Rikici ya barke a taron Atiku da kungiyoyin Arewa
Published: 26th, May 2025 GMT
Daliget sun tayar da jijiyoyin a wurin taron haɗakar siyasar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi domin fafatawa da shuagaban kasa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Ana tsaka da taron Kungiyar Tuntubar Siyasa ta Kasa Reshen Arewa a Abuja ne hayaniya ta kaure bayan tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ya sanar da wanda suna daliget da zai wakilci Jihar Jigawa.
Rashin gamsuwar sauran daliget din jihar dadi ba suka tayar da jijiyoyin wuya, inda suka hau kan mumbari suka dauke wanada aka ayyanan suka hana shi magana da yawunsu.
Daba bisani an yi nasarar shawo kan rikicin, inda aka zabi dan tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido, Mustapha Lamido, da wani daliget kuma suka gabatar da jawabi a madadin wakilan jihar.
Ana zargin wani mutum da kashe ɗan maƙwabtansa a Sakkwato Ko gwamnoni duka za su koma APC ba zai hana mu kayar da Tinubu a 2027 ba — Babachir An kashe matashi yayin rikici a ƙauyukan KanoAtiku wanda ya dade yana neman takarar shugaban kasa a Najeriya yana kokarin jagorantar jam’iyyun adawa domin kayar da Tinubu a zaben na 2027, yana daga cikin fitattun ‘yan siyasar da suka shiga hadakar APC a gabanin zaben 2015.
Hadakar tasu ta kai ga dan takarar APC Muhammadu Buhari, ya yi nasarar kayar da shugaban kasa Goodluck Jonathan a lokacin. Daga bisani ya fice daga APC zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP, inda yake hankoron cika burinsa na zama shugaban kasa.
Daga cikin wadanda ke cikin hadakar tasu Atiku har da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a zamanin Buhari,, Babachir David Lawal.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa
Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashuwa (FUGA) a jihar Yobe za ta gwangwaje Uwargidan Shugaban Sasa, Sanata Remi Tinubu, da gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, da wasu fitattun ’yan Najeriya shida da digirin girmamawa.
A cewar jami’ar, za a ba su shaidar ce saboda gudunmawar da suka bayar a bangarori da daman a ci gaban kasa.
Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri ce ta bayyana hakan a lokacin da take ganawa da manema labarai a jami’ar.
Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a Zirin Gaza Ba Tinubu kaɗai ne ya sa Buhari ya ci zaɓe a 2015 ba – Boss MustaphaTa ce za a karrama su ne a yayin bikin yaye dalibai karo na farko na jami’ar da zai gudana ranar Asabar mai zuwa.
Farfesa Maimuna ta ce za a karrama Sanata Remi ne da digirin digirgir ne na (D.Litt), yayin da Gwamna Buni da Ministan harkokin ’Yan Sanda kuma tsohon gwamnan Yobe, Sanata Ibrahim Geidam, dukkansu za su samu digirin digirgir ne a kan kwarewa kan harkokin mulki (DPA).
Ta kuma ce za a karrama tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan da digirin digirgir bangaren kimiyya na D.Sc.
Haka kuma a cikin wadanda za a karrama akwai Mai shari’a Sidi Bage Muhammad da kuma Alhaji Bukar Goni Aji.
Farfesa Waziri ta ce jami’ar ta yaye dalibai kusan sau shida wadanda adadinsu ya kai 3,449 a tsangayoyin jami’ar guda hudu tun bayan da aka kafa ta.