Leadership News Hausa:
2025-07-25@14:07:57 GMT

Nau’ikan Amfanin Gona Da Ke Saurin Girma Cikin ‘Yan Watanni

Published: 31st, May 2025 GMT

Nau’ikan Amfanin Gona Da Ke Saurin Girma Cikin ‘Yan Watanni

Akasari kafin a girbe ta, tana kaiwa kwanaki 60 zuwa 100 bayan an shuka ta. Kazalika, cikin sauki ake mallakar gonar da ake shuka Masara a Nijeriya, ana kuma shuka Irinta sannan a sayar da ita ga makwabta.

Dankali: Dankali na dauke da sinadarin ‘calories’ dan kadan, sannan mutane da dama na kasar nan na sarrafa shi a matayin abinci tare da yin amfani da shi.

Yana daukar watanni biyu zuwa uku bayan an shuka shi. Bugu da kari, ana iya shuka shi a kowacce irin kasar noma.

Tumatir: Ana matukar amfani da tumatir a Nijeriya, ko danyensa ko kuma busasshe. Yana dauke da sanadarin ‘bitamin C’, yana kuma taimakawa wajen rage kamuwa da cututtuka kamar wadanda ke yi wa zuciya illa, ciwon siga da kuma cutar daji.

Ana son a shuka Irinsa a kasar noma mai kyau tare da yi masa ban ruwa. Bayan an shuka Irin nasa, ana fara girbe shi daga watanni 2 zuwa 3, ya danganta da nau’in Irin da aka yi amfani da shi wajen shukawa.

Kankana: Duk yayin da aka shuka Irin Kankana, cikin dan gajeren lokaci ake girbe ta. A Nijeriya, daga wata 3 ake fara girbe ta, sannan ana iya shuka Irinta a kowanne bangare na fadin wannan kasa. Wakazalika, kankana na dauke da sinadarin ‘bitamin A’ da kuma ‘bitamin C’ mai yawan gaske.

Tattasai: Bayan shuka Irin tattasai, ana girbe shi cikin watanni uku kacal. Kazalika, ana iya cewa kusan kowane gida a fadin Nijeriya na yin amfani da shi. Ana kuma sayar da tattasai a kasuwanni da dama a wannan kasa, sannan wadanda ke yin sana’arsa na matukar samun rufin asiri ko kudaden shiga. Hatta a bayan dakin gidanka, za ka iya shuka Irin Tattasai ya girma ya kuma bayar da abin da ake so.

8. Kokumba: Kokumba na daya daga cikin sanannin kayan marmari ko lambu, ana kuma yin noman sa a wurare da dama na fadin Nijeriya. Wasu na cin sa tsurarsa, domin alfanun da yake da shi musamman a fannin kiwon lafiya. A duk lokacin da aka shuka Irinsa yana da matukar saurin yin girma, ana kuma girbe shi bayan akalla watanni 3. Sannan yana da saurin tafiya a kasuwa, ma’ana mutane suna son sa kwarai da gaske sakamakon amfaninsa ga lafiyar dan Adam.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza

Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin.

Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.” Motocin suna dauke da kayan abinci, ruwa da magani a cikin kasashen Jordan da Masar.

 A wani bayani da ofishin gwamnatin Gaza ya fitar a yau Alhamis, a cikin yankin Gaza duk wani abinci, ruwa da magani duk sun kare, don haka a halin yankin yankin yana da bukatuwa da buhunan filawa 500,000 a kowane mako.

 An shiga kwanaki 145 da HKI ta rufe dukkanin mashigar Gaza, da hana shigar da madarar jarirai da dukkanin kayan agaji.

Bugu da kari ofishin gwamnatin Gaza din ya kuma kara da cewa; Da akwai wasu kafofi da suke watsa jita-jita da karairayi akan shigar da kayan abinci zuwa cikin yankin na Gaza, yana mai cewa babu kamshin gaskiya a ciki.

Haka nan kuma ya yi kira ga mutanen Gaza da kar su yarda da wadannan irin karairayin, wacce manufarta rufe hakikanin laifukan da ‘yan sahayoniya suke aikatawa.

Har ila yau, ofishin na gwamnatin Gaza ya bukaci ganin dukkanin kasashen duniya ba tare da togiya ba, da su yunkura domin karya killace Gaza da aka yi, da kuma bude kan iyakoki saboda a shigar da madarar da kananan yara za su sha, da kuma abincin da mutane fiye da miliyan 2.4 za su ci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar ‘Yansanda Ta Yi Wa Wasu Manyan Jami’anta Karin Girma
  • Iran: Iran Tana Cikin Kasashe Biyar Na Duniya Da Suka Ci Gaba Wajen Kiwon Dabbobi
  • Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza
  • NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum
  • A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
  • Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi
  • Babban Hafsan Sojin Iran Ya Ce: Iran Zata Sanya Duk Wanda Ya Dauki Matakin Wuce Gona Kanta Nadama
  • Ɗan Shekaru 15 Ya Kashe Wani Matashi Kan Rikicin Gona A Jigawa
  •  Netanyahu: Ba Za Mu Daina Yakin Gaza Ba
  • Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC