2025-08-04@06:14:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1199
«Goyon Baya»:
Kocin Tottenham Frank, wanda ya koma Spurs daga Brentford a watan Yuni, ya yi godiya ga kyaftin din na Koriya ta Kudu, “shi gwarzo ne na gaskiya ga Spurs a kowane fanni, daya daga cikin manyan yan wasan da suka taba taka leda a gasar Premier inji kocin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Rundunar Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar DSS sun ceto Injiniya Joshua Saleh, wani malami a Jami’ar Taraba, wanda ’yan bindiga suka sace. An sace malamin ne a ranar 31 ga watan Yuli, 2025, a hanyar Chinkai–Kente zuwa Wukari, da ke Ƙaramar Hukumar Wukari a Jihar Taraba. Sai an samar da ’yantacciyar ƙasar...
Kungiyar Hamas wacce takr iko da Gaza kuma take gwagwarmaya da HKI tun shekara ta 2023 a baya-bayan nan, ta bayyana cewa ba za ta ajiye makamanta ba sai an kafa kasar falasdinu mai zaman kanta, wanda yin watsi ne da bukatar HKI na shafe kungiyar daga doron kasa. Shafin labarai na Internet Arab News...
Ƙungiyar Hamas ta sake jadadda matakinta na cewa ba za ta taɓa ajiye makami ba, har sai lokacin da duniya ta amince da samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu a yankin Gabas ta Tsakiya, wani abu da zai sake mayar da yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙoƙarin ƙullawa baya. A halin da ake ciki yanzu haka...
Rundunar sojin Jamus ta fara gudanar da aikin jefa kayayyakin gaji da suka hada da abinci da magunguna ta sama a Zirin Gaza. Ma’aikatar Tsaron Jamus da ke Berlin, fadar gwamnatin kasar, ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce jiragen rundunar sojin sama sun ajiye kunshin tallafi 34 dauki da tan 14 na...
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta ce Gwamnatin Tarayya ta yi sakaci game da ɓacewar ɗan gwagwarmaya Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata. A wata sanarwa da ta fitar, Amnesty, ta ce abin takaici ne ganin cewa shekara shida kenan da Dadiyata ya ɓace ba tare da wani sahihin bayani...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Fim Na Kisan Kiyashin Nanjing Ya Mamaye Kasuwar Fina-Finan Sin Bisa Samun Kudin Shiga Yuan Biliyan Daya
Wani fim mai suna “Dead to Rights”, wanda aka shirya game da kisan kiyashin da aka yi a birnin Nanjing, ya mamaye kasuwar fina-finai ta lokacin zafi ta kasar Sin, inda kudin shigar da aka samu da shi ya zarce yuan biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 140 cikin kwanaki takwas kacal. Wanda aka yi...
Bayan mutane da dama sun nuna ɓacin ransu kan al’amarin, gwamna Abba Yusuf ya kafa kwamiti domin bincikar lamarin, tare da umarnin a miƙa masa rahoton cikin mako guda. Gwamnan, ya taɓa goyon bayan jami’an tsaro wajen kama Danwawu, kuma ya umarci NDLEA ka da su sake shi. Wani jami’i ya ce: “Gwamna Abba Kabir...
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu. Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua...
A cewar NANNM, sun dakatar da yajin aikin ne domin ci gaba da tattaunawa bisa alƙawarin da gwamnati ta ɗauka na aiwatar da buƙatun cikin ƙanƙanin lokaci. Takardar ta ce, “Kwamitin zartarwa na ƙasa ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka, musamman yadda ta bayyana lokacin da za ta aiwatar da buƙatunmu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da Haniya yake cika shekara guda da shahada,...
An yi jana’izar Marigayi Sarkin Gudi da ke Jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, ranar Juma’a a Abuja, inda ya rasu a wani asibiti bayan fama da jinya. Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron. Sanarwar da Mamman Mohammad daraktan yada labarai na gwamna...
Iyalai ‘yan Sudan da dama ne suka taru a babbar tashar jirgin kasa ta birnin Alkahira, dauke da jakunkuna da kayayyaki a lokacin da suke shirin komawa gida bayan da suka tsere daga rikicin Sudan. Suna cikin dubban ‘yan kasar Sudan da suka rasa matsugunansu da ke kan hanyarsu ta komawa daga Masar zuwa yankunan...
A yanzu haka dai ratotannin sun tabbatar da cewa APC da ADC suna gogayya wajen neman samun goyon bayan mutanen arewa kafin babban zaɓen 2027 ya ƙariso. A ranar 1 ga Yuli, manyan ƴan adawa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023,...
Kungiyar Ma’aikatan jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta mayar wa da gwamnati martanin cewa har yanzu tana ci gaba da gudanar da yajin aikin da take yi. Ministan Lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ne dai ya bayyana cewa ƙungiyar ta janye yajin aikin gargaɗin. An ceto mutum uku da aka yi garkuwa...
Tarihin dan’adam ya nuna yadda ƙabilu daban-daban, ke nuna ƙin amincewa da auratayya ta haɗin gambiza a tsakanin ƴaƴansu da wasu ƴan ƙabilar da ba tasu ba. Hatta a cikin ƙabila daya ana samun wannan nuna wariya, tsakanin dangi, ko masu hali da talakawa. Hatta a tsakanin addini daya, bambancin aƙida ko fahimta na sa...
A Alhamis din nan ne dai kasar ta Habasha ta fito da Shirin shuka bishiyoyi har miliyan 700 a rana daya, ta hanar shigar da miliyoyin mutanen kasar. Fira ministan kasar ta Habasha Abi Ahmad yana son a rika tunawa da shi anan gaba ta hanyar shuka bishiyoyin da za su kai biliyan 50, daga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis. A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin...
Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato. A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman...
Firaminista Mark Carney ya ce Canada ta shirya amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu a cikin watan Satumba, inda ta zamo ƙasa ta uku daga cikin ƙungiyar G7 da ta fitar da irin wannan sanarwa a cikin kwanakin nan. Carney ya ce za su ɗauki matakin ne ta la’akari da wasu sharuɗɗan gyara daga ɓangaren hukumomin...
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi. Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji...
Ministan ya kuma ce ƙasarsa na shirin sanya hannu a wata takarda don neman goyon bayan sauran ƙasashe wajen ganin an kafa ƙasar Falasɗinu da Isra’ila. A taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar na kwana biyu, ƙasashe 125 sun amince cewa hanyar warware rikicin Gaza ita ce kafa ƙasashe biyu, wato Falasɗinu da Isra’ila....
Da alama tallafin da matar Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta ba wadanda hare-haren jihar Binuwai ya raba da muhallansu na Naira biliyan daya ya bar baya da kura. Kwana daya da bayar da tallafin, ’yan gudun hijirar sun fito suna zanga-zangar yunwa, amma kakakin hukumar bayar da agaji ta jihar (SEMA), Terna Ager, ya...
Dakarun Operation Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, sun ɗakile wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Jihar Borno. Sun kai harin ne yankunan Konduga, Bama da Gwoza. Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000 ’Yan ta’addan sun...
Kwamitin Majalisar Dattawa na bin Diddigi ya ba Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) wa’adin mako uku ya amsa tambayoyi kan rashin ba da ba’asi kan Naira tiriliyan 210 da ba a san inda suka shiga ba daga shekarar 2017 zuwa 2023. An dai bayar da wa’adin ne ga shugaban kamfanin na kasa, Bayo Ojulari, wanda...
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya shimfiɗa wa Isra’ila wasu jerin sharuɗan da ya ce idan ba ta cika ba, Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasdinu. A ranar Talata ne Mista Starmer ya ce idan har Isra’ila ba ta cika waɗannan sharuɗa ba zuwa watan Satumba Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu. Sharuɗɗan da...
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta taya sabon mai martaba Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, murnar hawansa karagar mulki a matsayin Sarkin Katsinan Gusau na 16. Jam’iyyar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta, Yusuf Idris Gusau, ta bayyana sabon sarkin a matsayin mai tarihi da kuma...
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci...
Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Babbar hukumar kwastam ta Sin ta fitar da sanarwar a yau Talata cewa, shirin amincewa da juna na tsarin “Masu gudanar da kamfanoni da aka ba su izni” wato AEO a takaice tsakanin Sin da Benin da Thailand zai fara aiki a hukumance daga ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2025. Bayan aiwatar da wannan...
Gwamnatin kasar Lebanon ta bada labarin cewa mutum guda ya yi shahada a yayinda, wasu mutum 4 suka ji rauni sanadiyyar hare-haren da HKI suka kai a kan gidajensu a lardin Nabatia a kudancin kasar Lebanon a safiyar a ranar Litinin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar kiwon lafiya na...
Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu. Daga bisani ’yan sanda sun...

Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau...
A cikin kwanakin bayan nan ana samun karuwar sojojin HKI da suke kashe kawunansu saboda tabuwar kwakwalensu sanadiyyar yakin Gaza. Kafafen watsa labarun HKI sun kunshi rahotanni da suke bayani akan yadda sojojin mamayar da su ka yi yaki a Gaza, suke samun tabuwar hankali, da hakan yake sa su kashe kawukansu bayan sun baro...
Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya. Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji. Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar...
Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa...
An fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa. Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da...
Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a...
Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569. Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad...
Kasar Sin ta fitar da manyan manhajojin AI har 1,509, matakin da ya sanya ta kaiwa matsayi na daya cikin jerin sassan duniya da suka fitar da jimillar irin wadannan manhajoji 3,755. Masana na ganin bunkasar sashen masana’antun fasahohin AI na kasar Sin zai ingiza sabbin nasarori a fannin. A jiya Lahadi, yayin taron karawa...
A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara...
Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran. Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin...
Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran. Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin...
An gano gwawar mutum 15 a yayin da ake ci gaba neman wasu uku bayan hastarin kwalekwale da ya auku a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja. Kwalekwalen ya kife ne a yayin da yake ɗauke da mutum 43 da buhuna 60 na shansherar shinkafa da shanu uku da tumaki biyu a ranar...
An gano gwawar mutum 15 a yayin da ake ci gaba neman wasu uku bayan hastarin kwalekwale da ya auku a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja. Kwalekwalen ya kife ne a yayin da yake ɗauke da mutum 43 da buhuna 60 na shansherar shinkafa da shanu uku da tumaki biyu a ranar...
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa nasarar ayyukan tsaro a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...