai ya nuna wani faifan bidiyo yayin ganawarsa da takwaransa na Afrika ta Kudu, inda har ma ya...
Don haka, CHINADA tana nuna matukar adawarta ga duk wani yunkuri na bayyana shan kwayoyi masu kara kuzari a matsayin wai ci gaban kimiyya, tare da yin kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a harkar wasanni na duniya da su tashi tsaye, su hada kai wajen yin fatali da wasannin da aka amince a sha kwayoyin kara kuzari. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mene ne burinki na gaba game da fim? Burina shi ne a ce yau ga ni ni ma na fito da kudina a ce yau ni ce furodusa ta kaina da kaina, ina rokon ubangiji Allah ya nuna mun ranar nan inada wannan burin sosai ace ni zan yi furodusin fim dina da kaina kuma in sha Allahu muna nan muna rokon Allah yayi mana zabin abin da ya fi zama alkhairi, in sha Allah. Wadanne jarumai ne suke burge ki tun kafin ki fara fim har ma da yanzu da ki ke cikin masana’antar su waye suka zama allon kwaikwayonki? Zan iya ce miki ‘acting’ din kowa yana burge ni kowa da yanayin aktin din da za ka ga...
Abin da ma yake faruwa kenan yanzu wallahi matasan nan maza! namiji babu sana’a babu isasshen ilimin zamani ke wallahi na addini ma wani babu sai ya tattago aure ko da yake an ce adashi suke shiga da an dauka sai zancen kai kudi karshe dai abar iyaye da wahala shi ya sa auren ma baya cin Litinin da Laraba an watse. Abin cewa nan yaro dai ya nutsu ya nemi sana’a da zai dogara da kansa sannan ya iya daukar nauyin iyali kuma a nemi karatu bakin iyawa. Su iyaye suna gujewa yaro abin da zai je ya zo ne ka dauko ‘yar mutane babu sana’a za a ci soyayya ne ina kai ba karatu ba sai kame-kame wani...
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan yarjejeniyar Naira biliyan uku domin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Gombe. Hakan wani bangare ne na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi (L-PRES) wanda Bankin Duniya ke tallafa wa. Shirin L-PRES na da nufin kyautata harkar kiwon dabbobi da sarrafa nama cikin tsafta a jihar. An kulla yarjejeniyar ce tare da kamfanin Lubel Nigeria Limited da wa’adin kammalawa na watanni 9, zuwa watan Fabrairun shekarar 2025. An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin L-PRES da ke G.R.A, a Gombe, inda shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana wannan aiki a matsayin babban ci-gaba a jihar. Sojoji sun kashe mayaƙan...
Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar ISWAP guda biyar sa’annan suka fatattaki ragowar da suka kawo hari a sansanin soji da ke kauyen Gajibo da ke Karamar Hukumar Dikwa a Jihar Borno. Wata majiyar daga Zagàzola makama na cewar, ’yan ta’addan sun kai hari kauyen Gajibo ne da misalin karfe 10:20 na daren ranar alhamis, inda sojojin rundunar Operation Hadin Kai suka yi musayar wata da su suka fatattaki maharan da hadin gwiwar dakarun rundunar ta 134 da suka isa garin. A yayin arangamar ’yan ta’addan sun tsere sun bar nau’uka daban-daban na makamai da suka hada da kuma na’urar sadarwa. Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar da ta’addanci, musamman bisa la’akari da...
Wasu gidajen aure kuwa sai ka samu mijin mai tsananin gyaran jiki da kulawa har ka ga ya tsaya bata lokaci yana gyara fuska da fatar jiki ke in kika gashin sai ki rantse mace ce ba namiji ba, saboda yadda fatarsa ke kyalli da haske, amma idan ka shiga gidansa sai ka tarar da matarsa tamkar mai aikin gidansa ita ma wacce ba ta damu da gyaran jiki ba. Don haka yana da matukar muhimmancin ga kowanne dan Adam ya lazamta wajen gyaran jikinsa, mace ko namiji musamman ma ga ma’aurata. Za Mu Ci Gaba Mako Zuwa Idan Allah Ya Kai mu Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...

Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu
Na yi imanin za mu iya hakan Kuma muna fasahar da za mu iya aiwatar da hakan? Idan aka yi la’akari da albarkatun noma da Nijeriya ke da shi, musamman a cikin amfanin gona irin su rogo da rake, da kuma ta hanyar saka hannun jari kan ababen more rayuwa da fasahar kere-kere, akwai gagarumin yuwuwar bunkasa damar samar da MSG na cikin gida ta hanyar amfani da wadannan albarkatun kasa da ake samu. Muna da injiniyoyi da yawa wadanda za su iya gyara injinan. Muna da dukkan abubuwan da ake bukata a Nijeriya don samar da kayan dandano. Yawanci muna samun abubuwan da duk da muke bukata. Idan kana bukatar ruwa mai yawa, muna da madatsun ruwa a Shiroro,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Iran bata amince da kafa kasashe biyu a matsayin hanyar warware rikicin Falasdinawa ba, saboda kafa kasashe biyu ba zai bawa Falasdinawa hakkinsu ba saboda matukar akwai ikon da HKI take da shi a yakin Falasdinawa ba zasu taba samun hakkinsu ba. Bil’hasali ma kasashe biyu a fahintar mu zai kara wahalar da Falasdinawa ne fiye da hadda suke sha a halin yanzu. Ministan ya bayyana haka ne a lokacinda ya kai ziyara birnin Vatikan na kasar Italiya inda ya gana da Cardinal Pietro Parolin a jiya Jumma’a. Aragchi ya kara da cewa an dade ana maganar raba gardamar ta hanyar kasashen biyu. Al-hali ba wanda ya amince da kafa kasashen biyu...
Gwamnatin kasar Saudiya ta bukaci a amince da samuwar kasar Falasdinu mai zamanta ne kawai hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudiya ya nakalto majiyar Saudia na fadar haka a MDD a jiya Jumma’a. Ta kuma kara da cewa Falasdinawa ba zasu taba amincewa a koresu daga kasarsu ba kamar yadda wasu yahudawa da magoya bayansu suke so. Labarin ya kara da cewa wannan bukatar na zuwa ne a dai-dai kasashen ta Saudia da Faransa suke kokarin gudanar da gagarumin Taro a cikin watan Yuni mai zuwa don bunkasa wannan ra’ayin ta kafa kasashe biyu. Wannan ra’ayin yana kara samun goyon baya a wannan makon musamman bayan da HKI ta kara yawan...
Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka JohnKerry ya bayyana cewa HKI bata isa ta wargaza cibiyoyin makamacin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dilancin labaran IP na klasar Iran ya nakalto Kerry na fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa babban al-amari a cikin duk wani kokari na kauda cibiyoyin Nukliyar kasar Iran ita ce yakin da zai biyo bayan wannan kokarin, Kerry yana magana ne don maida martani ga maganar cewa HKI tana shirin kai hare-hare ko yiyuwan ta kai harehare kan cibiyoyin nukliya kasar Iran idan ta ki amincea ta dakatar da tashe makamashiun uranium a cikin gida a tattaunawan da take da Amurka kan shirin nata. Labarin ya kara da cewa wannan yana tabbatar da...
Tsarin ilimin da ba sai an je makaranta ba Irin wannan nau’in ilmin shi ba tsara shi ake yi ba, hakanan ma ba yana bin wani abinda aka shirya bane dangane da koyarwar. Irin wannan ilimin baya bukatar wani adoI wato ilimin da a ciukin ajin dake makaranta ake koyon shi ba. A waje n eake koyon shi wato manufa ba a wata makaranta ba wadda ake koyarwa domin a samu shi ilimin. Wannan kuma yana faruwa ne idan mutane suka samu karuwa da wasu dabaru ko ilimi daga gida, dakin karatu, ko kum wata kafar sadarwa ta na’urar waya da duk wani abinda za’a iya amfani da shi domin hakan.Bugu da kari irin wannan ilimin ana iya samun...
Rayuwa ta yi wa Talatu atishawar tsaki (ba sunanta na asali ba ne) tun daga shekarar 2018, bayan ta fada harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi a lokacin da ƙawarta ta ƙwaɗaita mata yadda lamarin yake. Ta kasance yarinya mai hazaka mai kimanin shekara 29, kuma ta yi karatu a Jami’ar Kwatano har ta yi aiki a banki na tsawon shekaru biyu kafin ta yi aiki da Kamfanin NNPC da wasu manyan wurare. Sai dai harkar shaye-shaye ta sa ta siyar da motocinta guda biya da kwamfiyuta da wasu abubuwa masu mahimmanci. Halin da wakilin Aminiya ya tsince ta a ciki ke nan a Lungun Gurguwa da ke Lagas Street, Garki Abuja. Ta shaida masa cewa, sam ba ta jin dadin wanna...
Wata mata da ta yi wa masu neman aikin gwamnati damfarar kudi sama da Naira miliyan 250 ta shiga hannun jami’an tsaro. ’Yan sanda sun cika hannu da wannan mata mai suna Iyabode Oluwafemi ne a Jihar Ondo bisa zargin karbar kudaden ta hanyar yaudarar mutane da ta yi wa alkawarin sama masu ayyuka a ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban-daban. A yayin da da yake magana kan wadda ake zargin a ofishinsa da ke Akure, babban birnin jihar, Kwamishinan ’yan sanda a jihar, Wilfred Afolabi, ya ce jami’an runduanr sun yi nasarar kama Iyabode Oluwafemi ne bayan yawan korafin da mutanen da ta damfara suka yi. Ya bayyana cewa da zarar sun kammala bincike za su gurfanar...
Ministan ya kuma zayyano jerin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta kirkiro da nufin zaburar da matasa rungumar kiwon dabbobi, musamman don samun riba ciki har da sama musu hektar noma 51,000, a karkashin hadaka da shirin fitar da kaya na ‘Gulf’ na jihohi da kuma shirye-shiryen farfado da guraren kiwon dabbobi 417 a daukacin fadin kasar nan. “Muna da abubuwan da za mu yi amfani da su a kasar nan, domin yakar yunwa a fadin kasar baki-daya,” in ji Ministan. “Akalla a kasar nan, muna da Shanu kimanin miliyan sha biyar da Tumakai miliyan 60 da Kaji da miliyan 600 da Akuyoyi da miliyan 1.4 da Rakuma miliyan 700,000 tare kuma da kasar noma, amma sai dai har yanzu, kasar...
“Wannan ci gaban zai kuma taimaka wajen kara habaka tattalin ardikin da ke a yankin na Arewa maso Gabas, wanda hakan ya zame mana wajbi, mu sake dawo wajen yin aikin domin aikin ya ci gaba da tafiya,” A cewar Ojulari. Kan batun rikicin da yaki ci, yaki cinyewa a tsakanin Kamfanin na NNPCL da kuma rukunomin Kamfanin Dangote Ojulari ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokari domin a kawo karshen rikicin. “Dangote ya bayar da gagarumar gudunmawa wanda kuma, ya cannaci a yaba masa, za mu kuma yi hadaka domin mu tabbatar da, mun ci gaba da samar da wadataccen Man Fetur ga ‘yan kasar nan,” Inji Sabon Shugaban. “Ana samun masalaha kan komai ne, ta hanyar tattaunawa...
Jaridar “Maariv” ta buga labarin da yake cewa; Tattauanwa a tsakanin “Isra’ila” da kasashen Afirka akan yadda za su bayar da dama ga mutanen Gaza da su yi hijira zuwa can, ta yi isa sosai. Rahoton jaridar na jiya Juma’a ya ci gaba da cewa; Tattaunawar ana yinta akarkashin damar da za a bai wa Mutanen Gaza su yi hijira cikin zabin kansu, zuwa wasu kasashen na Afirka, kuma Amurka tana cikin wadanda ake tattaunawar da ita da wadannan kasashen na Afirka. Haka nan kuma jaridar ta ‘yan sahayoniya ta ce, kasashen da ake tattaunawa da su, sun nuna amincewarsu a matakin na farko ka karbar bakuncin mutanen Gaza. Tattaunawar dai ta kunshi yadda za a gina matsugunan Falasdinawan da...
Dan majalisar Amurkan mai suna Randall Adam Fine wanda yake wakiltar jam’iyyar “Republican” ya sake tunanowa duniya da yadda kasarsa Amurka ta jefa wa biranen Nagasaki da Hiroshima bama-baman Nukiliya a karshen yakin duniya na biyu, ta hanayr yin kira da a jefa wa zirin Gaza irin wadannan makaman na kare dangi. Kungiyoyin Falasdinawa mabanbanta sun yi tir da wannan irin kira na ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kare dangi, suna masu yin kira ga ita kanta majalisar Amurka da ta fito da yi Allawadai da wannan kira wanda yake cike da kiyayya.” Kungiyar Hamas ta bayyana abinda dan majalisar na Amurka ya yi da cewa, ya keta dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva, kamar kuma...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, hadin gwiwa a bangaren ilimi tsakanin Sin da Amurka na moriyar juna ne, kuma Sin ta kasance mai adawa da siyasantar da hadin gwiwar bangaren ilimi. Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Juma’a, lokacin da aka nemi jin ta-bakinta kan matakin gwmnatin Trump na hana jami’ar Harvard daukar dalibai daga kasashen waje. A cewar Mao Ning, ire iren wadannan matakai da Amurka ke dauka za su lalata kima da darajar kasar, tana cewa, Sin za ta nace wajen kare hakkoki da muradun dalibai da malaman kasar dake kasashen waje. Ta kuma jaddada adawar Sin ga bata sunanta da takalarta ba gaira ba dalili, tana mai...
Kasashen Sin da na ASEAN sun kammala tattaunawa game da kafa yankin ciniki cikin ‘yanci na Sin da ASEAN (CAFTA) karo na 3, wanda ke aikewa da sako mai karfi na goyon bayan gudanar ciniki cikin ‘yanci da hadin gwiwa mai bude kofa. A cewar Mao Ning, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, hakika wannan labari ne mai dadi, tana cewa, wani muhimmin mataki ne na rattaba hannu kan yarjejeniyar daukaka yankin a karo na 3. Ta kara da cewa, Sin da kasashen ASEAN, dukkansu masu goyon bayan dunkulewar tattalin arzikin duniya ne da cudanyar bangarori da dama, haka kuma yankin na CAFTA na 3, zai taimakawa Sin da kasashen wajen kara zurfafa budewa juna kofa da samun ci gaba...
“Haƙiƙa muna alfahari da Dr. Sani Dauda Ibrahim da wannan ajin naku, musanman cewa akan ku na fara koyarwa a jami’a, kuma haɗin kan ‘yan wannan ajin ya zama na daban a cikin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, musanman saboda ayyuka da kuka gabatar na ci gaban ilimi a jami’ar Bayero da yadda kuke damuwar da al’amuran ilimi” cewar Dr. Almajir. Taron ya samu halartar Dr. Maimuna Isma’il da ke koyarwa a sashen da sauran mambobin ƙungiya da ‘yan uwa da abokan arzikin Dr. Sani Dauda Ibrahim da aka karrama a wajen taron. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
An gudanar da taron kolin bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari na duniya na shekara ta 2025 jiya Alhamis 22 ga watan nan a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A gun taron, mai taken “rungumar zamanin digital, da samar da ci gaba cikin hadin-gwiwa”, an yi musanyar ra’ayi mai zurfi, tare da cimma matsaya daya kan batutuwa da dama, da bullo da shawarar Beijing ta taron kolin bunkasa kasuwanci da zuba jari na duniya na shekara ta 2025, inda aka yi kira da a fadada hadin-gwiwa a zamanin da muke ciki, da nufin samar da ci gaba da wadata tare. Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai Dan Asalin Jihar Kano...
PDP na fama da rikicin cikin gida mafi muni a tarihin jam’iyyar. Tun lokacin da jam’iyyar ta rasa shugabanci a 2015, ta ci gaba da fuskantar matsaloli wajen magance rikicin da take fama da shi. Ko wani zabe yana zuwa da nashi kalubalan, yana bayyana cin amana na cikin jam’iyya. Zaben 2023, jam’iyyar ta bai wa Atiku Abubakar takarar shugaban kasa, wanda shi dan Arewa ne, inda lamarin ya haifar da fushi na masu ruwa da tsaki daga kudancin kasar nan, musamman daga wajen ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike. Haka ma a daidai lokacin da ake kara fuskantar zaben 2027, wannan yanayi na sake kara bayyana adaidai lokacin da Atiku ke kokarin samun tikitin jam’iyyar. A lokaci guda, Wike...
Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya bayyana shirinsa na ficewa daga Jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ya umarci duka Kwamishinoninsa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da su sauya sheƙa tare da shi ko kuma su sauka daga muƙamansu. Da yake bayani a Uyo babban birnin jihar ranar Alhamis, gwamnan ya ce ba zai yi aiki da waɗanda ya naɗa su, su yi aiki da wata jam’iyya ba. An kama yarinya kan kashe jariri a sansanin ’yan gudun hijira Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Borno Gwamna Eno ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP ba ta da taswirar da za ta tabbatar masa da tafiyarsa cikin kwanciyar hankali a zaɓuka, yana mai cewa yana da yaƙinin cewa...
An dai fara goyon bayan tazarcen Tinubu a wurin taron lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce babu wani gurbi a fadar shugaban kasa a 2027. Barau ya ce, “A bayyane yake a 2027, za mu sami gagarumar nasara, In Sha Allah. Don haka, mu ci gaba da hanyar da muke kai. Mu hada kai da juna, mu yi aiki tare da shugaban kasa, mu yi aiki tare da kowa, mu hada kai a tsakaninmu don samun nasarar da ake bukata.” Sanata Barau ya ci gaba da cewa sauya shekan wasu shugabannin jam’iyyun adawa zuwa APC ya kasance sakamakon aikin Shugaba Tinubu a cikin shekaru biyu kawai da ya shafe a kan karagar mulkin Nijeriya. Kazalika, Ganduje...
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wata yarinya ’yar shekara 15 bisa zargin jefa gawar wani jariri a cikin wani banɗaki da ke sansanin ’yan gudun hijira a Monguno. A cewar wata majiyar ’yan sanda a ranar 22 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 9:15 na safe, an bayar da rahoton cewa, a safiyar wannan rana da misalin ƙarfe 6:00 na safe, an tsinci gawar wani jariri da aka haifa a yashe a ɗaya daga cikin banɗaki da ke sansanin. Kotu ta bai wa EFCC izinin binciken sayar da filin musabaƙar Alƙur’ani na N3.5bn a Kano Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Borno Majiyar ta ce, wacce ake zargin mai suna Yafalmata Alhaji Mustapha mai shekara 15, da...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Matsayin Amurka a cikin ɗakin tattaunawa da Iran ya bambanta da abin da suke shelantawa a waje Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Kalamai da matsayar da jami’an Amurka suka dauka a cikin dakin tattaunawa da Iran suna shan bamban a fili da abin da suke bayyanawa a bainar jama’a, yana mai cewa wannan sabani yana dakushe kwarin gwiwar bangaren Iran da kuma yin barazana ga makomar shawarwarin. A wata hira da ya yi da mujallar Der Spiegel ta Jamus, Takht-Ravanchi ya bayyana kin amincewar da Iran ta yi da bukatar “samar da sifili na Uranium da take sarrafawa”, yana...

Kotu A Iraki Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Tsohon Jami’in Kasar Kan Hannu A Kashe-Kashen Rayukan Jama’a
Kotun kolin kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan wani tsohon jami’in gwamnatin kasar kan laifin aikata kisa da kuma boye gawarwakinsu Kotun kolin kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa a jiya Alhamis kan wani tsohon jami’in gwamnatin kasar kan laifin aikata kisan gilla da kishe-kashe kan ‘yan kasar da kuma boye gawarwakinsu a manyan kaburbura. A cikin wata sanarwa da majalisar koli ta shari’ar kasar Iraki ta fitar ta bayyana cewa: Kotun kolin manyan laifuka ta kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan daya daga cikin jiga-jigan tsohuwar gwamnatin kasar Khairallah Hammadi Abd Jaru bisa laifin aikata kisan gillar da aka yi wa mutane 198 daga yankin Balad a shekara ta 1981, da kuma hannu a cikin aiwatar da...
Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta zargi shugaban gwamantin kasar Siriya al-Julani da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai Kungiyar ta’addanci ta Da’ish ko ISIS ta bayyana shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Abu Muhammad al-Julani a matsayin azzalumi wanda ya sayar da addininsa tare da yin sujjada a kofar shiga wajen kafirai. Ta yi kira ga ‘yan kasashen waje da ke cikin jami’an tsaron Siriya da su tuba su yi watsi da hidimar da suke yi wa azzalumi. A cikin wani sako na addini, a kokarinta na jan hankali masu saurarenta wadanda ta kira su “masu hijira saboda Allah,” kungiyar ta’addanci ta ISIS ta fitar da wani kira na farfaganda ga wasu ‘yan kasashen waje da kuma sabbin hukumomin...
Don haka, ya zama dole kasashen Global South su hada kansu su dauki matakan dakushe duk wani radadi da matakin harajin da Amurka ta dauka zai haifar, ciki har da bunkasawa da inganta cinikayya tsakanin wadannan kasashe,ta hanyar hada kansu domin rage dogaro da tattalin arzikin Amurka ko na kasashen yammaci, wannan yunkuri zai bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin Global South. Kasashen na Global South suna sake zayyana tsarin tattalin arzikinsu ta hanyar bayar da fifiko ga bunkasuwar tattalin arzikinsu da bayar da dama ta bai daya ga kowace kasa wajen taka rawa a harkar kasuwanci. Domin kuwa kasashen sun hade kansu wajen nuna turjiya ga wannan tsarin haraji na Amurka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Dakarun sojojin Najeriya na Operation Haɗin Kai da rundunar sojin sama sun daƙile wani harin haɗin gwiwa da ‘yan ta’addar ISWAP suka kai a garin Damboa, inda suka kashe mahara 16 a wani ƙazamin faɗa da suka yi cikin dare. Mai sharhi kan lamarin tsaro Zagazola Makama ya samu labarin cewa, harin ya afku ne a ranar Juma’a, inda aka kai harin da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar dare da wayewar garin ’yan tada ƙayar bayan sun kai hari a kan gadar Azir da kuma runduna ta 25 da ke Damboa. An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya 2027: ’Yan Najeriya sun yi watsi da takarar Tinubu, sun koka kan tsadar rayuwa Majiyoyin sun ce dakarun da ke...
Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
Kazalika ya kara da cewa, idan za a iya tunawa, Seyi ya kewaya kusan dukkanin jihohin Arewacin kasa nan tare da tallafa wa al’umma da kayan abinci da kudade, musamman a watan Ramadana da ya gabata. A karshe, Sanusi ya yi kira ga matasa maza da mata, kada su bari a bar su a baya a wannan tafiya, domin kuwa kungiya ta kowa da kowa ce, duk mai bukatar yin rajista; kofa a bude take, domin kuwa suna da ofisoshi a kowace jiha, ciki har da babban birnin tarayya Abuja da suke shirin bude kwanan nan ga masu bukatar shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Dakarun sojojin Najeriya na Operation Haɗin Kai da rundunar sojin sama sun daƙile wani harin haɗin gwiwa da ‘yan ta’addar ISWAP suka kai a garin Damboa, inda suka kashe mahara 16 a wani ƙazamin faɗa da suka yi cikin dare. Mai sharhi kan lamarin tsaro Zagazola Makama ya samu labarin cewa, harin ya afku ne a ranar Juma’a, inda aka kai harin da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar dare da wayewar garin ’yan tada ƙayar bayan sun kai hari a kan gadar Azir da kuma runduna ta 25 da ke Damboa. An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya 2027: ’Yan Najeriya sun yi watsi da takarar Tinubu, sun koka kan tsadar rayuwa Majiyoyin sun ce dakarun da ke...
“’Yan kwanakin da suka gabata, na yi wata ganawa da Babban Hafsan Sojin Kasa, inda ya bay-yana min cewa; yana neman akalla jirage marasa matuka kimanin 32, domin kawo karshen wannan ta’addanci, wanda kuma abin da ya fada din gaskiya ne. “Kowane jirgi maras matuki, na kai wa kimanin dala miliyan 5.5, don haka, me yasa ba za mu iya hada karfi da karfe wuri guda mu sayi jiragen ba, don bai wa harkar tsaro fifiko? Har wa yau, ya bayyana kwarin gwiwar cewa; tare da bin tsarin da ya dace da hadin kai a tsa-kanin dukkanin bangarorin gwamnati, za a iya magance wadannan tashin hankula cikin gagga-wa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya, NRC ta tabbatar da kama ma’aikacinta mai suna Gift Eseeli, mai shekara 38, bisa zargin satar waya a Rafa Yard da ke kan hanyar Warri-Itakpe a harabar tashar jirgin ƙasa (WITS) Jihar Delta. Jami’an rundunar Man O’war na shiyyar Railway Command ne suka kama ma’aikacin. A cewar mai magana da yawun hukumar ta NRC, Callistus Unyimadu, binciken farko na nuni da cewa an cire dogayen wayoyin da suke ba da sigina masu sulke mai tsayin 50mm daga na’urorin gefen titin kafin jami’an ‘yan banga ƙarƙashin jagorancin Mista williams Agiake su cafke wanda ake zargin. 2027: ’Yan Najeriya sun yi watsi da takarar Tinubu, sun koka kan tsadar rayuwa Cutar lamoniya ta kama alhazai 99 ’yan...
An dai haifi Dakta Mubarak a Unguwar Hausawa Masallacin Murtala, da ke Karamar Jukumar Kumbotso ta Jihar Kano a Nijeriya. Ya yi karatun Firamare a Hausawa Model ta Jihar Kano; ya yi karatu a Kwalejin Kimiyya ta jeka ka dawo a Kano; daga nan ya tafi zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudi, inda a nan ne ya samu digiri na farko. Ya samu digiri na biyu a fannin noma da gandun daji; sannan ya samu digirin-digirgir kan Agro Paris Tech, Paris, a Kasar Faransa, ya sake yin karatun digiri na biyu a fannin sanin yanayi, Amfanin Kasa da Ayyuka na Muhalli; ya kuma samu digirin-digirgir a Jami’ar Paris a fannin Ecology. Ya yi aiki a...
“Tsohon abin da ake zargin Sanata Natasha – duk karya ne,” in ji Obinna a fili. Har yanzu babu wata sanarwa daga ‘yansanda kan lamarin kama Obinna ya haifar da fushi a tsakanin masu fafutukar kare ‘yancin kafofin watsa labarai, waɗanda ke ganin harin ne kan ‘yancin faɗin albarkacin baki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan Najeriya daga kowane ɓangare daban-daban sun caccaki jam’iyyar APC bisa yanke shawarar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da cewa shekararsa biyu kacal da hawa mulki. Wasu na ganin matakin ya nuna rashin tausayi da rashin damuwa da halin ƙuncin da al’umma ke ciki. Cutar lamoniya ta kama alhazai 99 ’yan ƙasar Indonesiya a Saudiyya NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC Jagororin jam’iyyar APC, gwamnoninta da ’yan majalisa ne suka fito suka nuna goyon bayansu ga Tinubu. Amma jama’a na ganin hakan na nuna burin ci gaba da riƙe madafun iko ne kawai, ba wai taimakon talakawa ba. Ra’ayoyi daga sassa...
Mataimakin Daraktan Ayyuka na Operation Haɗin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da kashe ‘yan ta’addan, yana mai cewa Sojojin na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’addan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mutum daya ya rasu bayan da maniyyata 99 daga kasar Indonesiya suka kamu da cutar lamoniya a yayin da suka tafi aikin Hajji a Saudiyya. Ma’aikatar Lafiya ta kasar Indonesiya ta bayyana damuwa game da yawaitar kamu da cutar ta lamoniya a tsakanin maniyyatan nata. Sanarwar da ta fitar ta bayyana cewa maniyyatan suna samun kulawa a asibitoci a biranen Makka da Madina tana mai kira da ga maniyyatan da su “kiyaye sosai, saboda lamarin na iya kara munana idan ba a yi maganinsa da wuri yadda ya kamata ba. Shugabar Sashen Kiwon Lafiya na na Tawagar Aikin Hajjin Kasar, Liliek Marhaendro Susilo, ta danganta bullar cutar da tsananin zafi da gajiya da kuma cunkoson jama’a sai kuma matsalolin lafiya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin kasar Amurka tana takurawa JMI ne don ta dakatar da shirinta na makamashin nukliya. Don haka ne Amurka take barazana ga Iran a kan cewa idan bata amince a cimma yarjeniya da ita a kan shirinta na makamashin Nukliya ba to ba abinda ya rage sai zabinb soje don wargwaz cibiyotyin makamashin nukliya na kasar Iran. Wannan bukatar itace HKI ta yi ta nanatawa a MDD a kuma duk inda jami’an gwamnatinta suka yi jwabi shekara da shekaru. A halin yanzu Amurka na bin wannan Shirin sau da kafa. Wata majiya ta shaidawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa, a zagayen tattaunawa har 4 wadanda kasashen biyu suka gudanar za’a fahinci cewa Amurka tana bukata a...

Iran: Inda Makiya Kasar Sun San Cewa Zasu Sami Nasara A Kan Iran A Yaki Da Tuni Sunn Farmata Da Yaki
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa da Amurka da HKI sun san cewa zasu sami nasara a kan kasar Iran da yaki da tuni sun fadawa kasar sun kuma mamayeta. Amma saboda wannan tsoron ne suka zabi tattaunawa da ita a kan shirinta na makamshin nukliya. Sannan Shirin makamacin nikliya ma daya ne kacal daga matsalolin da ke tsakanin Iran da HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka. Ya ce akwai matsaloli da dama, tana jirin ta kamala da gudu don ta bullo da wata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya da yamma ya kuma kara da cewa, manufar Iran ta shiga tattaunawa da Amurka ita ce,...
Wani dan majalisar dokokin kasar Amurka daga jam’iyyar Republican daga jihar Florida Randi Fine ya bukaci gwamnatin Amurka ta yi amfani da dimbin makaman N uklkiya da ta tara don kawo karshen yaki a gaza, ta kashe dukkan Falasdinawa a lokaci guda a huta. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Fine yana fadar haka a wata hira da ta hadashi da tashar talabijin ta Foxnews a jiya Alhamis. Ya kuma kara da cewa Amurka bata shiga tattaunawa da sojojin Nazi a yakin dunbiya na biyu ba, bata kuma yi kome bas ai da ta yi amfani da makaman nuklioya a kan Hiroshima da kuma Nagasafi sai kasar Japan ta mika kai ba tare da wasu matsala ba....

Limamin Masallacin Jumma’a A Nan Tehran Ya Yi Magana Dangane Da Kwatar Garin Khurramshar Daga Sojojin Sadam
Mataimakin limamin Jumma’a a nan Tehran Sheikh kum Hujjatul Islam Kazen Sadiki bayan yayio Magana a kan al-amuran tsaron All..da kuma yadda bayin All..da kuma shidanun mutane zasu mutu da kuma yadda sakamakon ko wannansu a gaban All…/ Ya kuma ya gamanar fatahin garin KharramShahr dake kudancin kasar Iran kuma kan iyaka da kasar Iran, wanda dakarun kare juyin juya halin musulunci tare da sauran sojoji da mayakan sa kai suka kwace wannan garin daga hannun sojojin Sdam Hussain a rana irin ta yau wato 2 ga watan Khordod. Banda haka lamamin yana Magana kan littafan da aka buga dangane da wannan gagarumin fatahin da mutanen Iran suka sami a kan wannan garin. Wanda kuma daga wannan nasarar ne ta...

Jam’iyyar APC A Najeriya Ta Tabbatar Da Tinubu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar A Shekara Ta 2027
Jam’iyyar ‘All Progressives Congress” (APC) mai Mulki a tarayyar Najeriya ta tabbatar da shugaban Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar Jam’iyyar a zaben shugaban kas ana shekara ta 2027 mai zuwa. Shafin yada labarai na Afrika ya bayyana cewa a jiya Alhamis ce a taron Jam’iyyar wanda aka gudanar a Abuja, kuma wanda ya zo dai-dai da cika shekaru biyu da zagayensa na farko na shugabancin kasar Jam’iyyar ta nada shi Shugaba Bola Ahmed Tinubu dan shekara 73 a duniya a matsayin dan takararta a zaben na shekara ta 2027, don ya sami damar kamala shirinsa nag yare-gywaren tattalin arzikin kasar da y afara. Shugaban Tinubu dai ya kara farashin man fetur a ranar da ya hau kan kujerar...
Ma’anar addu’ar ita ce, “Allah ina neman tsari da kai, ya Ubangiji mai girma, da hasken fuskarka (yadda ya dace da shi) mai girma, da sarautarka dauwamammiya, daga shaidani abin jefewa, da sunanka Allah, Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad (SAW) da ‘ya’yan gidansa, ka yi aminci a gare shi. Allah ka gafarta mun zunubina, Allah ka bude mun kofofin rahamarka.” Ba a Harami ba kawai, a kowane Masallaci an so a karanta daga kan salatin Annabin nan zuwa karshen addu’ar idan za a shiga. Idan mutum bai iya wannan addu’ar ba, ya yi a’uziyya da bisimillah da salatin Annabi (SAW) da kuma addu’ar da ya iya. Ana so da zarar mutum ya shiga idanunsa sun kalli Dakin Ka’aba,...
Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Umar Iliya Damagun, ya yi Allah Ya isa ga masu zargin da yi wa jam’iyya mai mulki, APC, aiki. Wasu masu ruwa da tsaki a PDP na zargin cewa Damagun da yi wa jam’iyyar zagon ƙasa APC, shi ya sa yake rura wutar rikicin cikin gida da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a PDP. Amma a yayin wata hira da ya yi da BBC, Damagun ya yi fatali da zargin, yana mai cewa Allah Zai saka masa tsakaninsa da masu yi masa wannan ƙazafi. “Allah Ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan ƙazafi, kuma Allah Zai yi mana shari’a,” in ji shugaban na PDP, wanda ake zargi da zama ɗan-amshin-shatan...
Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa. Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa. ‘Yan mata suna cikin hadari, galibi ana tilasta musu auren wuri ko aikin gida ko aikin jima’i maimakon a ba su damar koyo. Wata kwararriyaa fannin ilimi da ke zaune a Jos, Jihar Filato, Misis Peace Pernam, ta ce, “Ilimi wata hanya ce ta rayuwa mai muhimmanci da ke kawar da fatara, rage matsalar tsaro, da samar da ci gaban kasa, duk da haka, ga miliyoyin yara a yankin Arewa...
Babban Mashawarcin Tsaro na Kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa an kashe ’yan ta’adda sama da 13,000 a fadin Najeriya daga lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hau mulki a watan Mayun 2023 zuwa yanzu. Ribadu, yayin da yake jawabi a taron Koli na Jam’iyyar APC a zauren taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ya bayyana cewa duk da an samu ci-gaba mai sosai wajen magance matsalar rashin tsaro, yanayin sarƙaƙiyar tsaro ya sa a mafi yawan lokaci jama’a ba sa iya gane waɗannan nasarori nan take. Ribadu ya bayyana cewa an kashe jimillar ’yan tada kayar baya da ’yan fashin daji 13,543, yayin ayyuka daban-daban da sojoji da sauran hukumomin tsaro suka gudanar a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Me sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya ɓangaren adawa suka zaɓi inuwar Jam’iyyar ADC domin haɗa hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC daga mulki? Da daren Talata ne dai manyan ’yan adawar, waɗanda suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma ɗan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a ƙarƙashin inuwar ADC din. Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya riƙe wannan haɗaka? Shin waɗannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Me sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya ɓangaren adawa suka zaɓi inuwar Jam’iyyar ADC domin haɗa hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC daga mulki? Da daren Talata ne dai manyan ’yan adawar, waɗanda suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma ɗan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a ƙarƙashin inuwar ADC din. Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya riƙe wannan haɗaka? Shin waɗannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da...
Kimanin kwanaki biyu ke nan ana jita-jitar cewa sojoji a sun yi nasarar hamɓarar da gwamnatin Shugaba Kasar Kwadebuwa, Alassane Ouattara. Jita-jitar ta fara yaɗuwa ne tun bayan jin ƙarar harbe-harbe a yankunan ƙasar da dama musamman a babban birnin ƙasar na Abijan. Ba mu tilasta wa kowa ya koma APC ba — Tinubu Jami’an tsaron Zulum sun buɗe wa Boko Haram wuta a Maiduguri Wasu rahotanni na nuna cewa an samu ɓarkewar rikici ne a cikin birnin na Abijan, lamarin da ake hasashen ya yi sanadiyar masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Ouattara kimanin mutum 33 cikin kwana biyu. Sai dai har ya zuwa yanzu babu wani tabbataccen rahoton daga majiya mai ƙarfi da ke bayyana hakikanin abin da ke...

Masanan Najeriya Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Tinkarar Kalubalen Harajin Kwastam Na Amurka
Wasu masana a tarayyar Najeriya sun jinjinawa yadda Najeriya da Sin suka daga dangantakarsu zuwa huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni a bara, matakin da ya tabbatar da goyon bayansu ga kokarin tinkarar kalubalen karin harajin kwastam da Amurka ke dora musu bisa radin kai. Kwanan baya, an gudanar da taron tattaunawa kan yadda za a tinkari harajin kwastam da Amurka ke kakabawa sauran kasashe a birnin Abuja hedkwatar Najeriya, inda babban darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Najeriya Charles Onunaiju ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da Najeriya bisa dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka, da shawarar “ziri daya da hanya daya” da dai sauransu, ba ingiza bunkasuwar manyan ababen more rayuwa a Afirka kadai...
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya caccaki masu cewa gwamnatinsa na ingiza ’yan Najeriya wajen bin tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa ba za ka iya zargi mutane kan zaɓar jam’iyya ba. Da yake jawabi a wajen taron ƙoli na jam’iyyar APC karo na farko da aka yi a ranar Alhamis, da ya gudana a fadar shugaban ƙasa a Abuja, shugaban ya ce “jam’iyya ɗaya ce ke mulki”. Jami’an tsaron Zulum sun buɗe wa Boko Haram wuta a Maiduguri An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe “Ga waɗanda har yanzu suke tunanin fita daga jam’iyyarsu, ƙasar nan taku ce, ku riƙe ta, ga masu maganar tsarin jam’iyya ɗaya, jam’iyya ɗaya ce ke...
Modric, ya lashe kofuna 28 da suka hada da gasar zakarun Turai 6 da Laliga 4 tun lokacin da ya koma Real daga Tottenham a shekarar 2012. “Na zo ne a shekarar 2012 tare da fatan sanya rigar yan wasan da suka fi fice a duniya da kuma burin samun manyan nasarori, Real Madrid ta canza rayuwata a matsayina na dan wasan kwallon kafa da kuma mutum, ina alfahari da kasancewata a daya daga cikin mafi kyawun kulob a tarihi” inji shi. Real za ta bude gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa da Al-Hilal ta Saudi Arabiya a ranar 18 ga watan Yuni, sannan kuma za ta kara da Pachuca ta Mexico da RB Salzburg ta...
A gun taro karo na 28 na kwamitin madatsar ruwa na duniya da ake gudanarwa, an bayyana cewa kasar Sin ta cimma nasarar gina madatsun ruwa masu kunshe da fasahar zamani da dama, kuma ci gaban da take samu a bangaren kirkire-kirkire, da nasarorin da take samu a fannin gudanar da harkoki masu masaba da hakan na jawo hankalin kasa da kasa. Ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta kyautata aikin na’urorin sa ido kan kananan madatsun ruwanta dubu 51, da zummar kafa tsarin taurarin dan Adam, da jiragen sama marasa matuka, da na’urar rada, da tasoshin doron kasa, da na’urorin karkashin ruwa, da na’urorin sa ido bai daya. Ban da wannan kuma, Sin ta fara aikin gwaji a wurare...
Arewa Tech Fest, taron koli ne na fasaha da kirkire-kirkire na kwanaki uku, wanda ke tattaro ’yan kasuwa, kwararru masu fasaha, masu zuba jari, da masu tsara manufofi don bunkasa fasahar kere-kere a Arewacin Nijeriya. El-Rufai ne da kansa ya shirya bikin. Minista Tijani, wanda ya gabatar da jawabi mai mahimmanci, ya yi magana a kan sauye-sauye na zamani da kirkire-kirkire a sassan gwamnati da masu zaman kansu na Nijeriya. El-Rufai ya isa wurin taron ne a makare, inda ya nemi afuwar mahalarta taron tare da bayyana cewa ya samu jinkiri saboda wani muhimmin taron siyasa da aka gudanar a yammacin jiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Ko shakka babu, ba wani tsari ko salon ciyar da al’umma gaba da za a iya cewa zai dace dari-bisa-dari da dukkanin sassan duniya bai daya, amma duk da haka, daukacin kasashen duniya za su iya koyi daga kwarewar kasar Sin, da tsawon lokacin da ta shafe tana gwada dabarunta na ci gaba wadanda suka haifar da da mai ido. Yayin da a nasu bangare sassan kasa da kasa ke da damar tsara manufofi daidai da burikansu da yanayin da suke ciki. Wasu masharhanta na ganin kwarewar da Sin ke samarwa duniya, tamkar sabon zabi ne ga sassa masu fatan gwada wani salo na bunkasa kasashe masu tasowa, wanda ya sabawa na yammacin duniya, don haka sassa daban daban ke...
Jami’an tsaro da ke raka ayarin motocin Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum sun buɗe wuta kan ’yan Boko Haram a hanyarsu daga Gamboru Ngala zuwa Maiduguri bayan wani rangadi na kwanaki uku. Kodayake ba a san dalilin ’yan ta’addan ba, amma jami’an tsaron ayarin motocin sun bi su inda suka yi ta musayar wuta na kusan rabin sa’a tsakanin ƙarfe 12:50 na rana zuwa ƙarfe 1:30 na rana. An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin ne sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin. Wata...
Jami’an tsaro da ke raka ayarin motocin Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum sun buɗe wuta kan ’yan Boko Haram a hanyarsu daga Gamboru Ngala zuwa Maiduguri bayan wani rangadi na kwanaki uku. Kodayake ba a san dalilin ’yan ta’addan ba, amma jami’an tsaron ayarin motocin sun bi su inda suka yi ta musayar wuta na kusan rabin sa’a tsakanin ƙarfe 12:50 na rana zuwa ƙarfe 1:30 na rana. An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin ne sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin. Wata...
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa. “Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su. Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida. Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39. Sanarwar ta MDD ta ci gaba...
Nahiyar Afirkan a karkashin tarayyar Afirka ta kafa cibiyar dake kula da sararin samaniya domin tattara bayanai, wacce ke da matsuguni a birnin “alkahira’ na Masar. Sabuwar cibiyar dai ta fara aiki ne a watan da ya gabata,kuma za ta rika musayar bayanan da take tattarawa da cibiyoyin kasashen da suke a fadin nahiyar. Haka nan kuma cibiyar za ta kyautata ayyukanta ta hanyar harba taurarin dan’adam a sararin samaniya da kafa cibiyoyin bibiyar yanayi domin yin musayarsu da kasashen nahiyar da kuma wajenta.
Jaridar ‘yan sahayoniya ta “Ma’ariv’ ta buga labarin da yake cewa; Isra’ila tana fuskantar matsalar diplomasiyya saboda ci gaba da yakin Gaza. Jaridar ta kuma ce; A halin yanzu “Isra’ila” tana fuskantar abinda ta kira “Tsunami Na Diplomasiyya” saboda yakin da take ci gaba da yi a Gaza. Haka nan kuma jaridar ta soki gwamnatin Netanyahu tare da bayyana ministan harkokin waje Gadion Sa’ir wanda ta ce, ba abinda ya dame shi kamar ci gaba da zama akan kujerarsa, da cewa; Ba ya fahimtar girman musifar da take tunkaro Isra’ila.” Har ila yau, jaridar ta yi suka ga ministar sufuri Miri Rigiv da cewa saboda ta’annuti, ta ki yin furuci da cewa Isra’ila tana karkashin takunkumin zirga-zirga ta sama, kuma...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci Sin da Faransa su kasance karfi abun dogaro wajen tabbatar da odar duniya da inganta ci gaban duniya da jagorantar hadin kai tsakanin kasa da kasa. Da yake zantawa ta wayar tarho da shugaba Emmanuel Macron a yau Alhamis, Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Faransa da su hada hannu wajen kare matsayi da ikon MDD da kare ka’idojin cinikayya na duniya da odar duniya da kuma tabbatar da cudanyar bangarori daban daban. Ya kara da cewa, kasar Sin tana daukar Turai a matsayin mai zaman kanta a duniyar dake da kasashe daban daban masu karfi. Ya ce, Sin na goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta karfafa cin gashin kanta...
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta sanar da samun nasarar kuɓutar da wata mace mai shekara 22 da aka yi garkuwa da ita tare da kama wasu mutum biyu. An kama mutum biyun ne da ake zargi da alaƙa da wani mummunan hari a ƙauyen Tashan Randa da ke ƙaramar hukumar Fika. A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce samamen da aka gudanar tare da haɗin gwiwar mafarautan yankin, ya nuna wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarin da rundunar take yi na yaƙi da rashin tsaro a jihar. An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Dangote ya sake rage farashin man fetur Sanarwar...
Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana. A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa. Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa. A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa. Dangote ya sake...
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mai suna Mohammed Umar mai shekara 19, mazaunin wata unguwa da ake kira hanyar Abuja a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu bisa laifin sanya tufafi da shigar mata. Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Ngoruje, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya bayyana cewa, mutumin yana ta kai-kawo a cikin harabar cocin Ngurore Lutheran Church of Christ Nigeria. Dangote ya sake rage farashin man fetur An yi Jana’izar Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a Zariya “Kamen matashi ya biyo bayan rahoton da wani mazaunin garin (da aka sakaya sunansa) ya kai hedikwatar ’yan sanda ta Ngurore, bayan ya lura da sintirin wanda ake zargin a cikin harabar...
“Hukumar ta amince da ƙirƙiro sashen AI a ƙarƙashin ɓangaren fasahar sadarwa na hukumar domin cin ribar AI da fasahar da take ɗauke da ita da kuma magance ɓarnar da fasahar ka iya kawowa a lokutan zaɓe” a cewar sanarwar Wannan matakin da INEC ta ɗauka dai ya biyo bayan tarurruka da dama da ma’aikatan hukumar suka halarta a sassa daban-daban na duniya a kan AI inda ƙasashen Afirka da dama suka tattauna domin rungumar sabuwar basirar ta hanyar yin amfani da ita a inda ya dace da kuma maganin yin amfani da ita wajen kawo cikas a zaɓe musamman yaɗa labarun ƙarya a lokutan zaɓe da sauransu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Kamfanin Dangote wanda ya mallaki matatar mai ta Dangote ya sanar da sake sabon ragin farashin man fetur na N15 a gidajen da ke hulɗa da shi. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce a sakamakon wannan ragi, ‘yan Najeriya za su sayi man fetur a kan farashi kamar haka: Naira 875 kowace lita a Legas; Za a sayar Naira 885 kowace lita a yankin Kudu maso Yamma; A Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya za a sayar kan Naira 895 kowace lita; yayin da za a sayar da shi kan Naira 905 kan kowace lita a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, da Arewa maso Gabas. Waɗannan farashin za su yi aiki ne...
A jawabinsa yayin Kaddamar rabon kayan Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya bayyana cewa “Komawar mu jam’iyyar APC ya nufin kawar da adawa don samar da ci gaba a jihar Kebbi, kuma zamu yi hadin gwiwa da gwamnatin, Gwamna Nasir Idris don amfanin mutanenmu ga irin ayyukan da ya gudanar a dukkan kananan hukumomin 21 na jihar, Wanda shi ne muke kira a ko da yaushe cewa a samar da cigaba ga jama’ar da muke shugabanta,” Inji Sanata Muhammadu Adamu Aliero. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...

Ma’aikatar Ayyuka Ta Bayyana Nasarorin Tsakiyar Zango Karkashin Shirin “Renewed Hope” na Shugaba Tinubu
Gwamnatin Tarayya ta fitar da cikakken rahoto na tsakiyar zangon mulki da ke bayyana muhimman nasarorin da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ta cimma daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025. Rahoton, wanda Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsare-Tsare da Daidaita Ayyuka ya gabatar, ya bayyana ci gaba mai ma’ana da aka samu a fannin gine-ginen ababen more rayuwa, musamman hanyoyi, karkashin shirin Renewed Hope Action Plan na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Daya daga cikin manyan nasarorin da rahoton ya nuna shi ne ci gaba da aiwatar da shirin Highway Development and Management Initiative (HDMI), wanda ke amfani da tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu (PPP). Wannan tsarin ya ba da damar janyo hannun jari...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An gudanar da Jana’izar Malam Maikudi Umar (Cashman) Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a garin Zariya, Jihar Kaduna. Marigayin dan shekaru 62, jarumi ne, mai shirya finafinai kuma ma darakta da ke gudanar da aikace aikacen sa a masana’antar Kannywood da Nollywood. Dan uwan mamacin, Abdul Azeez Muazu, Talban Tudun Jukun yace Umar ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a Asibitin Koyarwa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya. Yace rasuwar ya faru ne a daren ranar laraba sailin da akayi Jana’izar sa a ranar Alhamis a makabarta dake Zariya. Shi dai Marigayin har ilau malami ne a Kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zariya. Ya rasu ya bar yan uwanshi da dama Hoton...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gaggawar kulla alaka da kasar Siriya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: A halin yanzu babu wata alaka tsakanin Iran da Siriya, kuma Iran ba ta gaggawar kulla alakar. Ya ce: “Lokacin da gwamnatin Siriya ta ga irin yadda alaka da Iran za ta iya taimakawa al’ummar Siriya, a shirye mahukuntan Iran su amsa bukatar ta.” A wata hira da tashar talabijin ta Al Sharq, Araqchi ya jaddada dimbin damammaki, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gaske take yi wajen kulla kyakkyawar huldar makwabtaka da yankin da ke kewaye, kuma Iran ta bi ta wannan hanya.” Ya kara da cewa: “Iran ta...
Shuwagabannin Amurka da Afirka ta Kudu sun yi arangama kan zargin kisan kare dangi a Afirka ta Kudu Fadar White House ta shaida wata zazzafar musayar wuta tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ya musanta zargin da ake masa na cewa Pretoria na cin zarafin ‘yan kasar fararen fata. An yi ganawar ne mako guda bayan da Trump ya yi zargin cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na yin kisan kiyashi ga ‘yan kasarta ‘yan asalin Turai. A yayin tattaunawar da ta samu halartar jami’ai daga bangarorin biyu, shugaban na Amurka ya bukaci ma’aikatansa da su nuna masa faifan bidiyo da ke da alaka da zargin kisan kiyashin, sannan Ramaphosa ya kuma mika...
Ya kuma ce suna sane da cewa yajin aikin zai iya shafar jama’a musamman a Katsina. “Ba ma’aikata kaɗai muke ba – iyaye ne mu kuma masu ciyar da iyali. Abin da muke nema kawai haƙƙinmu ne,” in ji shi. Yajin aikin zai iya haifar da tsaiko wajen samun wutar lantarki a yankin, musamman a Katsina inda yajin aikin ke da zafi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da Kamfanin Bayar da Lamuni a Najeriya (CREDICORP), wani muhimmin shiri a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin rage radadin talauci da bunkasar tattalin arziki ta hanyar fadada hanyoyin samun lamuni. Da yake jawabi a wani gangamin wayar da kan al’adu a Kano, Shugaban Kamfanin na CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya jaddada bukatar sauya ra’ayi game da lamuni, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su dauke shi a matsayin wani makami na bunkasa maimakon akasin haka. “CREDICORP, wacce aka kafa a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wata cibiya ce ta kasa da ke aiki don tabbatar da dimokaradiyya ta hanyar samun lamuni ga duk ‘yan...
Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Sanata Muhammad Adamu Aleiro, ya raba wa al’ummar mazabar sa kayan tallafi da nufin ba su damar dogaro da kai. Kayayyakin sun hada da babura 150 (Keke NAPEP), babura 114, firiza mai zafin rana guda 302, injin nika 750, famfunan ruwa mai amfani da hasken rana 500, injin dinki 800 da kuma buhunan taki 3,400. Da yake jawabi a wajen bikin raba kayayyakin a karamar hukumar Aleiro ta jihar Kebbi, Sanata Adamu Aleiro, ya ce hakan na daga cikin romon dimokuradiyya ga al’ummar mazabarsa kadai, har ma da jihar. Sanata Aleiro, ya lissafo wasu ayyukan da ya aiwatar a matsayin aikin mazabu a kananan hukumomi takwas na mazabarsa da suka hada...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa jarirai dubu 14 a Gaza kan iya rasa rayukansu muddin Irsa’ila ta ci gaba da killace Zirin da hana shigar da kayan agaji. Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher na maida martini ne kan matakin gwmanatin Isra’ila na kyale manyan motoci hudu na agaji su shiga Gaza inda ya ce wannan tamkar”digo ne a cikin teku.” “Akwai jarirai 14,000 da za su mutu a cikin sa’o’i masu zuwa idan ba za mu iya kaiwa gare su ba inji shi. Ya ce motocin agajin da ke dauke da kayan abinci na jarirai da abinci mai gina jiki, suna cikin Gaza amma ba su kai ga farar hula ba saboda gwamnatin Isra’ila...
Masana sun yi kira ga hukumomi da su yi bincike mai zurfi don gano waɗanda ke taimaka wa Boko Haram sannan a hukunta su domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya ce soke hakkin wanda ya shigar da kara ya sabawa ka’ida, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukuncin ba shi da tushe balle makama. Karaye ya ci gaba da cewa, sanarwar kwace shaidar mallakar filin a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 3, 2021, daga ofishin kula da filaye na jihar Kano, an yi ta ne ba tare da an yi shari’a ta adalci ba, wanda hakan ya saba wa tanadin dokar amfani da filaye. Alkalin ya ci gaba da bayyana cewa, takardar shaidar mallakar fili ta asali mai lamba LKN/COM/2017/116 [wacce aka sake shedawa a matsayin LPKN 1188], MLKN01622,...
Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.” Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.” Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko,...
A bangaren masaku ma, masakar Zhejiang Yingfeng ta samu bunkasar ayyukanta musamman wajen rage yawan abubuwan da ba a bukata domin fitar da kayan da ake sarrafawa da tsafta, bayan ta rungumi amfani da fasahar zamani. Haka nan bangaren rina kaya ya samu ci gaba da kusan kashi 80 zuwa 95 cikin dari. Bangaren aikin gona shi ma yana samun habaka bisa amfani da fasahohin zamani wajen ayyukan noma, da kula da gonaki, da sayar da amfanin gona da sauransu. A garin Zhangzhuang dake gundumar Shangshui ta birnin Zhoukou dake lardin Henan na tsakiyar kasar Sin, ana iya ganin yadda ake amfani da na’urori da fasahohin zamani a ayyukan gona a bangaren zuba taki da ban-ruwa, da taraktocin noma da...

Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar Biliyan ₦2.6bn
A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya ce soke hakkin wanda ya shigar da kara ya sabawa ka’ida, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukuncin ba shi da tushe balle makama. Karaye ya ci gaba da cewa, sanarwar kwace shaidar mallakar filin a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 3, 2021, daga ofishin kula da filaye na jihar Kano, an yi ta ne ba tare da an yi shari’a ta adalci ba, wanda hakan ya saba wa tanadin dokar amfani da filaye. Alkalin ya ci gaba da bayyana cewa, takardar shaidar mallakar fili ta asali mai lamba LKN/COM/2017/116 [wacce aka sake shedawa a matsayin LPKN 1188], MLKN01622,...
Ya ƙara da cewa, “Kuma wajibi ne a gare mu, a matsayin mu na ƙwararrun ma’aikatan hulɗa da jama’a, mu daidaita da wannan lokaci ta hanyar amfani da dabarun sadarwa masu ɗauke da ƙwarewa, ƙima, da haɗin kai, domin ƙarfafa gwiwar al’ummar mu, a gida da waje, su shiga cikin farfaɗo da tattalin arzikin wannan babbar ƙasa.” Idris ya bayyana cewa aikin sake fasalin tattalin arziki ya faro ne tun daga ranar farko da Shugaban Ƙasa Tinubu ya hau mulki, lokacin da aka cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗi — matakan da ya bayyana a matsayin “tushen farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar nan.” Ya haƙƙaƙe da cewa waɗannan matakai sun haifar da wahalhalu da farko,...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi tattalin arziki zamantakewa ysaro da sauransu, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe kuma mu ji ra’ayin masana dangane da su. Dafatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///…Masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da tattaunawa tsakanin JMI da kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Wanda ya zuwa yanzu an gudanar zagaye na 4 na tattaunawar. Har zuwa wannan lokacin dai dukkan bangarorin suna fadar cewa ana samun ci gaba a tattaunawar. Amma bayan kwanaki da ...
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta soki yunkurin da Amurka ke yi na hana kasashen duniya amfani da sashen harhada na’urorin laturoni na Chips kirar kasar Sin. Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a Larabar nan, ta kira yunkurin na Amurka da cin zali daga bangare guda, da baiwa kasuwa kariya, matakin da tabbas zai illata tsarin ayyukan masana’antun kira da rarraba sassan semiconductor na duniya. Kazalika, kakakin ma’aikatar ya ce a baya bayan nan sashen lura da harkokin cinikayya na Amurka ya fitar da wasu bayanai, ta fakewa da batun wai ana keta dokokin Amurka na fitar da hajoji, da nufin haramtawa sassan kasa da kasa amfani da sassan na’urorin Chips masu kunshe da manyan fasahohin sarrafa bayanai...
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 3 ga watan Yuni, 2025 domin yanke hukunci kan shari’ar BBC da mawaƙi Abdul Kamal. Tunda farko Abdul, ya maka kafar ne a kotu, inda yake neman ta biya shi diyyar Naira miliyan 120, kan zargin amfani da waƙarsa a shirinsu na “Daga bakin mai ita” ba tare da izininsa ba. Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum A zaman shari’ar na ranar Litinin, lauyan mai ƙara, Barista Bashir Ibrahim Umar, ya gabatar da makaɗin waƙar, Muhammad Sani Uba a matsayin ɗaya daga cikin shaidun wanda ke ƙara. Makaɗin ya tabbatar wa kotu cewa shi ne,...
Sojojin HKI sun bude wuta nag aske kan jami’an diblomasiyya na wasu kasashen Turai wadanda suke kokarin shiga sansanin yan gudun hijira na Jenin don galin yadda rayuwa take tafiya a cikinsa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jamilan diblomasiyya wadanda suke ziyarar sansanin yan gudun hijiran a yau Laraba dai sun hada da jakadun kasashen Austria, Brazil, Bulgaria, Canada, Chile, China, Masar, Faransa, India, Japan, Jordan, Lithuania, Mexico Morocco, Poland, Portugal, Romania, Rasha, Sri Lanka, Spain, Turkey, tarayyar Turai (EU), da kuma Burtaniya. Tare da su akwai wakilai daga wasu kasashen duniya da kuma yan jarida. Ma’aikatar harkokin wajen gwamnatin Falasdinawa ne ta shiryawa wadannan kasashen ziyara zuwa wannan yankin na yamma da kogin Jordan don...
Kwamiti mai kula da al-amuran harkokin waje a kasar Burtaniya tana matsawa sakataren harkokin wajen kasar David Lammy kan cewa ya amince da kasar Falasdinu mai zaman Kanata. Jaridar Telegram ta kasar Burtaniya ta nakalto wannan rahoton a yau Laraba, ta kuma kara da cewa Dan majalisa Emily Thomberrry ya kara da cewa wannan mataki na farko ne, idan Lammy ya bada wannan sanarwan a cikin wata mai zuwa a lokacin haduwarsa da Saudiya da Faransa a wani babban taro wanda zai bada damar daukar matakai nag aba. Jaridar tace, wannan maganar tana zuwa ne bayan da sakataren ya dakatar da tattaunawa ta harkokin kasuwanci da HKI, da kuma kiran jakadan HKI a London don gabatar da korafinsa kan sake...