An kama mutum 41 da ake zargi da kisan DPO a Kano
Published: 30th, May 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce, ta kama mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan DPO ɗin Rano, CSP Baba Ali.
Rundunar ta bayyana lamarin, wanda ya janyo kace-nace, a matsayin harin kai tsaye kan sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi, waɗanda suke sadaukar rayuwarsu domin kare al’umma.
NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 NDLEA ta kama maniyyata aikin hajji ɗauke da hodar iblisA wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Alhamis, ya ce rundunar ’yan sanda na aiki tuƙuru domin ganin an gurfanar da duk waɗanda ke da hannu wajen kisan, da kuma masu alaƙa da ƙone-ƙone.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rundunar ta bayyana kaɗuwarta da alhini dangane da kisan gillar da aka yi wa CSP Baba Ali a lokacin da yake bakin aiki, wannan kashe-kashen na rashin hankali babban hari ne ga al’ummarmu.”
Kiyawa ya ce Kwamishinan ’yan sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori ya tabbatar wa mazauna Jihar Kano cewa, rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, kuma babu wani abin da za a bari wajen ganin an hukunta waɗanda suke da alaƙa da kisan jami’in.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Kwamishinan ya sake nanata cewa ’yan sanda ba za su ƙasa a gwiwa ba har sai an hukunta duk wanda ke da alaƙa da wannan ɗanyen aiki.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda DPO ɗin Rano
এছাড়াও পড়ুন:
Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
Har ila yau, Lin ya ce matsayin kasar Sin dangane da rikicin kasar Ukraine bai sauya ba, cewa tattaunawa, da gudanar da shawarwari ne kadai hanyoyi mafiya dacewa na warware rikicin. Har kullum Sin na kan turbar adalci game da rikicin, tana kuma ci gaba da ingiza bukatar komawa teburin shawara tun barkewar rikicin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp