Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Iran Na Rashin Tunanin Kera Makamin Nukiliya
Published: 30th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin akidar Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da haƙƙin da doka ta tanada ba ta fannin inganta sinadarin uranium, domin inganta harkar kiwon lafiya, aikin gona da masana’antu, yana mai jaddada cewa: makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin koyarwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A yayin ziyarar da ya kai masarautar Oman, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a wata hira da gidan talabijin na kasar, ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da kuma muradun yankin da na kasa da kasa na Iran da Oman, da kuma muhimman batutuwan da suke faruwa a duniya.
Ya kamata a lura da cewa: Wannan ziyara ta zo ne a cikin tsarin karfafa zumunci da fitacciyar alakar da ke tsakanin masarautar Oman da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da goyon bayan bangarori daban-daban na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma cikin tsarin muradun da shugabannin kasashen biyu ke da shi na kara karfafa da raya wannan dangantaka. An tattauna fannoni daban-daban na hadin gwiwa da suka yi daidai da muradun kasashen abokan juna da kuma biyan bukatunsu, musamman ma a fannin ci gaban yankin da kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria