Ɗalibai sun maƙale lokacin da gini ya rufta suna jarrabawa
Published: 29th, May 2025 GMT
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba.
Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba.
Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a NejaAjujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska.
Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su.
Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa, ajujuwan sun ruguje karo na biyu da ɗalibai, lokacin da rukunin farko ya gama jarabawa ya bar harabar makarantar.
Ya ce, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin Laraba.
DanAzumi, ya bayyana cewa, an kai ɗalibai da malaman da suka jikkata zuwa cibiyar kiwon lafiya a matakin farko da ke kusa da makarantar inda yanzu haka suke samun kulawa.
Ya ce, baya ga makarantar, guguwar ta lalata gidaje da dama a cikin unguwar .
DanAzumi ya bayyana cewa, an kai ɗaliban da Malamai da kuma masu yi wa ƙasa hidima da suka jikkata zuwa cibiyar kiwon lafiya a matakin farko da ke kusa daga makarantar inda yanzu haka suke samun kulawa.
Ya ce baya ga makarantar da guguwar ta lalata gidaje da dama a garin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Taraba a makarantar
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar.
Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata.
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu.
Domin sauke shirin, latsa nan