Kasar Uganda ta dakatar da aikin hadin giuwa na soje dake tsakanin kasashen biyu, saboda sukan da jakadan kasar Jamus yayiwa dan shugaban kasar yake kuma goyon bayan wata jam’iyyar adawar kasar.

Shafin yanar gizo na labarai Afirka News ya nakalto jami’iyyar shugaban kasar Uganda People’s Defence Forces (UPDF) tana bada rahoton cewa Jakada Schauer na kasar Jamus a Kamfani ya halarci wata taro tare da wata jam’iyyar adawa inda yake sukar dan shugaba Uwere Musevene jan yadda jam’iyyarsu take gudanar da harkokin shugabancin kasar.

Kasashen Uganda da Jamus sun dade basu sami irin wannan rashin jituwa ba. Kuma harkokon kasuwanci tsakanin kasashen biyu yakai dalar Amurka miliyon $335 a shekara 2023 kadai.

Sai dai muna iya cewa wannan ba zo da mamaki ba saboda shugaban yana shirin sake tsayawa takara a shekara 2026 mai zuwa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan

Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan.

Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka.

Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump

Ministan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin “mummunan bala’i,” yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tattara ne a Sudan ɗin.

A taron da aka gudanar a Bahrain, ƙasashen Birtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo ƙarshen tashin hankalin.

A ƙarshen makon da ya gabata, RSF ta kori rundunar soji daga sansanin ta na ƙarshe a yammacin Darfur.

Rahotanni daga garin El-Fasher sun bayyana cewa ana samun kashe-kashe ba tare da shari’a ba, da fyaɗe da fashi har ma da hare-hare kan ma’aikatan agaji.

Wata Kungiyar Likitoci ta MSF a ranar Asabar ta ce ana fargabar dubban fararen hula sun maƙale sannan suna cikin mummunan haɗari a birnin Al Fasher wanda ya koma hannun dakarun RSF.

Rikicin Sudan ya fara ne a watan Afrilun 2023, bayan taƙaddama ta siyasa tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban sojin ƙasar, da Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti), Kwamandan RSF.

Bayanai sun ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan yadda za a haɗa rundunar RSF da sojojin ƙasar bayan juyin mulkin 2021 da ya hamɓarar da gwamnatin farar hula.

Tun daga lokacin, yaƙin ya zama wani mummunan bala’i na jin kai, inda Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ce fiye da mutane miliyan bakwai sun tsere daga gidajensu, yayin da dubbai ke buƙatar taimakon gaggawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu
  • Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
  • MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar