Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Batun Dakatar Da Sarrafa Uranium Ba
Published: 27th, May 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta daina sarrafa sinadarin Uranium a kowane hali ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya tabbatar a wata hira da tashar CNN ta Amurka cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da hakkinta na tace sinadarin Uranium a kowane hali ba.
A yayin da yake mayar da martani game da kyakkyawan fata na shugaban Amurka Donald Trump game da shawarwarin nukiliyar da aka yi tsakanin gwamnatinsa da Iran da kuma yadda yake kallon ci gaban da aka cimma, Baqa’i ya ce: Idan manufar Amurka ita ce tabbatar da cewa shirin makamashin nukiliyar Iran ba zata yi amfani da shi wajen karfin soji ba, to yana ganin za a iya cimma hakan cikin sauki. To amma idan har Amurka tana son tauye wa Iraniyawa ‘yancinsu na samun cikakken fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya da lumana ne, to yana ganin hakan zai zama babbar matsala, ta yadda Iran za ta kalubalanci dukkan tsarin.
A lokacin da wakilin tashar CNN ya tambaye shi: Shin ko suna tsammanin gwamnatin Trump da mai shiga tsakaninta, Witkoff, sun gane kuma sun fahimci hakan? Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya mayar da martani da cewa: Kasancewar Iran tana ci gaba da tattaunawa ya zuwa yanzu tana nufin cewa ta san akwai wani matakin fahimtar da Iran ba za ta iya ba a kowane irin yanayi ta yi watsi da haƙƙinta na mallakar fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya da lumana da suka haɗa da inganta sinadarin Uranium.
Amurka
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA
Wata kotu da ke birnin Madrid ta yi watsi da ƙarar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Turai UEFA, LaLiga da Hukumar Kwallon Kafa ta Sipaniya suka shigar kan ƙin amincewa da gasar Super League.
Wannan yana nufin yanzu Real Madrid da sauran ƙungiyyoyin za su iya neman diyyar kudi Euro Milyan 4.
Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar Christopher MusaReal Madrid ta ce, wannan hukuncin ya tabbatar da cewa UEFA ta karya dokokin gasa, kuma ƙungiyyoyi sun rasa maƙuden kuɗaɗe tun daga lokacin da aka dakatar da gasar.
Gasar wacce aka shirya farawa a shekarar 2021 tare da manyan ƙungiyoyin Turai, an yi hasashen zata samar da kusan Yuro miliyan 200 ga ƙungiyoyin da suka shiga.
A nata martanin hukumar UEFA ta dage cewa wannan sabon hukuncin ba ya nufin an dawo ko an amince da a buga gasar Super League ba ne.