Gwamnatin Jihar Kano ta cika alƙawarin da ta ɗauka ga al’ummar ƙauyen Gadan, ƙaramar hukumar Gezawa, inda aka kona masallata a lokacin Sallar Asuba.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren Litinin, yana mai cewa gwamnati ta amince da kashe Naira miliyan 151,863,895.

97 domin gudanar da muhimman ayyukan ci gaba a garin.

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kona Masallata A Kano Yadda Rikici Ya Yi Sanadin Kashe DPO A Kano

Ayyukan sun haɗa da gyara da faɗaɗan masallacin da aka ƙona masallatan a ciki, da ginin sabuwar makarantar Islamiyya da ofishin malamai, da gyaran banɗakuna guda shida, da kuma aikin famfon tuka-tuka mai amfani da hasken rana tare da ƙarin tanki a sama.

Al’ummar ƙauyen Gadan sun bayyana matuƙar farin cikinsu da wannan ci gaba, inda suka bayyana cewa irin wannan cika alƙawarin na nuna shugabanci nagari da kishin jama’a.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa
  • Amurka Ta Rage Wa’adin Bizar ‘Yan Nijeriya Zuwa Wata Uku
  • An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba
  • An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano
  • Babban Kwamandan Sojin Iran Ya Bayyana Cewa Iran Ta Koyawa Gwamnatin Isra’ila Hankali
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutum 22 Kan Zargin Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato
  • Sojoji Sun Kai Hari Maɓoyar Boko Haram A Borno, Sun Kashe Wasu ‘Yan Ta’adda
  • Trump Ya Kakabawa Wata Jami’in MDD Takunkumi Bayan Ta Fallasa Laifukan HKI Da Hannun Amurka A Ciki
  • Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza
  • Hukumar Kiyaye Hadura Ta Kasa Za Ta Aiki Da ‘Yan Jarida A Kano