2025-08-16@08:25:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2626

«madara»:

    Rundunar sojan Mali ta sanar da kame wasu manyan hafsoshin sojin Mali guda biyu, dan kasar Faransa, da wasu mutane da dama da ake zargi da yunkurin tayar da zaune tsaye a kasar ta hanyar yunkurin juyin mulki, wanda kuma aka yi nasarar dakile shi. Ministan tsaron kasar Janar Daouda Aly Mohammedine ne ya bayyana...
    Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari, yace ziyarar kwamatin a kananan hukumomin jihar 27 tana bada damar ganawa kai tsaye a tsakanin masu ruwa da tsaki domin karfafa dabi’ar aiki tare da juna da kuma kyautata alaka a tsakanin bangarori daban daban. Ya yi wannan tsokaci ne lokacin da...
    “Sama da yara miliyan 10.1 ne ba su kai makaranta, kashi 70 masu zuwa makarantar kuma ba su da dabarun koyo, kuma fiye da kashi 60 na malaman firamare na gwamnati ba su da ilimin dijital,” in ji ta Da take yaba wa gwamnatin Koriya ta Arewa bisa tallafin da ta samu ta hannun hukumar...
    Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% da aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin...
    Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce matsalar tsaro na iya hana ta gudanar da aikin rijistar masu zabe a kananan hukumomin jihar Borno guda hudu. Kananan hukumomin da lamarin zai iya shafa su ne Abadam, Guzamala, Marte da Kala-Balge. Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauyen jagoranci a Hukumar Talabijin ta ƙasa (NTA), inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro a matsayin sabon Darakta-Janar. Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Karimah Bello a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Tallace-Tallace, Stella Din a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Labarai, da Sophia Essahmed a matsayin Manajing Darakta...
    A cikin jahohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa a jerin sunayen, inda take da garuruwa kusan 10 da suka hada da Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi. Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadin samun ambaliyar ruwa ga jihohi 15 daga cikin 19 na Arewa....
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Suna buƙatar kawar da makaman nukiliya da kuma kawo ƙarshen maganganun rashin jin daɗi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan kawar da makaman nukiliya da kuma amincewa da laifukan tarihi a hukumance kamar harin bam din da...
    Laifukan da ake gudanarwa a gabar tekun Siriya: Cin zarafin ya kai ga laifukan yaki! Rahotonni sun bayyana cewa; Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Siriya ya fitar ya ce: Rikicin kabilanci da ya faru a gabar tekun Siriya ya kunshi cin zarafi da ya kai ga laifukan yaki. Rahoton ya kara da cewa; Rikicin...
    Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta sanar da cewa: Mutane 40 ne suka mutu a Sudan sakamakon barkewar cutar kwalara mafi muni cikin shekaru Kungiyar likitocin ba da agaji ta “Doctors Without Borders” ta sanar da mutuwar mutane 40 sakamakon kamuwa da cutar kwalara a Sudan cikin mako guda kacal, tare da tabbatar da...
    Jami’an kwana-kwana a birnin London na kasar Burtaniya sun bukaci marasa lafiya da likitoci da sauran masu aikin a asbitin Guy da su fice daga asbitin saboda hatsarin samuwar wasu sinadarai masu cutarwa a cikinsa. Jaridar da Nation ta kasar Amurka ta bayyana cewa , da masalin karfe 8.49 ne aka shaidawa jami’an kwana-kwana batun...
    Gwamnatin kasar Afirka ta kudu zata fara tattaunawar kasa dangane da talauci da kuma rashin adalci a rabon arziki a kasar. Gwamnatin kasar ta ware kimani dalar Amurka miliyon 40$ don gudanar da tattaunawar. Inda ake saran dukkan mutanen Afrika ta kudu suna da damar bayyana ra’ayinsu dangane da wadannan matsaloli. Na talauci da rashin...
      Ya kara da cewa, kasar Sin tana kira ga kasa da kasa su ci gaba da tallafa wa ayyukan UNRWA, yana mai cewa a shirye Sin take ta yi abun da zai kawo karshen rikicin da samar da mafita mai adalci da dorewa bisa manufar kafa kasashe biyu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga...
    “Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya. “Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar...
    Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ), ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewar ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji, ya miƙa wuya ba gaskiya ba ne. Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis yayin bayani kan ayyukan sojoji. Rashin Lantarki: Babu...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya Bayyana cewa: Shugabannin gwamnatin nuna wariyar al’umma suna kokarin yaudarar al’ummar Iran A martaninsa ga fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ya yi a baya-bayan nan, shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Kasar Iran a yayin da yake gabatar da wasu takardu kan matsalar karancin ruwa da kuma matsalar...
      Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ya kuma nuna cewa, kaso 92 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na bayyana matukar damuwa game da tsaron rayukan al’ummun Amurka, yayin da kaso 81.7 bisa dari suka ce muggan laifuka, da karuwar masu kwana a kan tituna sun zamewa manyan biranen Amurka alakakai, lamarin da ya zamo...
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani tsohon malami kuma manomi, Andrew Imuekheme, a Jihar Edo. Lamarin ya faru ne a ranar Talata a garin Ikabigbo, da ke Masarautar Uzairue, a Ƙaramar Hukumar Etsako ta Yamma. Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da kara wayar da kan direbobi da fasinjoji da Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta ce tana yi, ana kara samun ƙaruwar wadanda ke rasa rayukansu sakamakon hadura a titunan kasar nan. A shafinta na internet, FRSC ta ce a watanni uku na farkon 2024, mutane...
    Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su. Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar...
    A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu tare da tabbatar wa al’ummar yankin ƙudurinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.   A nasa jawabin, gwamnan ya yi kakkausar suka ga hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa a baya-bayan nan, yana mai cewa da gangan maƙiya ke nufin...
    Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa a duk faɗin Nijeriya. Dakatarwar ta shafi ƙirƙirar sabbin jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na tarayya kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta tabbatar. Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 An naɗa...
    Tinubu ya yi kira da a sake duba kudaden gudanar da aikin NNPC da ake cire kashi 30 cikin 100 wanda doka ta tanadar a karkashin dokar masana’antar mai.   Shugaban ya bayyana godiya ga mambobin majalisar bisa jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da wahala wadanda suka dabaibaye ci gaban...
    Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran wato (AEOI) Muhammad Eslami ya bayyana cewa babu jada bayana a shirin nukliyar kasar iran, duk tare da takurawar kasashen yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Eslami yana fadar haka a wani taro nay an jarida a nan Tehran a jiya Talata. Ya kuma...
    Alausa ya ce dakatarwar, wacce ta shafi dukkan nau’o’in manyan makarantun gwamnatin tarayya an yi hakan ne da nufin dakatar da maimaici da barnatar da dukiyar gwamnati, inda za a yi amfani da kudin domin inganta makarantun da ake da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
    Wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi wa shugaban sun hada da kara farashin kudin takin gwamnati daga ₦20,000 zuwa ₦22,000 kan kowane buhu; hada rikici tsakanin shugabannin Siyasar yankin; raba kan Kansilolin karamar hukumar; tsunduma cikin harkokin siyasa masu raba kan jama’a ta hanyar bayar da dukiyar gwamnati ga abokan siyasarsa kawai; da dai...
    Ƙungiyar Ci Gaban Masarautar Jama’a (JEDA), ta roƙi Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da ya kammala manyan titunan Birnin Kafanchan, wanda aikin ya tsaya tun zamanin Nasir El-Rufai. Muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Ahmad Usman Husain, ya ce waɗannan tituna na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki da rayuwar yau da kullum a Kudancin Kaduna. Majalisar Kano...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Alhaji Muhammad Naziru Ya’u, na tsawon watanni uku sakamakon zarge-zargen aikata ba daidai ba. An yanke wannan hukunci ne a zauren majalisa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan kwamitin majalisar kan ƙorafe-ƙorafe ya gabatar da rahoton bincikensa. Yayin gabatar da rahoton,...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta dakatar da Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon wata uku domin gudanar da bincike kan zargin yin amfani da kujerarsa ba bisa ƙa’ida ba. Kansilolinsa sun zarge shi da karkatar da kayayyaki da kuma almundahana wajen tafiyar da dukiyar jama’a. Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini...
    An yi kira ga kwararrun kafafen yada labarai da su tabbatar da madogararsu domin tabbatar da samar da kyakykyawan rahoton abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.   Babban Limamin Masallacin Al-Waheed Central, Imam Mustapha Luqman ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida...
    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da kyakkyawar alaka da kafafen yada labarai.   Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, da ‘yan majalisar zartaswar NUJ na kasa (NEC) da suka je Kano domin...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Jami’ar Jihar Taraba Jalingo, ta bayar da wa’adin makonni biyu ga gwamna Agbu Kefas da shugabannin jami’ar da su gana da ita ko kuma ta shiga yajin aikin.   A cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron majalisar da aka gudanar a ranar 7 ga wata. Agusta 2025,...
    Biyo bayan wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fitar na cewa sama da likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya a cikin shekaru bakwai da suka gabata domin neman aiki a wasu kasashe, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na cike gurbin da likitocin suka haifar.   Da yake zantawa da manema...
    Majalisar Dokokin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Bashar Aliyu Gummi, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hada kai da ayyukan tsaro a Jihar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kamar yadda babi na biyu na kundin tsarin mulki ya tanada.   A zaman taron na ranar Talata, mambobin sun yi zargin cewa, ‘yan bindiga...
    Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Talata cewa: Sun kai farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda shida, inda suka kai hari kan wasu muhimman wurare...
    An ce ya amsa cewa an aikata fashi da makami sau biyu da shi, kuma yanzu hakan ana shari’arsu a kotun jihar Gombe. An miƙa shi tare da kayan da aka gano ga Sashen Yaƙi da Tashin Hankali domin ƙara gudanar da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu. Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo...
    Nijeriya da Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni daban-daban, kamar batun yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma bayar da horo na musamman ga jami’an tsaron Nigeria. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da...
    Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani matashi mai shekaru 18, Hassan Aminu Sadiq, bisa zargin aikata fashi da makami a lokuta daban-daban, bayan wani samame da aka kai unguwar unguwar Yelwa da ke garin Kwadon a Karamar Hukumar Yemaltu Deba. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama wanda...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya...
    Gwamnatin jihar Kano ta gana da shugabannin ‘yan bangar siyasa da suka tuba a jihar tare da yi musu alkawarin tallafa musu ta hanyar sauya tunaninsu da horar da su sana’o’i da kuma kayan aikin fara sana’ar. Taron wanda ya gudana a ranar Talata a Kano ya samu halartar tubabbun ‘yan barandan siyasa da masu...
    Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da...
    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta tsawaita dakatar da harajin da ya ƙaƙaba wa ƙasar China na tsawon kwanaki 90. Trump ya sanar da hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, sa’o’i kaɗan kafin wa’adin farko...
    Hukumomin Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya sun ufe makarantar a sakamakon zanga-zangar da dalibai suka gudanar domin nuna fushinsu kan harin da ’yan fashi suka kai dakunan kwanansu. Daliban sun tayar da tarzoma ne da sanyin safiyar Talata bayan harin ’yan fashin ya ya yi sanadiyyar jikkatar wasu dalaibai da dama, suna mazu...
    Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya ba da shawarar gudanar da taron kasashen Larabawan yankin tekun Pasha da Iraki da kuma Iran Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussein ya gabatar da shawarar gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Iraki, Iran, da kuma kasashen larabawan yankin Gulf, a tsarin na 6+2, a gefen taron...
    Kasar Italiya ta janye jirgin ruwanta daga tekun Bahar Maliya bayan gazawarta a fage kwamawa da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Kasashen Turai sun ci gaba da janye jiragen ruwa da jiragen yaki daga tekun Bahar Maliya, lamarin da ke tabbatar da hukuncin da kasashen nahiyar suka dauka na cewa ci gaba da zamansu a...
    Rijistaran makarantar, Alhaji Kasimu Salihu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an rufe makaranta kuma an umarci ɗalibai su bar harabar makarantar har sai an bayar da sanarwa ta gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi karin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tantancewa.   Bukatar, wacce aka mika ta wata wasika daga bangaren zartarwa, ta nemi amincewar majalisar ta kara kasafin kudi naira biliyan 169,522,463,294.82 domin daukar muhimman ayyukan raya kasa a fadin jihar.   Kakakin majalisar Alhaji...