Sojojin Yemen Sun Hana Jigilar Jiragen Sama A Isra’ila Tare Da Firgita ‘Yan Sahayoniyya
Published: 30th, May 2025 GMT
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami lamarin da ya tarwatsa cinkoson jama’a a filin jirgin
Sojojin Yemen sun sanar da kai farmakin soji kan filin tashi da saukan jiragen saman Ben Gurion tare da yin barazanar ci gaba da toshe hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa na haramtacciyar kasar Isra’ila muddin bata kawo karshen killace Zirin Gaza da ta yi ba.
Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa: Wannan farmakin ya samu nasarar cimma burin da aka sanya a gaba, wanda ya tilastawa miliyoyin ‘yan sahayoniyya ‘yan mamaya tserewa zuwa maboyar karkashin rami tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin.
Sari’e ya kara da cewa: Wannan farmakin yana tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan sojojin Yemen na wajibin addini, kyakkyawar dabi’a da jin kai da kuma dan Adamtaka ga ‘yan uwansu na Falastinu har sai an daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Falasdinawa da killace su.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba October 30, 2025
Daga Birnin Sin Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21 October 30, 2025
Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025