Sojoji sun kashe ɗan ta’adda da aka sa ladar N100m a kansa a Bor
Published: 31st, May 2025 GMT
Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wani kwamandan ’yan ta’adda, Amir Abu Fatima da aka sanya ladar Naira miliyan 100 ga duk wanda ya kama shi ko ya tona asirin inda yake, aka kama shi.
Sojoji sun halaka Abu Fatima ne a wani samame na musamman da suka kai a yankin Arewacin Jihar Borno.
Majiyar leken asiri ta sanar da Zagazola Makama cewa an kai harin ne da sanyin safiyar Juma’a, a yankin Kukawa da ke yankin Tafkin Chadi.
Majiyoyin soji sun tabbatarwa da Zagazola Makama cewa, wannan aikin wani shiri ne da aka tsara a tsanake na halaka ‘yan ta’adda da nufin kashe Abu Fatima, wani babban jigo na ‘yan tada kayar baya.
Dakaru na musamman sun kutsa cikin yankin da ‘yan ta’addan suke inda suka yi artabu da su a wani kazamin musayar wuta.
Abu Fatima ya samu munanan raunuka yayin arangamar kuma an kama shi da rai sai dai daga bisani ya mutu sakamakon zubar da jini da ya wuce kima sakamakon harbin bindiga da ya samu a yakin.
Majiyarmu ta bayyana cewa an kashe babban kwamandan sa na biyu, masu hada bama-bamai, da wasu mayaka da dama a samamen.
Kayayyakin da aka ƙwato daga farmakin sun hada da bindigogi kirar AK-47 da dama, da akwatunan harsasai masu yawa, da kayan ƙera bama-bamai, da sauran kayan yaƙi.
Abu Fatima dai ya kasance cikin jerin sunayen da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo saboda hannu a hare-haren ta’addanci da dama a yankin Tafkin Chadi.
Ana kallon mutuwarsa a matsayin wani babban koma baya na aiki da tunani ga cibiyoyin ’yan ta’adda da ke aiki a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800.
Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin NajeriyaJami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta.
Ya ce, “Binciken farko ya nuna cewa Iluyemi Bosede ta je wurin yayar tata, Tewogboye Omowumi mai shekaru 35, domin karbar bashinta na N800 na kudin tumatir da barkono. Sai dai tankiyar da ta fara a matsayin ƙaramin sabani ta rikide zuwa tashin hankali, inda ake zargin Bosede ta riƙe kayan marigayiyar har ta faɗi ƙasa.”
“Abin takaici, duk da an garzaya da marigayiyar asibiti don samun kulawar gaggawa, likitoci sun tabbatar da mutuwarta tun kafin a fara ba ta taimako. Wannan lamari ya nuna yadda ƙaramin sabani zai iya rikidewa zuwa mummunar husuma idan ba a magance shi cikin lumana ba.”
Bayan faruwar lamarin, rundunar ta ce ta kama wadda ake zargi kuma tana tsare da ita a halin yanzu, yayin da bincike ke ci gaba.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, domin ta girbi abin da ta shuka.