Aminiya:
2025-11-04@01:15:41 GMT

’Yan sanda sun kama wanda ake zargi da kisan matar aure a Kano

Published: 27th, May 2025 GMT

’Yan sanda sun kama babban wanda ake zargi da kisan wata matar aure masi shekaru 22 a gidanta da ke unguwar  Tsamiyar Duhuwa da ke yankin Farawa a Jihar Kano.

A ranar 6 ga watan Afrilu ne aka tsinci gawar matar mai suna Rumaisa Haruna, ne a gidanta bayan an yi mata kisan gilla.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar kama wanda ake zargin mai shekaru 35 mazaunin unguwar Madatai ne a ranar 23 ga watan Mayu ta hanyar binciken sirri.

Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin a hannun ’yan sanda, inda ya bayyana cewa ya shiga gidan wadda aka kashe ne ya shake ta, sa’annan ya soka mata wuka a wuya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.

Gwamnatin Kano za ta sabunta masallacin da aka kona masallata 23 a kan N150m Amarya ta kashe uwargida da wuka a Katsina

Sanarwar ’yan sandan ta ce: “Za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.”

Lamarin mai ban tausayi ya bayyana ne lokacin da mijin matar mai suna Ibrahim Mohammed, ya tsinci gawarta da mummunan rauni a wuyanta. An garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.

Rundunar ’yan sandan ta yaba wa jami’anta masu bincike saboda kwarewarsu da kuma jajircewarsu wajen cafke wanda ake zargi, inda ta kara da cewa ana ci gaba da bincike don tabbatar da an yi cikakken adalci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Farawa matar aure Tsamiyar Duhuwa wanda ake zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.

Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.

Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen  tsaro.

CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya
  • Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 
  • Matar aure ta yanka wuyan mijinta, ta fasa masa ido da wuƙa a Neja
  • Yadda matata ta ɓace a Abuja aka tsince ta a Sakkwato
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda