Yemen: Matukar Gaza Tana Fuskantar Yaki, To Babu Tsaro A HKI
Published: 30th, May 2025 GMT
Miliyoyin Mutanen Kasar Yemen sun yi gangamin a jihohi 14 na fadin kasar domin nuna goyon bayan Gaza.
A cikin birnin Sanaa an yi taron ne a dandalin Saba’in a yau juma’a da mahalartansa suka rika bayar da taken nuna kin amincewa da halin da mutanen Gaza suke ciki na yunuwar da aka jefa su da kuma ci gaba da yi musu kisan kiyashi.
Bugu da kari masu gangamin sun rika bayyana cewa; Taimakawa mutanen Gaza, kai wa manzon Allah cika-makin annabawa, manzon Allah ( s.a.w) dauki ne, kuma taimakon masallacin Kudus ne.
Haka nan kuma masu gangamin na birnin Sanaa sun yi tir da kutsa masallacin kudus da yahudawa ‘yan share wuri zauna su ka yi. Har ila yau, mutanen sun bayyana cewa; Fitowar da su ka yi, nau’in jihadi ne da kuma amsa umarnin Allah da yin jihadi a tafarkinsa da kuma neman yardarsa.
Baya ga birnin San’aa an kuma yi wasu gangamin a cikin birane 14 na fadin kasar ta Yemen.
Kasar Yemen dai tana ci gaba da kai wa manufofin HKI hare-hare saboda ci gaba da tafka laifukan yaki da take yi a Gaza, tare da jaddada cewa ba za su daina ba har idan an kawo karshen yakin na Gaza.
Sojojin Yemen ta bakin kakakinsu Janar Yahya Sari, sun sanar da kakaba takunkumi akan tasoshin jiragen sama da na ruwa na HKI. Daga lokaci zuwa lokaci sojojin na Yemen suna harba makamai masu linzami akan filin saukar jirgin sama na “Ben-Gorion” da kuma tashar jirgin ruwa ta “Haifa”.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Allah Ya Yi Wa Wakilin Sadarwan Bauchi, Jafaru Ilelah, Rasuwa
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin masani a harkar hulɗa da jama’a kuma ma’aikacin gwamnati na gari da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga jihar.
Ya ce aikin wayar da kai da ya yi ba za a manta da shi ba.
Gwamna Bala Muhammad, ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa, abokansa da masarautar Bauchi.
Ya bayyana Ilelah a matsayin mutum mai kishin ƙasa da jajircewa a bakin aiki.
Ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya jiƙansa kuma ya sanya shi a Aljanna Firdausi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp