‘Yansanda Sun Nemi A Kwantar Da Hankula Bayan Fashewar Wani Abu A Abuja
Published: 27th, May 2025 GMT
Rundunar ‘yansanda ta fara gudanar da bincike kan fashewar wani abu a mashigar babban birnin tarayya Abuja a kan hanyar Mararaba zuwa Nyanya a ranar Litinin. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu rahoton kiran gaggawa a ranar 26 ga watan Mayun 2025 da misalin karfe 2:50 na rana, dangane da fashewar wani abu a kan hanyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin
Ban da haka, bayan da aka tsara “shirin shekaru 5”, yana da muhimmanci a aiwatar da shi. A kasar Sin, bayan da aka gabatar da wani “shiri na shekaru 5”, dole ne a aiwatar da shi yadda ake bukata. Kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar za su tsara salon aiwatar da dukkan ayyuka, da raba su ga sassa da yankuna daban-daban, don a aiwatar da su a matakai daban daban. Bayan haka, hukumomi daban daban su kan gudanar da ayyukan sa ido a tsakiyar wa’adin shirin, kuma za a tantance ainihin sakamakon da aka samu bayan karewar shirin.
Ta wadannan halayen musamman, za a iya ganin abubuwan da za su tabbatar da aiwatar da shirin na raya kasa: Na farko, kokarin kare muhimman muradun jama’a, da tabbatar da yanke shawara ta wata hanya mai dacewa, kuma bisa tsarin dimokuradiyya. Na biyu, yin amfani da tsare-tsaren shari’a wajen tabbatar da ingancin shirin da aka tsara, da mai da shi karkashin sa ido da aka yi masa. Na uku, tun daga gwamnatin tsakiya zuwa kananan hukumomi, dole ne a aiwatar da shirin raya kasa a tsanake, domin tabbatar da cimma burin da aka sanya a gaba. A cikin wadannan abubuwa, ana iya ganin ruhin dimokuradiyya da bin doka da oda, da kuma yanayin aiki na mai da hankali, da nuna sanin ya kamata, wadanda suka kasance tushen ci gaban kasar Sin.
A cewar mista Peterside, ta hanyar koyi da fasahohin kasar Sin, Najeriya za ta iya cin gajiyar dimbin albarkatun kasa da take da su, don tabbatar da cikar burinta na raya tattalin arziki. Ni ma na yi imanin cewa, Najeriya za ta iya yin hakan, tare da samun biyan bukata. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp