Tare Da Taimakon Kasar China Za A Bude Masana’antun Sarrafa Sanadarin Lithium A Nigerria
Published: 27th, May 2025 GMT
Kasar Najeriya ta sanar da Shirin fara aiki a wasu sabbin masana’antu domin sarrafa sanadarin Lithium
Ministan ma’adanai na kasar ta Najeriya Daili Alaki ne ya sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a wannan shekarar da ake ciki ta 2025, da hakan zai samar da gagarumin sauyi a fagen kayan da kasar za ta rika fitarwa zuwa kasashen waje.
Kamfanin dillancin “Reuters” ya ambato ministan ma’adanai na kasar yana ci gaba da cewa; ‘yan kasar China ne za su zuba hannun jari mafi grima a cikin wannan Shirin da hakan zai samar da ayyukan yi a cikin kasar da kuma bunkasar harkokin kere-kere.
Haka nan kuma Alaki ya yi ishara da cewa; Msana’antar sarrafa Lithium din da za a kafa akan iyakar jihohin Kaduna da Niger, za ta ci kudin da sun kai dalar Amurka miliyan 600, yayin da za a kafa wata matatar sanadarin na Lithium a bayan birnin Abuja da kudin da sun kai dala miliyan 200.
Wata masana’antar ta sarrafa sanadarin Lithium da za kafa a tsakiyar wannan shekarar, za ta kasance ne a Jahar Nasarawa wacce ke iyaka da birnin Abuja.
Majiyar ta kuma ambaci cewa kamfanin kasar China na ” Geoling’ da kuma “Kankakas Tecnalogy” ne su ka samar da kaso 80% na jarin tafiyar da kamfanonin,yayin da za a samar da sauran kaso 20% daga cikin gida.
Tun a 2022 ne aka gudanar da wani bincike na karkashin kasa wanda ya tabbatar da cewa da akwai sanadarin “Lithium” a jahohi 6 na kasar, kuma yana da kyau sosai da kuma yawa,lamarin da ya ja hankalin kasashen duniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.
Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.
Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya ce an tsara wannan asusu ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.
Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.
Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a wuraren.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.