Duk Da Janye Tallafin Rarar Mai, Matsin Rayuwa Na Addabar ‘Yan Nijeriya
Published: 30th, May 2025 GMT
Wani masanin tattalin arziki, Ademola Adigun, ya ce, duk da janye tallafin mai, sashin mai a Nijeriya ba ya tafiya kan ka’ida.
Ya yi bayanin cewa kawai an rage biyan tallafin ne amma ba wai an daina biya gaba daya ba, kuma babu gasa tsakanin ‘yan kasuwa wanda shi ma na haifar da nakasu.
Adigun ya soki tsarin sayar da danyen mai a kan kudin naira domin zabar da masu saye, ta yadda za a samar da lamari kamar na ‘ya’yan mowa da bora, da ke iya korar ‘yan kasuwa masu zaman kansu, lamarin da ya tilasta wa kusan gidajen mai 5,000 rufewa.
Adigun, duk da ya nuna farin ciki kan yadda masu zuba hannun jari suke nuna sha’awar zuba jari a sashin gas da yaba wa kan farfado da yanayin kasafin kudi, sai dai ya yi gargadin cewa har yanzu kasuwannin Nijeriya ba su da karfin janyo hankalin dandazon masu zuba jari.
Don haka ne ya yi kira da a samar da sauyi kan hanyoyin sufuri domin rage kudaden kayayyaki, ya ce, yawan kudin sufuri ne shi ne babban dalilin da ke janyo tashin farashin kayayyakin masarufi a kasar nan.
Shugaban PETROAN, Dakta Billy Gillis-Harry, ya ce, gwamnati ta kasa fito da abubuwan da ake sa rai ko ake tsammani da kuma cikakken tsari kan cire tallafin mai.
Ya koka kan matsalolin da har yanzu ake ci gaba da samu kan sauran matatun mai na gwamnatin tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni a a ‘Delta state’, na yi makarantar firamare da sakandare a Delta, sannan nayi aure a can. Yara na uku, Allah ya kawo rabuwa tsakani na da mijina. Babana dan ‘Nasarawa State’ ne, Mama ta kuma ‘yar Jihar Kano ce. Shekaruna Talatin da hudu, na tsinci kaina a masana’antar Kannywood ne shekara shida da suka wuce baya.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Saboda fim yana daya daga cikin abin da ya fara burge ni bayan aure na ya mutu, shi fim abu ne wanda yake kamar wa’azantarwa da kuma tunatarwa.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Yadda gwagwarmayar ya kasace shi ne; na zo fim ne ba tare da tunanin yadda za ta kasance da ni ba, amma yanzu kam Alhamdulillah.
Ya batun iyaye lokacin da za ki sanar musu kina sha’awar fara fim, shin kin samu wani kalubale daga gare su?
Eh, a gaskiya na samu. Saboda mahaifiya ta da ‘yan’uwana sun ki yarda, sai da na samu na zaunar da su na fahimtar da su sannan.
Da wane fim ki ka fara?
‘Motsin Rai’ wanda Yahaya Sa’id ne yayi daraktin, da kuma Dadin Kowa.
Ya farkon farawar ta kasance?
Gaskiya na sha wahala kasancewar shi ne farkon dasa min ‘camera’.
Da su wa ki ka fara cin karo a farkon shigarki kannywood?
Bosho, su Dan’Auta da sauransu.
Kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?
Gaskiya ba zan iya kirgawa ba.
Cikin finafinan da ki ka fito wanne ne ya zamo bakandamiyyarki?
Kishiyar uwa, saboda na fito a mahaukaciya abun dai abun armashi.
Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?
Dalilin fim na je gurare wanda ban da ta wannan hanya, ban yi tunanin zuwa ba.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta cikin masana’antar?
Eh, kam ba za a rasa ba, to, amma Alhamdulillah.
Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farinciki ko akasin haka, wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba a rayuwa?
Kamar mutuwar mahaifi na, ba zan taba iya mantawa ba har abada.
Ko kina da ubangida a masana’anyar Kannywood?
Eh, ina da shi.
Kafin shigarki masana’antar Kannywood wadanne jarumai ne suke burge ki, kuma me ya sa?
Ali nuhu, saboda yadda yake aikinsa kamar a gaske.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
In zama babbar jaruma.
Bayan fim kina wata sana’ar ne?
Eh, ina ‘business’.
Misali wani daga cikin abokan aikinki ya ce yana sonki zai aure ki, shin za ki amince ki aure shi ko kuwa ba ki da ra’ayin auren dan fim?
Idan da so da kauna me zai hana.
Wasu na kokawa game da masana’antar kannywood, a takaice ya za ki yi wa masu karatu bayanin yadda masana’antar take, shin wace ce Kannywood ya cikinta yake?
Kannywood wata masana’anta ce wacce take kamar makaranta, kafin ka fara ta, dole sai ka mayar da hankali.
Wane kira za ki yi ga masu kokarin shiga kannywood?
Duk wacce za ta shigo ta dauka kamar koyan sana’a ce ya kawo ta, dole sai ta mayar da hankali tare da jajircewa.
Ko akwai wata shawara ko wani sako da ki ke da shi ga sauran abokan aikinki?
Sako na a gare su shi ne, su dinga rike gaskiya da amana, su sani mu kamar amana muke a hannunsu, su taya mu rike ta kima da mutuncin mu.
Me za ki ce da masoyanki masu kallon finafinanki?
Ina yi wa kowa fatan alkairi.
Muna godiya
Ni ma na gode.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA