2025-10-19@11:08:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3649

«Yan Jarida»:

    A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci.   Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar...
    Haka zalika, an yi zargin cewa; bai kammala karatun digirinsa na farko ba, sannan kuma takardar shaidar yi wa kasa hidima (NYSC) da ya mika wa majalisar dokokin kasar da shugaban kasa ta bogi ce. Sai dai, ya zargi Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da daukar nauyin zarge-zargen da ake yi masa na takardar shedar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kuduri mai lamba 2231 ya ƙare aiki a yau A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen kasar Iran ya tabbatar da cewa a karshe kuduri mai lamba 2231 ya kare...
    Makami mai linzami na Iran kirar “Ghadr-H” ya aika da sako mai muni ga gwamnatin mamayar Isra’ila Wani masani kan harkokin tsaro da tsare-tsare Kanar Abdul Karim Khalaf ya bayyana cikakkun bayanai masu inganci da siffofi na musamman na makami mai linzamin na Iran “Ghadr H”, yana mai jaddada cewa; Makamin ya aike da sako...
    Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Ruguza Gaza “ba abin da za a gaskata ba ne” domin an rusa yankin gaba daya Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai, Tom Fletcher, ya ce: Girman barnar da aka yi a zirin Gaza abu ne da ba za a taba mantawa...
    Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya dawo kasarsa daga Nairobi domin kalubalantar hukuncin kisa da aka yanke masa A wani gagarumin ci gaba na siyasa, tsohon shugaban kasar Kwango Joseph Kabila, ya bayyana a bainar jama’a a Nairobi babban birnin kasar Kenya, bayan da a makonnin da suka gabata wata kotun soji a kasarsa ta...
      Bayan dawowarsa kasar Sin, Yang ya ci gaba da koyarwa a jami’ar Tsinghua, inda cikin sama da shekaru 20 ya bayar da muhimmiyar gudummawa wajen kyankyashe, da horar da sabbin masu hazaka, da yayata musayar ilimi tsakanin sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Gargadi...
    “Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar.   A cewar rundunar sojoji, an gano...
      Kakakin ya kuma jaddada matukar adawa, da tanade-tanaden dokar, yana mai cewa, batun Taiwan shi ne jan layi na farko da ba za a iya tsallakewa ba a dangantakar Sin da Amurka.   Daga nan sai ya yi kira ga Amurka, da ta mutunta cikakkiyar manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya,...
    Mataimakin firaministan kasar Sin, kana jagoran tawagar kasar mai tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya da tsagin Amurka He Lifeng, ya zanta ta kafar bidiyo da sakataren baitul-malin Amurka Scott Bessent, da wakilin cinikayyar kasar Jamieson Greer a jiya Asabar. Yayin zantawar tasu, jami’an sassan biyu sun amince da gudanar da sabon zagayen tattaunawa game...
    Majalisar Dattawa ta shiga tsakani don warware rikici tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin gargadi na makonni biyu da malaman jami’ar ke yi. A sakamakon haka, kwamitocin Majalisar Dattawa kanKwadago da kuma Ilimi mai zurfi za su gana da Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da...
      Gwamna Radda ya jaddada cewa hukumomin tsaro kadai ba za su iya fada da ‘yan ta’adda ba, sai dai da gudummuwar ‘yan kasa. Ya yi kira ga ‘yan Nijeria da su zama masu sanya ido da kai rahotanni cikin gaggawa da bayar da ingantattun bayanai ga jami’an tsaro.   Ya yaba wa gwamnatin Shugaban...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn October 17, 2025 Manyan Labarai Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17,...
    An gudanar da bikin bayar da lambar yabo ta wasan kwallon kafa na Asiya da Futsal na shekarar 2025 a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. A bangaren mata kuwa, Marzieh Jafari, shugabar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Iran, ita ce babbar mai horar da mata, yayin da Salar Aghapour ta lashe kyautar ‘yar...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe. Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta...
    Tawagar sun gabatar da kansu ga babban sakataren hukumar gudanarwar ci gaban Jihar Katsina, Dakta Mustapha Shehu. Tawagar sun ce ziyarar wani bangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikace-aikace domin inganta zaman lafiya da kuma sanar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira.   Gwamnan Katsina ya yaba wa Bankin Duniya da ya yi...
    Shugaban ya kara da cewa, aana sa ran aikin za a fara gudanar da shi ne, a zangon farko na shekarar 2026.   Ya ci gaba da cewa, aikin na yiwa wadannan Tashoshin garanbawul, na daga cikin kudurorin Gwamnatin Tarayya na zamantar da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa, musamman ta hanyar samar da kayan aiki...
      Shin menene makasudin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin ilimi da aka gudanar a yau? Makasudin wannan taro shi ne a fadakar da mutane ayyukan wannan hukuma ta TETFUND da take yi, sannan kuma a yi magana da wadanda suka fi amfana da shi wannan tsari na TETFUND. Kamar...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tarwatsa wasu muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya a lokacin yakin 12 Kwamandan Dakarun sa-kai na Basij Birgediya Janar Gholamridha Sulaimani ya bayyana cewa: Tunanin kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yakin kwanaki 12 da aka yi, wauta ce ta makiya yahudawan sahayoniyya, wadanda suka gaza...
    Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, inda ta gudanar da samame a wata maɓoya da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da safarar ƙwayoyi a cikin jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ta bayyana...
    Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta sanar da nadin CP Dantawaye Miller a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja. Ya karɓi ragamar aikin ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Oktoba, 2025, daga hannun CP Ajao Adewale, wanda Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun, ya sauya wa wajen aiki. Wani mutum...
    Dantsoho ya sanar da haka ne, bayan kaddamar dashi a matsayin Mataimakin Shugaban Kungiyar a kwanan baya a wani taro kan harkokin Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya da aka gudanar.   Kazalika, Dantsoho ya ci gaba da cewa, zai mayar da hankali ne, kan wanzar da tsarin da NPA, ta sanya a gaba da kara...
    Abin da ya rage yanzu shi ne za a zuba ido don ganin irin sauyin da zai kawo na tsaro a birnin tarayyar, sakamakon taɓarɓarewar tsaro da ya addinin garin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 Manyan Labarai Shugaban Ƙasa...
    Majalisar koli ta sisaya ta kasar yamen ta sanar da nada major janaral Yousef hassan al-Madani a matsayin sabon babban hafsan hafsoshin sojin na kasar Yamen , inda ya gaji Janaral Mohammad Abdulkarim Al-Ghumari wanda yayi shahada a baya bayan nan sakamakon Harin da sojojin HKI suka kaddamar kan kasar ta yamen. Wannan sabon nadi...
    Baya ga yi masu afuwa, Shuagaba Tinubu, ya kuma karama su da lambar yabo ta kasa. ‘Yan Ogonin su tara, sun dai fuskanci shari’a ne, bisa zarginsu da kitsa kisan sarakunan Ogoni Albert Badey, Edward Kobani, Theophilus Orage da kuma Samuel Orage. Kotu ta tuhumi ‘yan Ogonin su tara, ta kuma yanke masu hukuncin rataya...
    Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, taron goron gayyata ne na kafa Nijeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi tare da sabuntawa a Afirka, sannan kuma sauyin da aka samu na makamashi Nijeriya, ya bayar da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410, daga tsakanin yanzu zuwa shekarar 2060. Ya kara da cewa,...
      Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin.   Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin...
    A baya- bayan nan ‘yan ta’addan wadanda suka daura damarar hanawa al’umma kwanciyar hankali sun kashe daruruwan mutane, kona gidaje tare da garkuwa da mutane ciki har da mata da kananan yara. Rahotanni daga yankunan sun tabbatar da yadda al’umma suka gaji suka kosa da jin alkawura marasa adadi daga gwamnati wadda ke kasa cikawa...
    Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Israel Sunny-Goli, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ya guji duk wata matsin lambar da wasu ƴan siyasa ke yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Sunny-Goli ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin halartar shirin Politics Today na tashar Channels,...
     Shugaban kasar ta Sudan Janar Abdulfattah al-Burhan  ya ziyarci Masar inda ya gana da takwaransa Janar  al-Sisi, inda su ka tattauna halin da ake ciki a Sudan, da kuma matsalolin da yankin yake fuskanta. Haka nan kuma bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi akan madatsar ruwan kasar Habasha da Masar take da sabani da Addis...
    A jiya Alhamis jiragen yakin HKI sun kai hare-hare na wuce gona da iri garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahada da kuma jikkatar mutane da dama. Majiyar tsaro daga kudancin Lebanon ta ambaci cewa, mutum daya ya yi shahada yayin da wasu 7 su ka jikkata. Hare-haren sun shafi garin...
    Jaridar Wall Street Jouranl ta kasar Amurka ta buga labarin da yake cewa, kasar Amurka ta fada girke makamai a kusa da tekun Caribbean da kuma wasu jiragen sama a arewacin kasar Venezuela. Labarin ya kara da cewa;Rundunar da ma’aikatar yakin Amurka ta “Pentagon” ta girke ta zaratan mayakan kundunbala ce wacce ta kashe Usama...
    A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da...
    Aƙalla jami’an tsaro takwas, ciki har da ɗan sanda guda ɗaya da masu tsaron al’umma bakwai, sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da aka kai musu a hanyar Gusau–Funtua da ke Jihar Zamfara a ranar Alhamis. Lamarin ya faru ne a lokacin da gamayyar jami’an tsaro, waɗanda suka haɗa da ’yan sanda da...
      Ya ce kamar ko da yaushe, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan muhimmiyar rawar da FAO ke takawa a bangaren aikin gona da samar da abinci a duniya.   An kafa hukumar FAO ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 1945, kuma Sin na daya daga cikin kasashe mambobi...
      An dage ci gaba da binciken har sai ranar 20 ga wata. Maris na shekara mai zuwa, a makon da ya gabata, dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Manchester domin gudanar da jana’izar Hatton, wanda ya kasance shahararren dan wasan dambe a kasar Ingila.   Dan wasan gaban Oasis...
    Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana. Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasika daga daukacin malamai da daliban jami’ar nazarin aikin gona ta kasar Sin, inda ya taya dukkan malamai da dalibai da ma’aikatan jami’ar, da kuma wadanda suka kammala karatu a jami’ar murnar cika shekaru 120 da kafuwar jami’ar. Xi ya yi fatan jami’ar za ta ci gaba da...
    Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa a koda yaushe makiya suna neman haifar da rikici tsakanin kasashen musulmi domin raunana su, yana mai nuni da barkewar tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan. Mr. Pezeshkian ya bayyana haka ne a yayin wani taro inda ya fayyace matsayin kasar Iran dangane da takun saka...
      “Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana ƙarshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.”   Lamarin ya jawo damuwa daga al’umma da shugabannin siyasa, yayin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙoƙari wajen gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi da tabbatar da zaman lafiya a...
      Haka kuma, shugabar kasar Iceland Halla Tomasdottir ta ce, a matsayin wata babbar kasa, kiran da kasar Sin ta yi yana da muhimmanci ga sauran kasashen duniya. Ayyukan da kasar Sin ta yi a fannin tabbatar da ci gaban mata da daidaiton jinsi, sun kasance abin koyi ga kasashen duniya.   Bugu da kari,...
      Hichilema ya kuma jinjinawa kamfanonin Sin, bisa yadda suke inganta darajar albarkatun dake kasarsa ta hanyoyin zuba jari, kana ya godewa Sin bisa yadda ta bude kasuwanninta ga Zambia da ma sauran sassan nahiyar Afirka baki daya. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya...
    An fara tantancewar da misalin ƙarfe 12:55 na rana, inda ake sa ran Farfesa Amupitan zai gabatar da tarihinsa da kuma amsa tambayoyin da ‘yan majalisar za su yi masa, kafin yanke shawara kan tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban INEC. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP October 15, 2025 Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama gungun mutane 11 da ake zargi da kasancewa ’yan fashi da makami da ke addabar matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Kano. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen tare...
    Ma’aikatar masana’antu da ma’adinai ta kasar Iran ta bayyana cewa na sami karin ci gaba a yawan karfen da kasar ke sayarwa ga kasashen waje a rabin farko na wannan shekara ta 2025 zuwa dalar Amurka billion $4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arzikin da...
    Majiyar hukumar fursinoni ta Falasdinawa ta bada sanarwan cewa masu gida a gidajen yarin HKI sun daki Marwan Barghouti a cikin makon da ya gabata har ya suma, kuma sun karya masa awaza har guda 4 sanadiyyar haka. Jaridar ‘The National’ ta kasar Amurka bayyana cewa Barghouti yana daga cikin shuwagabannin Falasdinawan da Hamas ta...
    Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa. Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu...
    Ministan Harkokin Cikin Gida Ya Yi Watsi Da Shelanta Samun Nasara Da Dantakara Isa Bakari Ya Yi Ministan harkokin cikin gidan kasar Kamaru Paul Atanga Nji ya yi watsi da yadda dan takarar shugabancin kasar Isa Tchiroma Bakari ya shelanta kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, ya kuma yi kira ga shugaban...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci mai tawali’u, mai aminci, kuma mai kishin kasa wanda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa abin a yaba ne.   Shugaban ya yaba wa Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma...