2025-05-24@13:28:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1259

«wannan shekara»:

    Gwamnatin kasar Saudiya ta bukaci a amince da samuwar kasar Falasdinu mai zamanta ne kawai hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudiya ya nakalto majiyar Saudia na fadar haka a MDD a jiya Jumma’a. Ta kuma kara da cewa Falasdinawa ba zasu taba amincewa a koresu daga kasarsu ba kamar yadda wasu yahudawa da magoya bayansu suke so. Labarin ya kara da cewa wannan bukatar na zuwa ne a dai-dai kasashen ta    Saudia da Faransa suke kokarin gudanar da gagarumin Taro a cikin watan Yuni mai zuwa don bunkasa wannan ra’ayin ta kafa kasashe biyu. Wannan ra’ayin yana kara samun goyon baya a wannan makon musamman bayan da HKI ta kara yawan...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, hadin gwiwa a bangaren ilimi tsakanin Sin da Amurka na moriyar juna ne, kuma Sin ta kasance mai adawa da siyasantar da hadin gwiwar bangaren ilimi. Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Juma’a, lokacin da aka nemi jin ta-bakinta kan matakin gwmnatin Trump na hana jami’ar Harvard daukar dalibai daga kasashen waje. A cewar Mao Ning, ire iren wadannan matakai da Amurka ke dauka za su lalata kima da darajar kasar, tana cewa, Sin za ta nace wajen kare hakkoki da muradun dalibai da malaman kasar dake kasashen waje. Ta kuma jaddada adawar Sin ga bata sunanta da takalarta ba gaira ba dalili, tana mai...
    An gudanar da taron kolin bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari na duniya na shekara ta 2025 jiya Alhamis 22 ga watan nan a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A gun taron, mai taken “rungumar zamanin digital, da samar da ci gaba cikin hadin-gwiwa”, an yi musanyar ra’ayi mai zurfi, tare da cimma matsaya daya kan batutuwa da dama, da bullo da shawarar Beijing ta taron kolin bunkasa kasuwanci da zuba jari na duniya na shekara ta 2025, inda aka yi kira da a fadada hadin-gwiwa a zamanin da muke ciki, da nufin samar da ci gaba da wadata tare. Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai Dan Asalin Jihar Kano...
    PDP na fama da rikicin cikin gida mafi muni a tarihin jam’iyyar. Tun lokacin da jam’iyyar ta rasa shugabanci a 2015, ta ci gaba da fuskantar matsaloli wajen magance rikicin da take fama da shi. Ko wani zabe yana zuwa da nashi kalubalan, yana bayyana cin amana na cikin jam’iyya. Zaben 2023, jam’iyyar ta bai wa Atiku Abubakar takarar shugaban kasa, wanda shi dan Arewa ne, inda lamarin ya haifar da fushi na masu ruwa da tsaki daga kudancin kasar nan, musamman daga wajen ministan Abuja na yanzu, Nyesom Wike. Haka ma a daidai lokacin da ake kara fuskantar zaben 2027, wannan yanayi na sake kara bayyana adaidai lokacin da Atiku ke kokarin samun tikitin jam’iyyar. A lokaci guda, Wike...
    A yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da shugaban gwamnatin kasar Jamus Friedrich Merz, bisa gayyatarsa da aka yi. Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin da Jamus suna raya dangantakar dake tsakaninsu bisa girmama juna, da amincewa da bambance-bambance, da hadin gwiwa don samun moriyar juna, kuma akwai bukatar bangarorin biyu su yi kokari tare don tabbatar da raya dangantakarsu yadda ya kamata. Ya ce, da farko dai, ya kamata a yi imani da juna a fannin siyasa tsakanin kasashen biyu. Na biyu kuma, ya kamata a kara inganta dangantakarsu, wato ci gaba da hadin gwiwa a fannonin da suka riga sun hada hannu kamar su kera motoci, da injuna, da kuma masana’antar sinadarai...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ana gudanar da zagaye na biyar na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin tawagar Amurka da na Iran a cikin yanayi na kwarewa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana a yau Juma’a cewa: Tattaunawar tana gudana cikin kwarewa da kwanciyar hankali, yana mai cewa abin da ake yadawa a kafafen yada labarai hasashe ne da baya da tushe ko inganci kuma baya da bambanci da shaci fadi. A yau Juma’a da yamma ne aka fara shawarwarin da ba na kai tsaye ba karo na biyar...
    Don haka, ya zama dole kasashen Global South su hada kansu su dauki matakan dakushe duk wani radadi da matakin harajin da Amurka ta dauka zai haifar, ciki har da bunkasawa da inganta cinikayya tsakanin wadannan kasashe,ta hanyar hada kansu domin rage dogaro da tattalin arzikin Amurka ko na kasashen yammaci, wannan yunkuri zai bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin Global South. Kasashen na Global South suna sake zayyana tsarin tattalin arzikinsu ta hanyar bayar da fifiko ga bunkasuwar tattalin arzikinsu da bayar da dama ta bai daya ga kowace kasa wajen taka rawa a harkar kasuwanci. Domin kuwa kasashen sun hade kansu wajen nuna turjiya ga wannan tsarin haraji na Amurka.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a S.M. Shuaibu ta ƙi amincewa da buƙatar wasu mambobin Kwamitin Musabaƙar Alƙur’ani da ke son a hana EFCC bincike kan yadda aka sayar da wani fili mai darajar Naira biliyan 3.5. Filin da ake magana a kai yana bayan titin Ahmadu Bello Way, kuma yana da faɗin hekta biyu. Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 16 a Borno An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya Tsohon Gwamnan Sojan Kano, Kanal Abdullahi Wase ne, ya bayar da filin don a gina katafaren waje da za a riƙa gudanar da musabaƙar Alƙur’ani duk shekara. Amma daga baya sai wasu mambobin kwamitin suka ga an gina gidaje 38 a filin ba...
    Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
    “’Yan kwanakin da suka gabata, na yi wata ganawa da Babban Hafsan Sojin Kasa, inda ya bay-yana min cewa; yana neman akalla jirage marasa matuka kimanin 32, domin kawo karshen wannan ta’addanci, wanda kuma abin da ya fada din gaskiya ne. “Kowane jirgi maras matuki, na kai wa kimanin dala miliyan 5.5, don haka, me yasa ba za mu iya hada karfi da karfe wuri guda mu sayi jiragen ba, don bai wa harkar tsaro fifiko? Har wa yau, ya bayyana kwarin gwiwar cewa; tare da bin tsarin da ya dace da hadin kai a tsa-kanin dukkanin bangarorin gwamnati, za a iya magance wadannan tashin hankula cikin gagga-wa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa da Amurka da HKI sun san cewa zasu sami nasara a kan kasar Iran da yaki da tuni  sun fadawa kasar sun kuma mamayeta. Amma saboda wannan tsoron ne suka zabi tattaunawa da ita a kan shirinta na makamshin nukliya. Sannan Shirin makamacin nikliya ma daya ne kacal daga matsalolin da ke tsakanin Iran da HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka.  Ya ce akwai matsaloli da dama, tana jirin ta kamala da gudu don ta bullo da wata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya da yamma ya kuma  kara da cewa, manufar Iran ta shiga tattaunawa da Amurka ita ce,...
    Jam’iyyar ‘All Progressives Congress” (APC) mai Mulki a tarayyar Najeriya ta tabbatar da shugaban Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar Jam’iyyar a zaben shugaban kas ana shekara ta 2027 mai zuwa. Shafin yada labarai na Afrika ya bayyana cewa a jiya Alhamis ce a taron Jam’iyyar wanda aka gudanar a Abuja, kuma wanda ya zo dai-dai da cika shekaru biyu da zagayensa na farko na shugabancin kasar Jam’iyyar ta nada shi Shugaba Bola Ahmed Tinubu dan shekara 73 a duniya a matsayin dan takararta a zaben na shekara ta 2027, don ya sami damar kamala shirinsa nag yare-gywaren tattalin arzikin kasar da y afara. Shugaban Tinubu dai ya kara farashin man fetur a ranar da ya hau kan kujerar...
    Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa. Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa. ‘Yan mata suna cikin hadari, galibi ana tilasta musu auren wuri ko aikin gida ko aikin jima’i maimakon a ba su damar koyo. Wata kwararriyaa fannin ilimi da ke zaune a Jos, Jihar Filato, Misis Peace Pernam, ta ce, “Ilimi wata hanya ce ta rayuwa mai muhimmanci da ke kawar da fatara, rage matsalar tsaro, da samar da ci gaban kasa, duk da haka, ga miliyoyin yara a yankin Arewa...
    Wasu masana a tarayyar Najeriya sun jinjinawa yadda Najeriya da Sin suka daga dangantakarsu zuwa huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni a bara, matakin da ya tabbatar da goyon bayansu ga kokarin tinkarar kalubalen karin harajin kwastam da Amurka ke dora musu bisa radin kai. Kwanan baya, an gudanar da taron tattaunawa kan yadda za a tinkari harajin kwastam da Amurka ke kakabawa sauran kasashe a birnin Abuja hedkwatar Najeriya, inda babban darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Najeriya Charles Onunaiju ya bayyana cewa, hadin gwiwar Sin da Najeriya bisa dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka, da shawarar “ziri daya da hanya daya” da dai sauransu, ba ingiza bunkasuwar manyan ababen more rayuwa a Afirka kadai...
    Jami’an tsaro da ke raka ayarin motocin Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum sun buɗe wuta kan ’yan Boko Haram a hanyarsu daga Gamboru Ngala zuwa Maiduguri bayan wani rangadi na kwanaki uku. Kodayake ba a san dalilin ’yan ta’addan ba, amma jami’an tsaron ayarin motocin sun bi su inda suka yi ta musayar wuta na kusan rabin sa’a tsakanin ƙarfe 12:50 na rana zuwa ƙarfe 1:30 na rana. An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe  An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin ne sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin. Wata...
    Jami’an tsaro da ke raka ayarin motocin Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum sun buɗe wuta kan ’yan Boko Haram a hanyarsu daga Gamboru Ngala zuwa Maiduguri bayan wani rangadi na kwanaki uku. Kodayake ba a san dalilin ’yan ta’addan ba, amma jami’an tsaron ayarin motocin sun bi su inda suka yi ta musayar wuta na kusan rabin sa’a tsakanin ƙarfe 12:50 na rana zuwa ƙarfe 1:30 na rana. An ceto matar da aka yi garkuwa da ita, da kama mutum 2 a Yobe  An kama wani matashi da ya yi shigar mata a Adamawa Gwamnan ya zagaya ta wasu ƙananan hukumomin ne sakamakon hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai musu, babu tabbas ko gwamnan na cikin ayarin motocin. Wata...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci Sin da Faransa su kasance karfi abun dogaro wajen tabbatar da odar duniya da inganta ci gaban duniya da jagorantar hadin kai tsakanin kasa da kasa. Da yake zantawa ta wayar tarho da shugaba Emmanuel Macron a yau Alhamis, Xi Jinping ya yi kira ga Sin da Faransa da su hada hannu wajen kare matsayi da ikon MDD da kare ka’idojin cinikayya na duniya da odar duniya da kuma tabbatar da cudanyar bangarori daban daban. Ya kara da cewa, kasar Sin tana daukar Turai a matsayin mai zaman kanta a duniyar dake da kasashe daban daban masu karfi. Ya ce, Sin na goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta karfafa cin gashin kanta...
    Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana. A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa. Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa. A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa. Dangote ya sake...
    Kamfanin Dangote wanda ya mallaki matatar mai ta Dangote ya sanar da sake sabon ragin farashin man fetur na N15 a gidajen da ke hulɗa da shi. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, ya ce a sakamakon wannan ragi, ‘yan Najeriya za su sayi man fetur a kan farashi kamar haka: Naira 875 kowace lita a Legas; Za a sayar Naira 885 kowace lita a yankin Kudu maso Yamma; A Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya za a sayar kan Naira 895 kowace lita; yayin da za a sayar da shi kan Naira 905 kan kowace lita a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, da Arewa maso Gabas. Waɗannan farashin za su yi aiki ne...
      Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana muhimman nasarori da ta cimma a fannin noma da tabbacin isasshen abinci, karkashin shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Renewed Hope. Rahoton rabin wa’adi na aiki daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2025, wanda Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsare-Tsare da Hadin Gwiwa ya fitar, ya bayyana ayyukan da Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci ta gudanar domin cika alkawurran yakin neman zaben shugaban kasa. Daya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a rahoton shi ne sabunta da inganta dakunan ajiya na abinci na kasa, wanda ya taimaka wajen rage karancin abinci da daidaita farashi a kasuwanni. Ma’aikatar ta kuma kaddamar da ayyukan gina hanyoyin ban ruwa da tafkunan ruwa domin kara...
    Shuwagabannin Amurka da Afirka ta Kudu sun yi arangama kan zargin kisan kare dangi a Afirka ta Kudu Fadar White House ta shaida wata zazzafar musayar wuta tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ya musanta zargin da ake masa na cewa Pretoria na cin zarafin ‘yan kasar fararen fata. An yi ganawar ne mako guda bayan da Trump ya yi zargin cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na yin kisan kiyashi ga ‘yan kasarta ‘yan asalin Turai. A yayin tattaunawar da ta samu halartar jami’ai daga bangarorin biyu, shugaban na Amurka ya bukaci ma’aikatansa da su nuna masa faifan bidiyo da ke da alaka da zargin kisan kiyashin, sannan Ramaphosa ya kuma mika...
    BudgIT ta buƙaci gwamnati da ta riƙa bin gaskiya da adalci wajen tsara kasafin kuɗi, domin a tabbatar kuɗin gwamnati na yi wa jama’a amfani kai tsaye. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a yau Laraba, inda jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar da ke da ruwa da tsaki ya bayyana cewa, aiwatar da matakan da suka dace bisa “Ayyuka guda goma” na hadin gwiwa da Afirka, ya haifar da sakamako mai kyau, wanda ya zuba babban kuzari ga hadin gwiwar Sin da Afirka. Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, an riga an tattauna tare da kasashen Afirka sau da dama, an kuma amince da tsarin “Kasa daya, manufa daya” wajen tsarawa da aiwatar da matakai. Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo Za A Gudanar Da Baje Kolin...
    Amma kuma kariyar ciniki ba za ta taimaka ga raya sana’o’i da masana’antu a duniya ba. Idan mun lura, a cikin shekaru 10 da suka wuce, yadda kasar Amurka ta dauki matakai na kare sana’o’in samar da karafa, a maimakon ya hana raguwar guraben ayyukan samar da karafa, sai ya haifar da karuwar kudaden da sana’o’i masu alaka suka kashe. Haka al’amarin yake ma ta fannin samar da sassan na’urorin laturoni na Chips da fasahohin kirkirarriyar basira, domin rashin yin takara da hadin gwiwa da sauran kasashe ba zai haifar da da mai ido ba, illa koma baya da illoli ga sana’o’i masu alaka. A bangaren kasar Sin kuma, yadda kasar Amurka ke yi mata kafar ungulu don dakile ci...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa wasu daga cikin sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa ƙungiyar Boko Haram ta hanyar ba su bayanai. A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na News Central, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke taimaka wa ’yan ta’adda. Hajjin 2025: Kashi 79 na maniyyatan Najeriya sun isa Saudiyya – NAHCON Gwamnati za ta sayar da gidaje 753 da EFCC ta ƙwato a hannun Emefiele  Ya ce: “Akwai masu bai wa Boko Haram bayanaj a cikin sojoji, ’yan siyasa da sauran jama’a. Za mu ƙarfafa leƙen asiri, kuma mu ɗauki tsattsauran mataki a kansu.” Gwamna Zulum ya ce dole...
    “An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista.   “Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya.   “Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba.   “Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda...
    “An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista.   “Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya.   “Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba.   “Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu nay au zai yi Magana dangabe da “Tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran da Amurka yana tanga-tanga’ wanda ni tahir amin zan karanta. Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa, da alamun tattaunawa tsakanin kasar ta kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran ba zai je ko in aba, saboda yadda bangaren Amurka a cikin kafafen yada labaransu, daga ciki har da jakadan Amurka kan al-amuran gabas ta tsakiya, kuma shugaban tawagar Amurka a tattaunawar wato Steve Witkoff  ya fito a kafafen yada labarai na Amurka yana fadar cewa duk wata yarjeniyar da za’a cimma da kasar Iran nan gaba dole sai...
    Sakataren harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwaryar Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makonni Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwarya a Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makwanni, lamarin da zai sa kasar ta fada cikin yakin basasa matukar Amurka ba ta ba ta hadin kai ba. A yayin zaman Majalisar Dattijan Amurka, Sakataren harkokin wajen kasar Rubio ya yi furuci da cewa: Idan Amurka ta yi aiki da gwamnatin Siriya, yana iya yiwuwa, gwamnatin ta samu nasara, ko kuma gwamnatin ta kasa samun nasara idan Amureka ba yi aiki da ita ba, kuma tabbas ba zata taba samu nasara ba. Ya kara da cewa: “A hasashen Amurka, idan aka yi...
    Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da yaki da rashin tsaro a kafatanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar   Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Mohammad Bello Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a taron shirye-shiryen babban taron tsaro da za a gudanar a Minna.   Janar Mohammad Bello Abdullahi ya kara da cewa Gwamnati jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da rashin tsaro, inda ya bukaci hadin gwiwa daga kowane bangare domin cimma burin da aka sanya a gaba.   A cewarsa, babban taron zaman lafiya da tsaro na farko da za...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga  Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati dake Dutse. Ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen siyan motoci Sharon guda goma sha shida da kuma motoci Golf Volkswagen guda ashirin domin raba wa mambobin ƙungiyar guda talatin da shida a matsayin tallafin dogaro da kai. Ya ƙara da cewa, majalisar ta kuma yanke shawarar fitar da...
    Ministan harkokin wajen Faransa ya kira yi tarayyar turai da ta sake bitar alakarta da Isra’ila saboda ci gaba da kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Gaza da kuma hana shigar da kayan agaji.  Matakin na Faransa dai ya biyo bayan na kasashen Spain, Ireland da kuma Holland, da suke son ganin an gudanar da bincike akan ko hare-haren Gaza din sun karya wani sashe na yarjejeniyar tasu. A karkashin yarjeniyoyin tarayya a tsakanin turai da HKI da akwai batun kare hakkin bil’adama. Tun a cikin watan Yuni na 2000 ne nahiyar turai din ta kulla yarjejeniyar ayyuka a tsakaninta da HKI a fagage da dama, da hakan ya bai wa Tel Aviv fifiko na musamman a cikin kasuwannin...
    Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato tashar talabijin din ‘aljazira’ tana fadin cewa: ” yawan sojojin da suke kashe kansu, da kuma masu kamuwa da cutukan kwakwalwa yana karuwa.” Majiyar tsaron ‘yan sahayoniya ta tabbatar da cewa; sojojin nasu sun shiga wannan halin ne na kashe kai da tabin kwakwalwa, tun bayan da su ka shiga Gaza. Tun da yakin Gaza ya barke, an sami sojojin 9000 da su ka sami tabin kwakwalwa, kuma a halin yanzu suna karbar magunguna daga asibitocin mahaukata. Su kuwa sojojin da suke kashe kansu, ba a yi musu jana’izar soja don haka ba a bayyana adadinsu.
    Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya.   Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa.   “Ya kasance mutum mai dattako wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata zaman lafiya da cigaba,” in ji gwamna Bala.   Gwamnan sai ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamacin ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya. Ya kuma jajanta wa masarautar Bauchi, iyalai da al’ummar jihar da fatan Allah ba su haƙurin juriya na wannan babban rashin.. ...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban. An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Ya ce za a bai wa ’yan sa-kai motoci shida ƙirar Toyota Hilux, ciki har da CJTF, mafarauta da ’yan banga, sannan za a bai wa sojoji ƙarin motoci huɗu masu bindiga. Zulum, ya kuma raba wa iyalai 10,000 da ke fama da talauci a yankin kayan abinci, yawancin waɗanda...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu geopolitical bisa tsarin mulkin Amurka. A jawabin da ya gabatar a wajen rufe taron tattaunawa na Tehran a jiya litinin, Qalibaf ya kara da cewa: A fagen siyasar kasa, siyasa ba ita ce kullin nauyi ba, a maimakon haka, labarin kasa shi ne ginshikin da siyasa ta ginu a kansa a matsayin wani mataki mai girma. Ya bayyana cewa: Idan ana magana game da ababen...
    Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da kai farmakin da suke kai wa Zirin Gaza tare da yin barazanar daukar matakin hukunta Isra’ila. Wannan bayani dai ya samu karbuwa daga fadar shugabancin hukumar cin kwarya-kwaryan gashin kan Falasdinawa da kungiyar Hamas, amma fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shi. Wannan dai ya zo daidai da gargadin da kasashen duniya suka yi na fuskantar bala’in jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza sakamakon killace yankin da bullar masifar yunwa...
    Mutane sun koma kwana a cikin jejin a sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara. Mazauna yankunan sukan dawo cikin gari su yini, idan dare ya yi kuma su shiga daji su kwana, sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan ta’adda, inda suka kashe mutum huɗu suka yi garkuwa da wasu 26. Wani mazaunin Ƙauran Namoda da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce adadin mutanen zai iya cin haka, inda ya tabbatar cewa maharan sun kashe wata mata tare da sace wasu 26. Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da wani magidanci da matansa biyu da ’ya’yansa uku. An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin...
    Akalla dalibai marasa galihu 300 da ke makarantun gaba da sakandare daga zababbun al’ummomi a kananan hukumomin Edu/Patigi/Moro na jihar Kwara sun samu tallafin karatu don tallafa musu.   Da yake jawabi a wajen taron rabon tallafin karatu da aka gudanar a Ilorin, mai taken “Hatsarori na Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi Tsakanin Dalibai A Manyan Makarantu” wanda Michael Imoudu tare da hadin gwiwar mamba mai wakiltar mazabar Edu/Moro/Patigi na Jihar Kwara, Ahmad Adamu -Saba ya shirya, ya ce za a yi rabon ne kashi biyu.   Dan majalisar wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa, Muhammed Salihu, ya ce manufar shirin bayar da tallafin shi ne tallafawa daliban da iyayensu ba za su iya biyan wasu kudadensu a makaranta ba.  ...
    Yemen ta yi barazanar killace babbar tashar jiragen ruwan Haifa ta Isra’ila, tare da gargadin cewa jiragen ruwa da ke tafiya a can. “Dukkan kamfanonin da jiragensu ke nan ko kuma suka nufi wannan tashar, ana sanar da su cewa, ya zuwa wannan sanarwar, an saka tashar cikin jerin wuraren da muke son kaiwa hari,” in ji kakakin kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a Yemen Yehya Saree. Rundunar sojin Yeman ta ce kakaba takunkumi na a matsayin mayar da martani ga yadda gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.   Sanarwar ta ce sojojin Yemen ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar...
    Mai dakin Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta sake jaddada kudurin gwamnatin jihar na ganin an kawar da tu’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar. Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta karɓi shugabannin Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Hana Safarar Mutane ta Jihar Zamfara, waɗanda suka kai mata ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Gusau. Hajiya Huriyya ta bayyana shirinta na yin aiki kafada da kafada da hukumar, domin gano ingantattun hanyoyin da za su taimaka wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a fadin jihar. “Muna shirin zama tare domin duba hanyoyin da za mu bi wajen magance matsalolin da kuke fuskanta, domin muna da aniyar ganin Zamfara ta nisanta daga illar...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kira mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehran zuwa ma’aikatar don gabatar mata da korafi kan yadda jami’an tsaron kasar Burtaniya suke kama yan kasar Iran ma zauna birnin London tare da tuhumarsu da ayyukan Leken asiri wa JMI. Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a cikin wannan watan Mayu da muke ciki Jami’an yansanda a kasar Burtaniya sun kama Iraniyawa mazauna birnin London har guda 7 a sumamen guda biyu da suka kaimasu a gidajensu. Labarin ya kara da cewa an gabatar da mutane uku a gaban kotu a birnin London tare da tuhumar su da aikin leken asiri ga JMI. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara...
    Aƙalla mutum uku aka kashe, yayin da aka sace 26 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai yankin Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda, a Jihar Zamfara. Harin ya faru ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar a ƙauyukan da suka haɗa da Sabon Gari da Kungurki. Mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta yi murabus Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200 Wani mazaunin yankin ya ce: “Mutane sun fara barin gidajensu da daddare, suna dawowa ne da safe. Hare-haren da ake kai wa Sabon Gari da maƙwabtan ƙauyuka na ƙara tsananta.” Ana zargin yaran wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Bello Kaura wanda aka fi sani da Dan Sade ne da...
    Akalla mutane uku ne aka ce an kashe tare da yin garkuwa da wasu 26 a wani sabon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Kauran Namoda da ke jihar Zamfara. Daily trust ta bankado cewa, hare-haren na tun ranakun Alhamis zuwa Asabar, sun shafi al’ummomi da dama a yankin. Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Bisa Daidaito A Afirilu Yanzu-Yanzu: Ana Zargin Makiyaya Sun Kashe Mutane 15 A Benuwe Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, lamarin ya fi kamari akauyen Sabon Gari, inda aka kashe mace guda tare da yin garkuwa da mazauna yankin kusan 20. Wani mazaunin Kauran Namoda, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya yi ikirarin cewa, adadin ya zarta haka, inda ya...
    Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta ce duk da matsi sakamakon dalilai na ciki da na waje, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa daidaito a watan Afirilun da ya gabata. Alkaluman da NBS din ta fitar a Litinin din nan sun nuna karuwar hajojin da manyan masana’antun kasar ke samarwa da kaso 6.1 bisa dari a shekara, yayin da alkaluman samar da hidimomi suka karu da kaso 6.0 bisa dari a shekara. Sai kuma darajar jimillar hajojin sayayyar daidai, ta kayayyakin bukatun yau da kullum da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 3.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 515.6 a shekara, adadin da shi ma ya yi karuwar kaso 5.1 bisa dari. Kazalika, alkaluman sun nuna daga watan Janairu...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da taron tattaunawa ta Tehran wanda aka bude a ranar Lahadi 18 ga watan mayu a nan Tehran. A ranar Lahadi 18 ga watan Mayu da muke ciki ne aka bude taron tattaunawa da ta Tehran ta farko a nan Iran, don tattauna batutuwan da suka shafi kasashen yankin yammacin Asiya. Inda shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran suka gabatar da jawaban farko a taron. An sami halattan baki daga kasashe 53 daga cikinsu akwai jami’an gwamnatoci wadanda suka hada da ministoci  masana da shuwagabannin cibiyoyin bincike da bada shawarori na kasashen duniya da dama. Daga cikin bakin akwai ministan...
    Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
    Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta yi kakkausar suka ga gwamna Dauda Lawal kan kalaman da ta bayyana a matsayin bata gari dangane da kokarin gwamnatinsa na magance ‘yan fashi da makami da kuma bayar da tallafi ga wadanda ‘yan fashin suka kashe.   Hakan ya biyo bayan wani faifan bidiyo ne da aka ga gwamnan yana magana da manema labarai kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da harkokin tsaro da kuma jin dadin wadanda matsalar tsaro ta shafa.   A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana kalaman gwamnan a matsayin rashin gaskiya da yaudara.   Malam Idris Yusuf Gusau ya yi zargin cewa, gwamnatin ta gaza cika wasu...
    “Mutanen Zamfara ba wawaye ba ne. Gwamnan ya kamata ya daina waɗannan maganganun ƙarya, ya daina farfaganda, ya kuma haɗa kai da masu ruwa da tsaki na gaskiya don magance matsalar tsaro,” in ji Gummi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Akalla manoma 90 ne mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka kashe a Jihar Borno cikin watani biyar da suka gabata. Mayakan kungiyar sun kuma yi garkuwa da wasu da dama baya ga wadanda suka tsallake rijiya da baya a hare-haren kungoyiyoyin da raunin harbi. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa kungiyoyin ‘yan ta’addan sun kai hare-haren ne a tsakanin watan Janairu zuwa Mayun nan da muke cikin na shekarar 2025. Hari na baya-bayan nan shi ne wanda mayakan kungiyar ISWAP suka yi ritsa manoman da ke aiki a gonakin wake suka yi wa mutum 50 kisan gilla a yankin Karanti da ke Karamar Hukumar Kukawa a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu. Gwamnatin Kano ta dakatar da haska shirin...
    Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
    A wancan lokacin,Mrs. Bintu M.Sadik, cewa tayi  Sir S.M. Banaman shi ne Shugaban Kwalejin na farko duk kuma Malaman Turawa, daga baya ne aka dauke Hausawa ‘yan asalin wurin saboda su koyar da Hausa da kuma al’amarin daya shafi addinin musulunci.Ta ce mshahuran ‘yan Arewa sun halarci Kwalejin daga cikinsu akwai Firayim Minista na farko Abubakar Tafawa Balewa,Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan  Arewa, da kuma Sir Kashim Ibrahim,  da dai sauran wasu duk sun halarci Kwalejin ta Katsina An samu labarin kasar Katsina ta taba kasancewa wata babbar cibiyar Kasuwanci ta Sahara. Wannan  shi tun  lokacin da aka hade Arewa da Kudancin Nijeriya Katsina tana daya daga cikin wuraren da  hanyar jirgin kasa ta bi ko kuma Layin Dogo ...
    A gauraya kayan hadi cikin zumar, a rika sha cokali 3 da safe bayan karyawa da kuma da dare kafin kwanciya. A fara amfani da wannan hadi kafin zuwan al’ada, sannan a ci gaba har ciwon ya lafa, da izinin Allah. Ciwin Ciki na mata mai  zafi Hadi mai matukar karfi: Garin hulba cokali 7, Garin habbatussauda (habbur rashad) cokali 7, Man zaitun cokali 10 Yadda ake amfani da shi: A gauraya su wuri guda. A rika diban cokali 2, a tafasa, sai a tace, sannan a zuba zuma kadan a ciki sai a sha. A fara amfani da wannan hadin kwana 5 kafin zuwan al’ada, a ci gaba har lokacin al’adar. Wannan zai kara lafiya da ni’ima a jiki....
    Gobara ta tashi a Kwalejin Karatun Alƙur’ani da ilimin addinin Musulunci mallakin fitaccen malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da ke Rafin Albasa, a Jihar Bauchi, inda ta ƙone ginin makarantar da kayan cikinta. Binciken wakilinmu ya gano cewa gobarar ta lalata bene mai ɗakuna da dama ciki har da ofisoshi, ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan kwamfuta, da ɗakunan karatu. Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa An kuma rasa kayan sawa na malamai da ɗalibai, katifu, barguna da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum. Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Sai dai daraktan makarantar, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, ya ce sun...
    Jiragen na sojojin HKI sun kai hari ne dai a yau Lahadi a kan hanyar da ta raba tsakanin garin Beit-Yahun da Bent-Jubail dake kudancin kasar. A garin Kafar-kalla ma wani jirgin saman marar matuki ya jefa bama-bamai masu sauti a kusa da wani gida da dama an rushe shi. Harin na sojojin HKI yana cikin ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon da take yi wanda ya wuce 2000 tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Nuwamba na 2024.  Bugu da kari HKI ta girke sojojinta a cikin wasu wurare 5 dake kan iyaka,wanda shi ma keta karjejeniya ce. Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hizbullah ta sha yin kira ga gwamnatin kasar da ta yi duk abinda...
    A wani rahoton da MDD ta fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa, tun daga 2024 ne yunwar da ake fuskanta a duniya ta kara tsanani domin ta shafi mutanen da sun kai miliyan 295. Rahoton  ya kara da cewa; wannan adadin na mutanen dake fama da yunwa mai tsanani suna warwatse a cikin kasashe 53 na duniya. A  Juma’ar da ta gabata aka fitar da wannan rahoton. Haka nan kuma an bayyana cewa idan aka kwatanta da yunwar da aka yi fama da ita a shekarar 2023, to da aka shiga 2024 an sami karuwar masu fama da matsananciyar yunwar da adadinsu ya karu da  miliyan 13.7. Shekaru shida kenan a jere da ake samun karuwar yawan mutanen...
      Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Kin san komai a rayuwa akwai abin da Allah ya tsara maka kuma duk abin da Allah ya tsara maka za ka ga sai ya tabbatu, ni dai farko mahaifiya ta zan iya ce miki tsohuwar furodusa ce ta taba ‘producing film’ a da’, Momi Jamila Haruna Allah ya ji kanta kawar ta ce tare suke tun muna yara ba mu san za mu shiga harkar ba, har muka shiga harkar. Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance? Eh! to, kin san ita rayuwa ba za ka ce baka samu irin akasi ko damuwa da wannan ba, amma ni dai gaskiya zan iya ce miki Alhamdulillahi ni dai...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta ceto wata tsohuwa mai shekaru 80 da aka sace a Jihar Kano, bayan wani samame da suka kai Ƙaramar Hukumar Garki. A yayin samamen, sun kashe mutane biyar da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sannan sun kama wasu biyar. Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso Rahoton ya ce samamen ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar 16 ga watan Mayu, 2025 bayan samun sahihan bayanan sirri. Waɗanda suka sace tsohuwar, Hajiya Hajara daga Ƙaramar Hukumar Minjibir, a Jihar Kano, su 12 ne ɗauke da bindigogi, kuma sun zo ne a kan babura. Rundunar ta haɗa...
    Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta bayyana cewa, gidajen tarihi na sassan kasar sun gudanar da bukukuwan nune-nunen kayayyaki 43,000, da tarurrukan ilimi 511,000. An bayyana wadannan alkaluman ne a yau Lahadi a wani bikin tunawa da ranar gidajen tarihi ta duniya a gidan adana kayayyakin tarihi na babban mashigin ruwa wato Grand Canal a Beijing. A cikin shekarar 2024, an yi rajistar sabbin gidajen tarihi 213 a kasar Sin, inda hakan ya kara yawan adadin gidajen tarihi na kasar zuwa 7,046, kamar yadda hukumar kula da su ta bayyana. Kazalika, ta kara da cewa, kasar Sin tana kara fadada manufofinta na shiga gidajen tarihi ba tare da biyan kudi ba, inda sama da kashi 91 cikin...
    Sojojin Yemen sun kai hari filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami guda biyu da kuma jirgin sama mara matuki ciki Sojojin Yemen sun sanar a yau Lahadi cewa: Sun kai hari kan filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makamai masu linzami guda biyu da kuma jirgin sama maras matuki ciki. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa: Sojojin Yemen sun kai hari da makami mai linzami kan filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke Jaffa da makami mai linzami guda biyu, daya daga cikin makami mai linzami na Falastinu 2 da kuma makami mai linzamin Dhu al-Fiqar....
    Bayan da wani matashi ɗan shekara 33 ɗan kasar Japan mai suna Honkon ya yi tarin kuɗi na tsawon shekaru 10 don siyan motar da yake mafarki — na wata sabuwar mota ƙirar Ferrari 458 Spider — sai ya zauna yana kallon yadda motar take ƙonewa cikin sa’a ɗaya da tuƙa ta a karon farko. Kafofin sada zumunta na ƙasar Japan sun yi sharhi game da rahoton baƙin ciki na Honkon, matashin da ya kasance mai shirya wakoki, wanda ya kashe makudan kuɗi game da mafarkin sayan motarsa ta Ferrari, sai dai ya kalle ta tana ci da wuta a ranar da ya tuƙa ta a karon farko. ISWAP ta kashe manoma sama da 50 a Borno Guguwar raba Masarautar...
    Kasar Faransa ta mika iko na sansanin soja na Contre-Amiral Protet ga kasar Senegel, wanda shi ne sansanin soja na 3 da aka mikawa kasar a bana. An mika sauran sansanoni biyu da suka hada da Marechal da Sanit-Exupery ne a watan Maris din da ya gabata, Kuma dukkan sansanonin na da mazauni ne a Dakar, babban birnin Senegal. Wata sanarwa da ofishin jakadancin Faransa ya fitar, ta ce an tsara mika dukkan wasu sansanonin dake karkarshin ikon Faransa a Senegal a bana, biyo bayan yarjejeniyar da kasashen biyu suka yi. A ranar 31 ga watan Disamban 2024, shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya sanar a jawabinsa na sabuwar shekara cewa, za a bukaci dakarun Faransa su fara janyewa daga...
    A farkon wannan sati ne wata takardar neman raba Masarautar Katsina ta bayyana, wadda take neman a ƙirƙiro ƙarin masarautu uku da suka haɗa da ƙarin sarki mai daraja ta ɗaya da mai daraja ta biyu da kuma mai daraja ta uku. Takardar wadda aka gani da tambarin da ke nuna alamar an miƙa ta ga Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta tayar da ƙura, inda ake ta musayar yawu kan abin da ta ƙunsa da kuma abin da zai iya biyo baya. Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma ISWAP ta kashe manoma sama da 50 a Borno Wakilinmu ya gano cewa takardar, wadda kafar yaɗa labarai ta Katsina Times ta fara wallafa wa a kafofin sada zumunta,...
    Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirarren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da Dala biliyan 1 a kudin tikitin shiga a kasuwar cikin gida kadai. Bugu da kari, wannan adadi, ya haura sama da Dala biliyan 2 a kudaden shiga...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara da cewa da dama daga cikin maganganunsa basu cancanci maida martani ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Asabar, a lokacinda yake ganawa da wasu malaman makaransu daga larduna daban daban na kasar, a Husainiyyar Imam Khonaini (q) a nan Tehran. Jagoran ya kara da cewa : Trump yace yana son amfani da karfin da Amurka...
    A taron kasashen larabawa karo na 34Th wanda ake gudanarwa a birnin Bagdaza na kasar Iraki, shuwagabannin kasashen larabawa sun bukaci tsagaita wuta a gaza sannan sun yi kira da aka kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, shuwagabannin sun bukaci a magance matsalolin da suke faruwa a Siriya Lebanon da kuma sudan. Ana taron shuwagabannin kasashen larabwa a Bagdaza ne a dai dai lokacinda gwamnatin HKI take kara fadada hare-hare a kan zirin Gaza da kuma kashe Falasdinawa maza da mata da yara mutkar abinda zata iya kashewa. Majiyar kiwon lafiya ta Gaza ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu sojojin HKI sun kashe falasdinawa kimani 53,272 mafi yawansu mata da...
    Wani babban jami’in kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza ya bada sanarwan cewa an fara tattaunawa da HKI ta kawo karshen wannan yakin a birnin doha ba tare da shimfida wasu sharudda ba. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto Taher Annunu daga daga cikin manya-manyan jami’an kungiyar ta Hamas yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa tattaunawar zata hada dukkan matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu. Annunu ya ce kungiyarsa zata gabatar da dukkan abubuwan da yakamata a tattaunawa a kansu kama daga tsagaita wuta, musayar fursinoni da kuma ficewar sojojin HKI daga Gaza. Majiyar HKI ta nakalto firai ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa ya aika tawagar tattaunawarsa zuwa birnin Doha na kasar Qatar.
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina ta sanar cewa, za a fara jigilar maniyyatan jihar a ranar Lahadi 18 ga wannan wata na Mayu, 2025, zuwa Ƙasa Mai Tsarki. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Badaru Bello Karofi, ya shaida wa wakilinmu, cewa maniyyatan da suka fito daga Malunfashi da Bakori, Ƙanƙara, Dandume, Ƙafur da Ɗanja sune rukunin farko da ake sa ran za su tashi daga filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa da ke cikin babban birnin jihar. Tun farko sai da jagoran mahajjatan jahar, wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Joɓe ya bayyana cewar, gwamnatin jihar ta ɗauki duk wasu matakan da suka wajaba tun daga gida har zuwa Ƙasa...
    Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, ta dakatar da dukkanin cibiyoyin gudanar da taro da ke faɗin jihar, tare da haramta gudanar da bikin ‘Kauyawa Day’ gaba ɗaya. Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar, bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar. ISWAP ta yi wa manoma 15 yankan rago a Borno Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas Ya ce wannan mataki na cikin sabuwar doka da majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da ita, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanya wa hannu. “Daga yanzu, duk wanda ya shirya wani taro da sunan Kauyawa ko Villagers Day, ya karya doka,” in ji El-Mustapha. Sabuwar dokar ta bai wa hukumar...
    Shugaban kasar Iran ya jaddadacewa: Sun yi Imani da tattaunawa, amma ba su jin tsoron duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Tabbas Iran tana gudanar da zaman tattaunawa da Amurka amma ba ta tsoron duk wata barazanarta, yana mai nuni da kalaman Trump da ke cin karo da juna, wani lokaci yana magana kan zaman lafiya sannan a wasu lokutan yana barazana da yaki. A jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru biyu da samun nasarar tawagar “Rukunin Jirgin Ruwa na 86” na sojojin ruwan Iran, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yaba da sadaukarwar da jaruman da suka yi wannan hidimar, yana mai cewa: “Suna alfahari da kasancewar dakarunsu, yana mai...
    Tsohon fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Fira ministan Netanyahu ya yi sakaci da rayuwar yahudawa a cikin aikinsa don haka hambarar da gwamnatinsa ita ce mafita Tsohon Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Barak ya yi kira da a hambarar da Benjamin Netanyahu da gwamnatinsa, yana mai zarginsa da yin sakaci wajen kubutar da fursunonin yahudawa da suke hannu ‘yan gwagwarmaya a Zirin Gaza. Barak ya ce: Netanyahu yana sakaci da rayuwar fursunonin yahudawa da ake tsare da su a Gaza domin faranta wa masu tsattsauran ra’ayi a gwamnatinsa rai.” Ya bayyana shi a matsayin mai sakaci wajen gudanar da ayyukansa, da kuma ci gaba da kisan kiyashi a Zirin Gaza domin karecmanufofin siyasa saboda neman...
    Sai ya ce “Na riga na amsa wannan tambayar amma har yanzu kana sake maimaita ta. Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jarida 43 mazauna Kaduna ne suka halarci taron, ciki har da wasu ‘yan jarida daga wasu jihohin da suka raka gwamnonin nasu. Don haka, ba daidai ba ne a ce na hana ‘yan jarida shiga taron gwamnonin Arewa. Duk jaridun kasar nan sun je a wurin. Duk gidajen rediyo da talbijin na Kaduna suna wurin. Duk wakilan manyan gidajen Talabijin da Rediyo da ke wajen Kaduna su ma suna nan. Kada ka dauki maganata a wani bangare daban, je ka bincika. Duk wadannan labarai ne irin na teburin mai shayi. Ni kuma ban sani ba. Abin da...
    “Dangote ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba wanda ya cancanci yabo. Muna kan tattauna yadda za a kawo karshen rigimar. Nan gaba, za mu yi aikin hadin gwiwa domin tabbatar da samar da wadataccen mai ga al’ummar Nijeriya,” in ji shi. Ya nuna cewa ta hanyar zaman sulhu za su kawo karshen matsalar, “Nan gaba kadan ba za ku ji wata rigima tsakanin NNPCL da matatar mai ta Dangote ba. Za mu yi aikin hadin guiwa domin amfanuwar ‘yan kasa.” Ojulari ya kuma yi tsokaci kan faduwar farashin danyen mai a duniya a baya-bayan nan, wanda ya rage kudaden shiga da ake sa ran Nijeriya za ta samu. “Wannan raguwar ta shafi kasafin kudin Nijeriya tun da babban...
    Wata mata da age zargin ta cije mazakutar saurayinta ta shiga hannun ’yan sanda. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta kama matar mai shekara 43 ne bayan ta yi wa masoyin nata wannan aika-aika ne a lokacin da suke rikici a cikin gida a unguwar Mile 3 da ke yankin Diobu a garin Fatakwal babban birnin jihar. Lamarin wanda ya afku a ranar Alhamis, ya girgiza mazauna titin Bishop Okoye mai yawan jama’a lokacin da aka samu labarin lamarin. A cewar majiyoyi, rikicin ya fara ne lokacin da masoyin matar ya nemi kwanciya da ita. An bayar da rahoton cewa matar ta ƙi amincewa da buƙatar saurayin nata, inda ta zarge shi da yin amfani da ƙwayoyin masu ƙara kuzarin...
    Gwamnatin Isra’ila ta yi barazanar kashe jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Abdul-Malik al-Houthi, idan har Sana’a ta ci gaba da kai hare-hare da makami mai linzami kan Isra’ilar don goyon bayan Falasdinu. Ministan harkokin soji na gwamnatin, Isra’ila Katz ya ce idan har Yemen ta ci gaba da ayyukanta “za su sha azaba mai radadi.”  Katz ya ce kisan da gwamnatin za ta wa al-Houthi zai yi kama da kisan gilla kan “Deif da Sinwars a Gaza.” Ministan na Isra’ila yana magana ne a kan tsohon kwamandan kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da ke Zirin Gaza, Mohammed Deif, wanda gwamnatin kasar ta sanar da kashe shi a watan Janairu. Katz ya kuma ce yuwuwar nasarar kisan gillar da gwamnati...
    A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa. Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama abin tsoro kuma ya nuna akwai jan-aiki. “Alal misali, a jihar da ke da mutane kusan miliyan 6 tare da tarin ƙalubale, na’urar duban ɗan tayi ɗaya ce kawai a cikin dukkan cibiyoyin da gwamnati ta mallaka, kuma shi ma duk faci ne a jikinsa da salataf ko’ina! Nan take na ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya don dawo da ababen more rayuwa, samar...
    Aƙalla mutum biyar ne sun jikkata bayan da gobara ta tashi a gidan man Nobpet da ke kusa da mahaɗar Sojojin Sama a garin Fatakwal, Jihar Ribas. Gobarar ta kuma ƙone sama da motoci takwas da aka ajiye kusa da ofishin Hukumar Sufuri ta Jihar Ebonyi. Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba  Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Ma’aikatan kashe gobara na Jihar Ribas tare da haɗin gwiwar na Sojojin Sama ne suka yi aiki tare har suka iya kashe gobarar. Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Emmanuel Ninyaegwu, wanda direba motar haya ne, ya ce motarsa mai ɗaukar fasinja 18 ta ƙone gaba ɗaya. Ya...
    A yau Jumma’a, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya yi hadin gwiwa da kawancen gidajen rediyon Turai na EBU wajen gabatar da rahoton Report ITU-R BT.2550, wato fasahar tsara shirye-shiryen bidiyo da rediyo ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta 5G, a shafin intanet na kwancen harkokin sadarwa na duniya wato ITU. Lamarin da ya nuna cewa, CMG ya taka muhimmiyar rawa a fannin tsara shirye-shirye masu inganci, ya kuma kai matsayi na gaba a fannin fitar da fasahohin tsara shirye-shiryen zamani masu inganci. (Mai Fassara: Maryam Yang)     Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Sojojin da suke aiki a ƙarƙashin rundunar birget ta 6 da ke garin Jalingo a Jihar Taraba sun kashe ’yan bindiga biyu tare da ƙwato shanu guda dubu ɗaya daga hannun ɓarayin shanu. Muƙaddashin Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojoji ta birget ta 6 da ke garin Jalingo, Kyaftin Oni Olubodunde ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Jalingo a ranar Juma’a. Tinubu zai halarci rantsar da sabon Fafaroma Leo An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno Ya ce, nasarar ƙwato shanu tare da kashe ’yan bindigar ya kasance ne biyo bayan wani bayanan sirri da rundunar ta samu dangane da shuguban wasu guggun ’yan bindigar akan bubura talatin...
    Kididdigar da ma’aikatar kula da harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta yi, ta nuna cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun bana, adadin yarjejeniyoyin da suka shafi fasaha da aka kulla ya kai dubu 228 a kasar Sin, wadanda suka shafi Yuan triliyan 1 da biliyan 600, adadin da ya karu da kaso 13.3 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Lamarin da ya nuna cewa, kasuwar fasaha ta kasar Sin tana bunkasuwa yadda ya kamata.   A matsayin daya daga cikin muhimman kasuwanni 5 na kasar Sin, bunkasuwar kasuwar fasaha tana da muhimmanci ga aikin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sana’o’i. Kididdigar ta nuna cewa, a shekarar 2024, jimillar kudaden da aka samu daga...
    “Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne.   “Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.”   Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi.   Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane uku da ake zargi ɗauke da buhuna 20 na haramtattun takin zamani samfurin “Urea”. An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Borno DSP, Nahum Kenneth Daso ya fitar a ranar 15 ga Mayu, 2025. Cikin makonni kaɗan Obasanjo ya murƙushe Boko Haram — Atiku Gwamnatin Katsina za ta gina birnin dawakai na farko a Afirka Rundunar kai ɗaukin gaggawar (RRS), ƙarƙashin jagorancin Kwamishin ‘Yan sandan jihar CP Yusufu Mohammed Lawal ne ta kama waɗanda ake zargin a ranar 13 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na safe a unguwar Tashan Journey, Maiduguri. Waɗanda ake zargin sun haɗa da, Shamsuddeen Rabiu mai kimanin shekara 35,...
    Shugaban Runkunin Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya bayyana shirinsa na karya farashin shinkafa a Najeriya, yana mai cewa nan gaba kadan wadanda suka saye shinkafar suka boye suna jiya ta yi tsada, za su tafka mummunar asara. Dan kasuwar ya kuma bayyana cewa suna tattunawa da Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, kan hanyoyin da za su bi domin ganin sun daidaita farashin siminti. BUA ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa. “Farashin kayan abinci na saukowa a Najeriya kuma muna yin duk abin da za mu iya na ganin cewa mun mara wa gwamnati baya a kan hakan,”...
    “Wannan ya ba wasu jihohi fiye da goma sha daya ‘yancin kai, tare da karin wadanda ake sa ran za su biyo baya. Wadannan jihohin yanzu suna iya shiga cikin masana’antar wutar lantarki, daga samarwa har zuwa isarwa, rarraba, har ma da samar da mitoci.” “Na biyu, dole ne mu magance rashin ingancin ababen more rayuwa, wanda ya taru a cikin shekaru 60 da suka wuce saboda rashin kula da rashin isasshen zuba jari don farfado da tsarin zamanantar da wutar lantarki.” Ministan ya kuma jaddada bukatar cike gibin mita na sama da kashi 50 bisa dari, yana mai cewa shirin shugaban kasa yana nufin cimma wannan ta hanyar girka mita miliyan 18 a cikin shekaru biyar masu zuwa. Ya...
    A yayin da Babbar Sallah ke ƙara ƙaratowa, ’yan kasuwar dabbobi sun bayyana fargaba game da yiwuwar farashin raguna da sauran dabbobin lauya zai yi tashi gwauro a Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar ta sanya takunkumin wucin gadi kan fitar da dabbobi zuwa ƙetare, gami da yawaitar sace-sacen dabbobi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya. A farkon watan nan na Mayu ne Gwamnatin Nijar ta sanar cewa matakin na da nufin daidaita farashi dabbobin layya a cikin gida da kuma tabbatar da wadatarsu ga al’ummarta —waɗanda mafi rinjaye Musulmi ne — kafin zuwan Babbar Sallah a farkon watan Yuni. Haramcin ya shafi fitar da shanu da tumaki da awaki da raƙuma, tare da...
    Harajin ya kuma kai kasa da kimanin kaso 11 a cikin dari, wanda ya kai kasa da wanda ake karba, idan aka kwatanta da duniya. “Abinda muka yi shi ne, mun cire daukacin ma’aikatan da karbar kasa kaso uku a cikin darei a cikin tsarin na karabar harajin,” Inji tsohon Shugaban LLP. Ya shedawa manyan Malaman Makaranta  da Jami’an da ke katbar haraji hakan ne, a wani taro da aka gudanar a jihar Legas Nijeriya dai, ta kasance kasar da sama da alumominta miliyan 8o, ke fama da kangin talauci. Hakan ya kuma kara haifar da hauhawan farashin kayan masarufi, musamman yadda kayan suka tashi a 2024, kafin su sauka zuwa kaso 24.2 a cikin dari. Kazalika, hauhauwan farashi da...
    Haramun ne ga mai harama namiji ya daura duk wani abu dinkakke, sai dai hirami kawai. Amma idan bai samu hirami ba, babu laifi ya daura wando kamar yadda Abdullahi bin Abbas (RA) ya ruwaito daga cikin hudubar da Annabi (SAW) ya yi a ranar Arfa. Idan mai harama bai samu silafas ba, zai iya sanya takalmi sawu-ciki, amma ya yanke shi zuwa karkashin idon sawunsa kamar yadda ake wa khuffi. Wannan duk an haramta ne ga namiji. Amma ita mace babu abin da ya haramta mata illa sanya turare, nikabi da safar hannu, kamar yadda Abdullahi bin Umar (RA) ya ruwaito daga Manzon Allah (SAW). Haka nan kar ta sanya kayan da aka yi musu rini da turare, amma...
    Sojojin Najeriya sun kai wani mummunan harin ramuwar gayya kan sansanonin ’yan ta’adda a Dajin Sambisa, inda suka kashe mayaƙa da dama tare da tarwatsa maɓoyar miyagun. Sojoji sun ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan kisan abokan aikinsu huɗu da ’yan ta’adda suka yi a farkon wannan makon. Kai tsaye sojojin suka kai hari kan sansanonin ’yan ta’addar da ke Garin Malam Ali da Garin Glucose da kuma da Ukuba, waɗanda ke cikin Dajin Sambisa. Wannan matakin da aka ɗauka ya biyo bayan jerin hare-hare da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a ranar Talata kan sansanonin sojoji guda uku a Rann da Gajiram da kuma da Dikwa a Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji hudu....
    Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma. Akasarin fadin kasar nan, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma duba da cewa, wadannan yankunan biyu, sun yi fice wajen yin noma, amma abin takaici, ‘yan bindiga daji, ‘yan ta’adda da kuma wasu Fulani Makiyaya, sun mayar da wadannan yankunan fagen daga, inda suka kashe manoma da kuma lalata amfanin gonakansu. Bugu da kari, wadannan bata garin sun kuma kone wasu gidajen alumomin da ke a...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba A yayin ganawarsa da masu fafutukar siyasa da zamantakewa a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar Iran a jiya Alhamis, shugaban na Iran Masoud Perzeshkiyon ya ce za a gudanar da shawarwari kan shirin makamashin nukiliyar Iran cikin karfin gwiwa da mutunta juna, yana mai jaddada wajabcin rashin mika wuya ko mika kai ga duk wata barazana. Shugaba Pezeshkiyon ya jaddada cewa yin shawarwari ɗaya ne daga cikin ka’idodin hankali da zurfin tunani, amma ba a kan kowane farashi ba. Dole ne a gudanar da shawarwari cikin aminci da mutuntawa tare da bin ka’idojin kasa da kare kima....
    A cewarsa, yanzu haka ana sayar da shinkafa kimanin naira 60,000 kan kowane buhu, buhun fulawa kan naira 55,000, da masara a kan Naira 30,000.   Ya yi bayanin cewa, kafin zartar da umarnin rage harajin kwastam kan kayayyakin abinci, ‘yan kasuwa kan sayen kayan abinci tun yana gona su boye, sannan su sayar da shi a farashi mai tsada. Ya kara da cewa, “Amma a yanzu, wannan shirin ya kare, yanzu masu irin wannan halin, asara kawai suke kirgawa Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Majalisar wakilai za ta binciki yadda aka samu mummunar faduwa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) ta 2025 da hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta gudanar kwanan nan. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa, Adewale Adebayo ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Da yake gabatar da kudirin, ya koka da cewa, da yawa daga cikin daliban, sun yi tafiya mai nisa domin zana jarabawar UTME a cibiyoyin jarabawar. Amma abin takaici, sai ga sakamakon ya fito da koma baya da yawa. Duk da cewa, hukumar JAMB ta amince cewa, tangardar na’ura ce ta janyo faduwar amma akwai bukatar a binciki hukumar. Idan za a iya tunawa, sakamakon jarabawar UTME na 2025 da JAMB...
    Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka kaɗan a watan Afrilu 2025 zuwa kashi 23.71, daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan na nuna cewa hauhawar farashi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda a watan Afrilun 2024 aka samu kashi 33.69. Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Wuta ta kashe ɓarawon wayar lantarki a Jigawa Wannan ragi da aka samu a watan Afrilu ya kai kusan kashi 10. Har ila yau, hukumar ta ce hauhawar farashi daga wata zuwa wata ya ragu a watan Afrilu, inda aka samu kashi 1.86, ƙasa da kashi 3.90 da aka samu a watan...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga hukumomin gwamnati da shugabannin makarantu da su ba da fifiko wajen kula da duk wasu gine-ginen makarantu da aka gyara domin kiyaye abubuwan da kuma tabbatar da ci gaban fannin ilimi.   Gwamna Dauda Lawal ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da sabuwar makarantar sakandaren Larabci ta mata ta gwamnati da aka gyara tare da inganta ta a garin Gusau.   Ya bayyana cewa, aikin sauran makarantun da ake gudanarwa a fadin jihar, wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na farfado da tsarin makarantun kwana, tare da karfafa tsaro domin kare makarantu da kewayen su.   A cewar Gwamna Lawal, inganta kayan aikin makarantu na da matukar muhimmanci wajen...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da jirgin farko na maniyyatan jihar Kano da ke niyyar gudanar da aikin hajjin bana.   Gwamna Abba Kabir Yusif, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu na gari a jihar, su kuma yi addu’ar zaman lafiya, ci gaba, da hadin kan jihar Kano da Nijeriya baki daya.   Ya jaddada kudirin gwamnati na tallafa wa duk maniyyata a duk tsawon zamansu a kasa mai tsarki.   Tun da farko, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, ya shawarci alhazai da su kwantar da hankulansu, su kuma maida hankali wajen gudanar da ibada.     A nasa jawabin babban daraktan hukumar jin dadin...
    Majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da dokar hukumar kula da manyan makarantu ta jihar Kaduna, ta shekarar 2025, ya zama doka. Dokar dai na da nufin daidaita harkokin gudanar da manyan makarantun sakandire a fadin jihar domin daidaita tsarin ilimin zamani.   Da yake jagorantar zaman majalissar, mataimakin kakakin majalisar Mista Henry Magaji Danjuma ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta inganta yadda ake gudanar da manyan makarantun sakandire a jihar.   Kudirin dokar ya biyo bayan gabatar da rahoton Barr. Mahmud Lawal Isma’ila, shugaban kwamitin hadin gwiwa kan ilimi da shari’a, kuma wakilin mazabar birnin Zaria. Ya bayyana cewa dokar ta zama dole ne ta hanyar gyare-gyaren nan a tsarin ilimin Najeriya.   “A da, mun gudanar da...
    Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hada kai da tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano, domin bayar da takardar shaidar difloma ga masu amfani da shafukan sada zumunta da ke da hannu wajen tallata manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf.   Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana hakan a karshen taron yini biyu da aka gudanar a Kano.   Kwamared Waiya ya ce horon na da nufin inganta yadda mahalarta taron ke amfani da kafafen sada zumunta wajen musayar bayanai da suka shafi ayyukan gwamnati.   “Kwas din diflomasiyyar da aka gabatar zai inganta karfin mahalarta don yin amfani da dandamali na kafofin watsa labarun yadda ya kamata wajen yada bayanai kan manufofi...
    Ɗaliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) na shekarar 2025 da Hukumar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta gudanar sun buƙaci a soke sakamakon ɗungurungum. Ɗaliban sun bayyana haka ne bayan da Hukumar JAMB ta amsa laifin kurakurai da aka samu da suka haifar da yawan rashin ƙoƙarin ɗalibai a jarabawar. Rashin kyawun sakamakon jarabawar, wadda sama da ɗalibai miliyan 1.5 suka kasa samun mako 200 ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya. A yayin da wasu suka ɗora laifin a kan matsalar na’ura, wasu kuma sun zargi rashin kyakkyawan shiri da kuma rashin iya kula da lokaci daga ɓanagaren dalibai. NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai A Jarabawa JAMB ta ɗauki alhakin faɗuwar ɗalibai...