Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na MDD ta bukaci kasashen duniya su takurawa HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da take yi a gaza bayan hare-haren da ta kai a kan wata makaranta a unguwar Fahmi Aljarjawi a cikin birnin Gaza wanda ya kashe falasdinawa akalla 36.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Francesca Albanese tana fadar haka a shafinta na X a jiya Litinin.

 Ta kuma kara da cewa  an kashe mutane da yawa, kuma an kashe yara da yawa. An kona su da ransu, a cikin makarantar inda suke mafaka a ciki.

Albanese ta hada da hotunan bidio wanda suke nuna irin yadda wuta take kona Falasdinawa a cikin makarantar, ta turasu a shafin nata.  Ta kara da cewa dole ne mu tsaida wuta a gaza kuma falasdinawa su gafarta mana kan cewa mun kasa yin haka har abin ya kai wannan matsayin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista

Ministan Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce Gwamnatin Tarayya na shirye-shiryen sake kara kudin wutar lantarki domin rage yawan bashin da bangaren lantarkin ke bi.

Bayanai dai sun nuna yanzu haka, bashin lantarkin da ake bi a Najeriya ya haura Naira tiriliyan hudu.

Amma a cewar ministan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki 300 a Abuja, yunkurin wani bangare ne na tabbatar da cewa bangaren lantarki ya tsaya da kafarsa.

Matar tsohon Gwamnan Adamawa ta sauya sheka daga PDP zuwa ADC Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda

Idan dai za a iya tunawa, duk da Karin kudin wutar da aka yi wa kwastomomin da ke tsarin Band A, mutane na ci gaba da korafin cewa ba sa samun isasshiyar wutar da ta kai ta kimar abin da suke biya.

Sai dai ministan ya ce yin karin na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya da kuma ci gaban kasa.

A cewarsa, “A yanzu haka, akwai tarin bashin da lamfanonin da ke samar da wutar ke bin bashi sakamakon cire tallafin lantarkin da gwamnatin ta yi, wanda yah aura Naira tiriliyan hudu a karshen watan Disambar bara.

“Tuni gwamnatin ta fara tsare-tsaren ganin cewa wannan bashin bai ci gaba da taruwa ba, shi ya sa ma take kokarin kara farashin wutar, sannan ta kirkiro da sabon tallafi ga masu karamin karfi a cikin masu amfani da wutar.

“Abin da hakan ke nufi shi ne gwamnati za ta kawo karshen tallafin da take biya, wanda hakan ke nufin za a sami karuwar farashin a dukkan matakai,” in ji Ministan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci A Kawo Karshen Matsalar Sayen Kuri’a
  • An Kashe Jami’in Sojan HKI A Gaza
  •  HKI Tana Cigaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi
  •  Masu Kare Hakkin Dan’adam Suna Allawadai Da Takunkumin Amurka  Akann Jami’ar MDD A Falasdinu
  • Gwamna Namadi Ya Bukaci Hadin Gwiwar Hukumar Kwastam Don Farfado Da Yankin Kasuwanci Na Maigatari
  • UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
  • Abdullahi Ojlan Ya Sanar Da Kawo Karshen Fada Da Makami
  • HKI: Sojoji 62 Ne Su Ka Halaka A Gaza A Cikin Wannan Shekara Ta 2025
  • Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista
  • HKI Ta Kashe Falasdianwa 6 A Gaza, Kuma Tsoffin Fursinoni