‘Yansanda Sun Gurfanar Da Lauya A Abuja A Kotu Bisa Tuhumarsa Da Aikata Sojan Gona
Published: 31st, May 2025 GMT
Wadanda ake zaton mawallafin wasikar sun yi jayayya cewa ya kamata a janye tuhumar da ake yi wa Giwa saboda “adalci, daidaito, da aiki mai kyau.”
Giwa, tare da mai kula da kadarorin Cecil Osakwe da sauran su, za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume guda tara da suka hada da fitar da mutane ba bisa ka’ida ba, cin zarafi, barazana ga rayuwa, da barnar dukiya da suka kai Naira miliyan 300.
Laifukan da ake tuhumar Giwa da Bukola sun hada da hada baki wajen aikata jabun takardu da aikata laifuka (wanda za a hukunta shi a karkashin sashe na 97 na dokar Penal Code Act, 2004), da rashin gaskiya da aiwatar da takardar damfara (Sashe na 364), da kuma yin karya ga wani lauya (Sashe na 179).
Shari’ar da ta kunshi zarge-zargen da ake yi wa sana’a, Rabi’u U. Usman Esk., na sashin shari’a/masu gabatar da kara da ke karkashin ikon babban sufeton ‘yansanda ne ke gurfanar da shi.
A zaman da aka shirya yi a ranar litinin, karar ta zo gaban mai shari’a Jude Onwuegbuzie na babbar kotun Babban Birnin Tarayya Abuja a Apo. Sai dai kuma an dakatar da shari’ar saboda rashin halartar dukkan wadanda ake tuhuma.
Lauyan masu gabatar da kara J.K. Kolawole ya bayyana a madadin Sufeto Janar na ‘yansanda, yayin da U.J. Udo ya wakilci wadanda ake tuhuma.
Da yake jawabi a kotun, Udo ya sanar da mai shari’a Onwuegbuzie cewa wanda ake kara na farko, Victor Giwa, ba ya nan ya tafi kauyensu domin yi masa jana’izar ‘yar uwarsa. Don haka ya bukaci a dage zaman.
Mai shari’a Onwuegbuzie ya amince da bukatar sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Satumba 2025 domin gurfanar da shi a gaban kuliya. Alkalin, ya yi gargadin cewa ba za a sake yin wani uzuri a zama na gaba ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yansanda
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai October 30, 2025
Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda October 30, 2025
Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025