2025-11-13@14:43:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11520

«da ake zargin»:

    Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa da taron NIQS karo na 31 da kuma babban taron cibiyar na kasa. Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle Nzekwe, wanda ya bayyana cewa, Cibiyarsa tana bai wa gwamnati shawarwari amma ya nanata cewa, alhakin gwamnati ne ta ɗauki mataki da kuma daidaita kuɗin...
    1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo  Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari a gaba. Ko da yake ƙungiyar sau da yawa tana saumn rinjayan samun kwallo da kirkirar damar kai hari, amma kash suna gaza amfani da waɗannan damarmaki zuwa nasara. Wanda hakan yake nuna rashin ‘yan wasa masu ƙwarewa da zasu ci kwallon, wanda ya sa ake dogaro da wanda suka kwana biyu kamar Rabiu Ali, yana iya kokarinsa amma ba aikinsa ba ne kuma tsufa...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwan nan da ya samu takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kyautar sabuwar mota kirar Toyota SUV. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa na X a ranar Alhamis, Atiku ya bayyana labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya tsagwaronta ba tare da wata hujja ba. An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal Ibe ya bukaci jama’a da su yi watsi da wannan labari da...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bai wa Laftanar Ahmed Yerima, sojan ruwan nan da ya samu takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kyautar sabuwar mota kirar Toyota SUV. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafinsa na X a ranar Alhamis, Atiku ya bayyana labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya tsagwaronta ba tare da wata hujja ba. An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal Ibe ya bukaci jama’a da su yi watsi da wannan labari da...
    A jiya Laraba ne aka bude shari’ar tsohon madugun ‘yan tawayen kasar DRC Roger Lombala a kasar Faransa bisa tuhumar da ake yi masa da aikata laifuka akan bil’adama a yayin yakin DRC na biyu. Ana kuma tsammanin cewa wannan shari’ar za ta dauki wata daya ana yinta. A yayin zaman shari’ar za a gabatar da shaidu daga wadanda su ka cutu sanadiyyar ayyukan kungiyar ‘yan tawayen wacce Lombala ya jagoranta. Wannan shi ne karon farko da za a yi wa dan kasar DRC shari’a a kasar Faransa bisa ka’idar hurumin shari’a na duniya. Ofishin Fada Da Laifuka Aka Bil’adama ( OCLCH)  ya kama Lombala ne a ranar 29 ga watan Disamba 2020 a birnin Paris. An kuma gabatar da...
    Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta fitar da wani rahoto da shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya fitar da a ciki yake tabbatar da cewa, Iran tana aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Rahoton dai ya kunshi cewa, tun bayan yarjejeniyar birnin Alkahira na kasar Masar da aka yi a tsakanin ministan harkokin wajen Iran da kuma shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa Refael Grossy, Iran din ta yi aiki da dukkanin nauyin da ya rataya a wuyanta. Grossi ya rubutawa Iran wasika a ranar 7 ga watan Nuwamba na 2025 yana mai cewa; Bayar da dama ga hukumar domin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin Iran, yana...
    Janar Fadwi wanda shi ne mataimakin kwamndan dakarun kare juyin musulunci na Iran ya ce; Muna aiki akan nisan Zangon da makamanmu masu linzmai za su iya kai wa gare shi. Fadwi wanda ya gabatar da jawabi a yau Alhamis a wurin taron girmama shahidan rundunar dake kula da kare sararin samaniyar Iran, ya kara da cewa; Babu iyaka ko haddi akan aikin da Iran din take yi a fagen kare sararin samaniyarta da kuma samun karfi. Dangane da batun da makiya suke yi na rage tsawon Zangon da makamai masu linzami za su ci, Fadwi ya ce; Wasu suna yin Magana akan abinda bai shafe su ba, kuma ba su da wata masaniya akan hakan.”  Mataimakin kwamandan dakarun kare...
      “Mun yi imani cewa ‘yan wasanmu tare da kwarewar da suke da ita, zai janyo wa Nijeriya abin alfahari, ba kawai a ranar Alhamis ba, har ma a duk tsawon wasannin share fagen da zamu buga”, hakan yasa muke da kwarin gwuiwar cewar kasarmu za ta iya samun tikitin shiga gasar cin kofin Duniya,” in ji Gusau. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle November 13, 2025 Manyan Labarai Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su November 13, 2025 Manyan Labarai Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta dakatar da wani Hakimi da Dagaci a ƙaramar hukumar Funakaye bayan barkewar rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin. Rahotanni sun ce rikicin dai ya yi sanadin mutuwar ɗan sanda ɗaya tare da jikkatar wasu jami’an tsaro da dama. Gwamnatin Tarayya ta dakatar da harajin kashi 15 na shigo da fetur da dizal Yadda na yi asarar N120m a gobarar Singa — Ɗan Kasuwar Kano Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Zubairu Muhammad, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai bayan zaman kwamitin tsaro da aka gudanar ranar Laraba. Ya ce an dauki matakin dakatarwar ne domin tabbatar da doka da oda, tare da aika sakon gargaɗi ga sauran masu rike da sarautun...
    3.LukaModrić (Croatia) 4.ManuelNeuer (Jamus) 5.VirgilvanDijk (Netherlands) 6.HarryKane (Ingila) 7. RobertLewandowski (Poland) 8.SonHeung‑min (Koriya ta Kudu) 9.MohamedSalah (Masar) 10.Luis Suárez (Uruguay)   Tasirinsu a kungiyoyi da ƙasa na da matukar muhimmanci, kuma 2026 na iya zama damarsu ta ƙarshe ta haskakawa a babban kofin ƙwallon ƙafa mafi daraja.   Biyu da suka yi fice acikin 10, sun hada da Cristiano Ronaldo (Portugal). Yana da shekaru 41, ya tabbatar da cewa wannan zai zama gasarsa ta ƙarshe, yana da niyyar ƙara Kofin Duniya a cikin jerin kofunan da ya taɓa lashewa.   LionelMessi (Argentina). Bayan ya lashe gasar cin kofin duniya ta 2022, ɗan wasan mai shekaru 39 ya nuna cewa gasar 2026 a Arewacin Amurka na iya zama damarsa ta ƙarshe...
    Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aiwatar da harajin shigo da man fetur da dizal na kashi 15, wanda a baya aka amince da shi domin daidaita farashin shigo da kayayyaki da yanayin kasuwa. Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NMDPRA) ce, ta sanar da hakan a wata sanarwa da Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a, George Ene-Ita, ya sanya wa hannu. Yadda na yi asarar N120m a gobarar Singa — Ɗan Kasuwar Kano MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC Harajin ya janyo cece-kuce, inda wasu ke ganin zai kare matatun gida, yayin da wasu ke cewa hakan zai ƙara tsadar kayayyaki sannan ya tsauwala wa talakawa. “Hukumar na shawartar ’yan kasuwa da su guji ɓoyewa ko sayar...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar. Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa Cin Zarafi (SARCs) da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) a Ilorin da kuma Asibitin Kwarari ta Sobi da ke Alagbado. Kwamishiniyar ta bayyana cewa cibiyar an kafa ne tare da hadin gwiwar ofishin Uwargidar Gwamna, domin jinya kyauta da kuma kwantar da hankali, da tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafi a jihar. Afolashade ta ƙara da cewa bincike da tantancewar...
    A ci gaba da aikace-aikacen yaki da ta’addanci da laifuffuka a fadin Jihar Taraba karkashin Operation Lafiya Nakowa, sojojin Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya / Sashen 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun samu nasarar kama wani wanda ake zargin dillalin makamai, tare da kwato makamai da harsasai daga hannunsa. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Lieutenant Muhammad, Mai Rikon Mukamin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar 6, ya sanya wa hannu. A cewar sanarwar, bisa sahihan bayanan leƙen asiri da aka samu, a ranar 12 ga Nuwamba, 2025, sojojin suka kai samame a kauyen Shagada, karkashin gundumar Namnai a Karamar Hukumar Gassol, Jihar Taraba. Samamen ya haifar da kama wani mutum mai suna Abdulmudallabi Audu, mai...
    Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa hangen nesansa na ƙarfafa masana’antu a jihar shi ne domin ƙirƙirar ayyukan yi da kuma inganta rayuwar jama’ar jihar. Gwamnan ya bayyana haka ne a Fadar Gwamnati ta Lafia, yayin da yake karɓar bakuncin sabbin shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu aiko rahotann dake Jihar (Correspondents’ Chapel). Ya ce baya ga jawo ‘yan kasuwa masu saka jari a fannin masana’antu da ma’adinai, gwamnatin sa tana kuma zuba jari mai yawa a harkar noma. “Ɗaya daga cikin abubuwan da ke ba ni farin ciki shi ne harkar noman shinkafa. Ka san muna da wata ƙaramar gona mai girman hektare 3,300 domin noman shinkafa. Ina alfahari da gonar shinkafar mu domin mun fara girbi,...
    A wani sabon yunƙuri na inganta haƙƙin yara da walwalarsu, Hukumar kula da kananan yara ta MDD wato UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Wayarda kan jama’a da ta Ƙasa (NOA) da Hukumar kidayar Jama’a ta kasa (NPC), da Hukumar Kula da katin zama dan Ƙasa (NIMC), sun kaddamar da shirin wayar da kai na yini guda kan muhimmancin rijistar haihuwa ga sabbin jarirai a duk faɗin Yankin Gwarzo na Jihar Kano. Wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryen gwamnati da UNICEF ke tallafawa, domin ƙarfafa tsarin kare yara da kuma tabbatar da samun damar yin amfani da muhimman aikace-aikacen zamantakewa, musamman a yankunan karkara na jihar. Wakilin NPC, Malam Abubakar Lawal, ya jaddada muhimmancin haddin kan al’umma wajen cimma nasarar...
    Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano, Yusuf Shuaibu Imam, ya yi kira ga mazauna yankin da su ziyarci ofisoshin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin yin rijistar zaɓe da kuma karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PVC). Imam ya yi wannan kiran ne yayin da yake kaddamar da jerin ayyukan raya al’umma a mazabar Tudun Wada da Gama. Ya jaddada muhimmancin matasa, musamman waɗanda suka kai shekaru 18 a kwanan nan, da kuma waɗanda suka rasa ko katinsu ya lalace, da su tabbatar sun yi rijista domin su samu damar shiga cikin zaɓuɓɓukan da za su zo nan gaba. Shugaban karamar hukumar ya ce yin rijistar zaɓe hanya ce ta bai wa ‘yan ƙasa damar cika...
    Gidauniyar  fadakar da al’umma akan dokoki da ka’idoji ta Nijeriya ta kaddamar da kwamiti a jihar Nasarawa domin aiwatarwa da sa ido kan shirin mata, zaman lafiya da tsaro, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen gina zaman lafiya a cikin jihar. Daraktan gudanarwa na gidauniyar, Mista Peter Maduoma, ne ya bayyana hakan a Lafia yayin taron horarwa na kwanaki uku da aka shirya ga masu ruwa da tsaki kan batun mata, zaman lafiya da tsaro, wanda gidauniyar ta shirya. Mista Maduoma, wanda Jami’in Shari’a da Albarkatun Ƙasa na Gidauniyar, Mista Ifeyinwa Akwiwu, ya wakilta, ya ce shirin wani ɓangare ne na aikin gidauniyar mai taken “Ƙarfafa tsarin adalci ta hanyar kare haƙƙin ɗan adam da bunƙasa zaman lafiya a Najeriya.”...
    Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar.   Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na Ƙasa da Ƙasa na Nijeriya, Suleja, Jihar Neja; Millennium Tower, Abuja; Ginin Hukumar Haraji ta Tarayya a Jihar Abia; Hedikwatar Dakin karatu na Ƙasa, Abuja; Kamfanin Masana’antar buga Labarai na Nijeriya, Kaduna; Ginin Masaƙa ta Kaduna; da Kamfanin Narka Alluminium na Nijeriya, Jihar Delta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule...
    Ministocin harkokin wajen Iran da na Rasha sun tattauna ta  wayar tarho gabanin taron kwamitin gwamnonin IAEA A yayin tattaunawar Araghchi da Lavrov, sun yi musayar ra’ayi kan batutuwa daban-daban, ciki har da rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan, tare da jaddada muhimmancin yin shawarwari don warware batutuwan da ba su dace ba. Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya kuma jaddada bukatar tuntubar juna tsakanin Iran da Rasha da ma sauran kasashen duniya domin lalubo hanyoyin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A yayin da yake ishara da matakin da Amurka da kawayenta na Turai suka dauka a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dangane da Falasdinu, da wani daftarin kuduri na kafa rundunar kasa da kasa...
    A yammacin jiya  ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Iraki ta sanar da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar 2025, tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da inganci ta hanyar amfani da na’urorin lantarki. A taronta na manema labarai, Hukumar ta bayyana cewa yawan masu kada kuri’a ya kai kashi 56.11% bayan samun sakamako daga kashi 99.98% na rumfunan zabe. Wannan sanarwar ta zo ne sa’o’i 24 bayan kammala babban zaben da aka gudanar a wannan  Talata, da kuma zabe na musamman da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, domin zaben ‘yan majalisar dokokin Iraki na shekara ta 2025. Jimillar masu kada kuri’a sun kai 20,063,773,...
    Wani kamfanin hakar ma’adinai na Biritaniya ya sanar a jiya Laraba cewa, an gano tarin zinari a karkashin kasa a gundumar Kakamega da ke yammacin kasar Kenya, wanda darajarsa ta kai sama da dalar Amurka biliyan 5.28 kwatankwacin shilin kasar Kenya biliyan 683, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na tarihi ga fannin hakar ma’adinai na kasar. Kamfanin ShantaGold Kenya Limited ya sanar da cewa, an gano hakan ne a hanyar Lerehanda, wanda ya ratsa cikin kananan hukumomin Kakamega da Fihiga, bayan kwashe tsawon shekaru ana bincike. A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce aikin yana da nufin samun lasisin da ya dace don hakar albarkatun zinare a mahakar Isolo-Bushiangala don...
    Hamas ta tabbatar da cewa tana aiki da alƙawarinta na amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma nauyin da ke kanta na ƙasa da na jinƙai ga al’ummar Falasɗinu. Ta yi kira ga masu shiga tsakani, ƙasashe masu garantin, da kuma al’ummar duniya da su ɗauki mataki nan take da muhimmanci don tilasta wa mamaya ta dakatar da take haƙƙoƙinta, ta ɗage killacewar, ta ba da damar shigar da agaji, da kuma tabbatar da haƙƙin al’ummar Falasɗinu na tsaro, ‘yanci, da mutunci. Ƙungiyar ta buƙaci kawo ƙarshen kisan kiyashi da take haƙƙoƙin al’ummar Falasɗinu a Gaza, da bin layin janyewa na ɗan lokaci da aka amince da shi, da kuma hana duk wani ƙarin kutse ko keta haƙƙoƙi. Ta kuma...
    Gwamnan Sule ya ce irin wannan jaridar da ke kan gaba ta zaɓo shi a matsayin gwarzon gwamna, abun farin ciki ne sannan ya yaba wa kamfanin bisa tabbatar da sahihancin labarai da daidaitasu wanda hakan yasa ta bambanta ta da takwarorinta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025
    Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya guda biyu sun yi gargadi a jiya Laraba cewa, miliyoyin mutane a yankuna akalla 12 da ke fuskantar rikici a duniya, ciki har da Sudan da zirin Gaza, na fuskantar barazanar yunwa, tare da gabatar da bukatar gaggawa na samar da kudade don magance gibin tallafin abinci, sakamakon raguwar tallafin da kasashen duniya ke bayarwa. A cikin wani rahoto na hadin gwiwa, Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) da Hukumar Abinci da Aikin Noma (FAO) sun sanya kasashen Haiti, Mali, Sudan ta Kudu, da Yemen cikin kasashen da ke fuskantar barazanar yunwa. Rahoton ya kuma bayyana halin da ake ciki na yunwa a wasu kasashe shida wato Afganistan, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Myanmar, Najeriya, Somaliya, da Syria, a...
    Kungiyar Kare Muradun Musulmai (MURIC) ta bukaci a gaggauta tsige Farfesa Joash Amupitan daga shugabancin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), saboda matsayinsa kan batun rashin tsaro a Najeriya. Aminiya ta rawaito cewa, a cikin wani rubutu a baya, Amupitan wanda a lokacin malami ne a Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya ce “abu ne sananne cewa ana aikata laifuka a ƙarƙashin dokokin kasa da kasa a Najeriya, musamman laifukan da suka shafi cin zarafin bil’adama, laifukan yaki da kuma kisan kare dangi.” Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano Ya kara da cewa: “Kalma guda da hukumomin Najeriya da masu bincike na kasa da kasa...
    Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓo rancen Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025. Amincewar ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Manu Haruna, ya gabatar. Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana Super Falconets ta lashe gasar WAFU ta ’yan ƙasa da shekaru 20 Ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2025 na Naira tiriliyan 59.99 ya bar giɓin naira tiriliyan 1.15 wanda dole ne a cike ta hanyar nemo rancen a cikin gida. Sanatoci sun amince cewa rancen ya zama dole domin ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan gwamnati da tabbatar da nasarar kasafin kuɗin 2025,...
    Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar SDP da Wilson Iliya Yange na jam’iyyar PDP, da Honarabul Simon Na Allah na jam’iyyar LP, sai Ibrahim Musa na jam’iyyar ADC daga shiyya ta biyu shi ne Sakataren kwamitin.   Da yake jawabi bayan kaddamar da kwamitin, Shugaban jam’iyyar na jihar, Elder Patrick Ambut, ya shawarci mambobin da su kasance masu jajircewa tare da tabbatar da adalci da gaskiya a cikin aikin da aka...
    Kasar Sin ta bukaci Japan da ta daina yi wa masu fafutukar neman “‘Yancin kan Taiwan”, ingiza mai kantu ruwa, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Guo Jiakun ya bayyana a yau Laraba. An ruwaito cewa, gwamnatin Japan a ranar Talata ta ba da wata lambar girmamawa ga tsohon “wakilin Taiwan a Japan” Hsieh Chang-ting. A martanin da ya mayar game da hakan a wani taron manema labarai, mai magana da yawun ma’aikatar Guo Jiakun ya ce, kasar Sin tana matukar adawa da matakin gwamnatin Japan na ba da lambar girmamawa ga wadanda ke fafutukar “‘yancin kai na Taiwan” kuma yin hakan wani babban kuskure ne da bangaren Japan ke yunkurin tafkawa kan batun da ya...
    Aƙalla mutum 12 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani turmutsutsu da ya faru yayin jarabawar ɗaukar aikin soja a Filin Wasa na El-Wak da ke Accra, babban birnin ƙasar Ghana. Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da ɗaruruwan matasa masu neman aikin suka kutsa cikin filin wasan ba tare da bin tsarin shiga da aka tanada ba. An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo Rundunar Tsaron Ghana (GAF) ta ce mutum shida ne suka mutu a farko, amma rahotanni daga asibitin sojoji sun tabbatar da cewar adadin mamatan ya ƙaru zuwa mutum 12. Wasu mutum 22...
    Taron ya hada bijiman masana, da masu tsara manufofi, da masu ilimi,da masu bincike, da abokan hadin gwiwa na haɓaka harkar ilimi daga Afirka, Kudancin Asiya, da Birtaniya don tattauna dabarun inganta ilimi ta hanyar harshe.   Dr. Alausa, ya jaddada cewa, yayin da kiyaye harsunan asali har yanzu yana da mahimmanci ga al’adu, amma Turanci ya kamata ya zama babban harshen koyarwa tun daga firamare har zuwa makarantun gaba da sakandare don inganta fahimta da gogayyar ilimi a tsakanin Daliban Nijeriya da takwarorinsu na duniya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi November 12, 2025 Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya...
    Uwargidan Shugaba Xi Jinping na kasar Sin Peng Liyuan, da Sarauniya Letizia ta kasar Spain, wacce ke rakiyar Sarki Felipe na VI na Spain a ziyarar da ya kawo kasar Sin, sun ziyarci cibiyar gwaji ta kula da nakasassu ta Beijing a yau Laraba. A cibiyar, Peng da Letizia sun saurari bayanan da aka yi kan ayyukan hidimar nakasassu kuma sun ziyarci wani babban sashen nune-nune na gasar wasannin lokacin hunturu ta nakasassu (Paralympic) ta Beijing da aka yi a shekarar 2022. Daga nan suka je zauren baje kolin kayayyakin tallafa wa nakasassu da aka kera da manyan fasahohin zamani da kuma sashen karatu na kyauta, inda suka nazarci yadda ake amfani da kayayyakin tallafa wa nakasassu, da ayyukan karatu...
    Ya kuma yi nuni da cewa, a binciken da za a yi na gaba, akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwaje da za su mayar da hankali ga fadada nemo samfuran da za a yi aiki a kansu. Yana mai cewa, “har yanzu muna bukatar kara tabbatar da tasirin maganin da aka yi amfani da shi da kuma samar da nagartattun hanyoyin warkarwa ta yadda jami’an lafiya za su nakalci sahihin zabin da za su yi amfani da shi wajen magance matsalolin rashin haihuwa mabambanta, da kuma tabbatar da cimma muradun samun haihuwar.” Tabbas, kamar yadda kasar Sin take da sa kwazo cikin abubuwan da take yi, ina da yakinin za a zurfafa wannan bincike domin cike gibin da aka gano...
    Tawagar matan Najeriya ’yan ƙasa da shekaru 20, Super Falconets, ta lashe gasar Yammacin Afirka ta bana WAFU B U-20, bayan ta doke Black Princesses ta Ghana da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a safiyar Talata. An fafata wasan ne a filin Stade Omnisports da ke Jamhuriyar Benin, inda Akekoromowei, Alaba Olabiyi da Ramotalahi Kareem suka zura ƙwallaye uku da suka bai wa Najeriya nasara. An gano motar da aka sace a Gidan Gwamnatin Kano Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Super Falconets ke lashe wannan kofin tun lokacin da aka fara gasar. Ghana, wadda ta lashe kofin a shekarar...
    Wakil ya ce, bayan samun rahoton, tawagar ‘yansanda karkashin jagorancin jami’in ‘yansanda na sashin, CSP Holman Simon, sun ziyarci wurin nan take domin tantance irin barnar da aka yi.   Ya bayyana cewa, binciken farko ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da Alhassan Jibrin, wanda aka fi sani da Babani Biri, matashi mai shekaru 20 mazaunin yankin Danjuma Goje, Bauchi, ya jefar da wayarsa ta Android a wurin da aka yi fashin.   “Binciken ya kai ga kama wasu mutane uku: Lawan Adamu, da Lawan Idris, mai shekaru 20, da Muhammad Yau, wanda aka fi sani da Madugu, mai shekaru 22, duk mazauna Bauchi ne” in ji CPRO ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan...
    ’Yan sanda a Jihar Kano sun gano wata mota ƙirar Toyota Hilux mallakar ofishin mataimakin gwamnan jihar, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, wadda aka sace kwanan nan a harabar gidan gwamnati. Majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano sun ce an sace motar ce cikin dare, lamarin da ya kai ga tsare direban da motar ke hannunsa, Shafiu Sharp-Sharp a matsayin ɗaya daga cikin ababen zargi. Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo Troost-Ekong ya gargaɗi Super Eagles kan wasan da za ta fafata da Gabon Sai dai wata sanarwa da ofishin mataimakin gwamnan ya fitar, ta ce jami’an tsaro sun gano motar da safiyar wannan Larabar bayan wani aikin haɗin gwiwa na gaggawa da aka...
    A shekaru fiye da 20 da suka gabata, birnin Wenzhou dake lardin Zhejiang na kasar Sin ya yi suna domin samar da takalma, kuma kayayyakin da ya samar sun samu karbuwa a duniya domin suna da araha. Amma ma’aikatan kamfanonin samar da takalma sun yi aiki har na tsawon awoyi 14 a kowace rana, inda yawan takalman da aka samar a shekara daya ya kai miliyan 100, amma ribar kowane takalma biyu ba ta wuce Yuan biyu kacal ba, kana ba su da inganci, har ma mutanen Turai suna wa takalman shagube da sunan takalman yini daya. Batun ya sa kaimi ga Xi Jinping wanda ya yi aiki a gwamnatin lardin Zhejiang da ya tsai da kudurin canja burin kamfanonin...
    Amurka ta dakatar da ka’idar fadada jerin wadanda kasar ta takaita fitar wa kayayyaki a kwanan nan, wani muhimmin mataki ne da Amurkan ta dauka a fannin cimma matsayar da aka amincewa, yayin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin Sin da Amurka a Kuala Lumpur. Kuma kasashen biyu za su ci gaba da tattaunawa kan shirye-shirye bayan dakatarwar shekara guda. Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin ya bayyana hakan ne kan tambayar da ’yan jarida suka yi masa game da matakin na Amurka na dakatar da ka’idar fadada jerin wadanda kasar ta takaita fitar wa kayayyaki, a yayin taron manema labarai na jiya Talata. Kakakin ya kara da cewa, Sin tana son yin aiki tare da Amurka, ta...
    Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa. Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko biyu masu zuwa. Troost-Ekong ya gargaɗi Super Eagles kan wasan da za ta fafata da Gabon Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro “Eh, tabbas wannan shi ne Kofin Duniya na ƙarshe da zan halarta. Zan kai shekara 41, kuma ina ganin wannan ne lokacin da ya dace na ajiye takalmi,” in ji shi a wata tattanawa...
      A jawabinsa, ministan ya bayyana cewa, binciken jin ra’ayin ‘yan kasa a fannin kiwon lafiya da aka gudanar a shekarar 2023, 2024, da 2025 ya nuna sakamako mai karfafa gwiwa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025
    Kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya gargaɗi ’yan wasan ƙasar da su guji tafka kura-kurai a wasan da za su buga da Gabon a ranar Alhamis. Ekong ya yi wannan gargaɗi ne kafin fara atisayen ’yan wasan a safiyar Talata, a yayin da suke ci gaba da shirin fafatawar neman gurbin shiga Kofin Duniya na 2026. Wike: Za mu kare duk wani soja da ke aiki bisa doka — Ministan Tsaro ’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa Super Eagles za ta kece raini da Panthers of Gabon a wasan da ake sa ran zai kasance mai matuƙar muhimmanci wanda shi zai tabbatar da matsayin Najeriya na samun tikitin...
    Daga Bashir Meyere Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman rancen Naira Tiriliyan 1.15 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025. Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da lamuran bashi na cikin gida da na waje. Yayin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, wanda mataimakinsa Sanata Haruna Manu ya wakilta, ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 59.99 da Majalisar ta amince da shi, ya karu da Naira tiriliyan 5.25 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 54.74 da gwamnatin tarayya ta fara gabatarwa. Ya ce an riga an amince da Naira tiriliyan 12.95 a cikin kasafin, wanda hakan ya...
      An umarci shugaban karamar hukumar da ya mika harkokin majalisar ga mataimakiyarsa, Mrs Victoria Okolo, har sai an kammala binciken.   Majalisar ta bai wa kwamitin binciken wata daya don kammala aikinsa tare da bayar da rahoto kan matakin da ya dace. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Bisa Zargin Rashin Ɗa’a November 12, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025
    An umarci shugaban karamar hukumar da ya mika harkokin majalisar ga mataimakiyarsa, Mrs Victoria Okolo, har sai an kammala binciken.   Majalisar ta bai wa kwamitin binciken wata daya don kammala aikinsa tare da bayar da rahoto kan matakin da ya dace. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Bikin Baje Koli CIIE, Bikin Zaburar Da Manoman Afirka November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025
    Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amurka tana shirin kafa sanssanin soji  don aikewa da dubban dakaru zuwa iyakar Isra’ila da yankin Gaza, adaidai lokacin da ake fargabar wata sabuwar kasada da kuma sha’awar taimakawa gwamnatin mamaya wajen karbe ikon kula da yankin a nan gaba. Masharhanta na ganin wannan shirin yana zuwa ne saboda irin bakin jini da Isra’ila ta yi a duniya bayan kisan kare dangi da ta yi a yankin Gaza, da ta fara tun daga watan Oktoban shekara ta 2023, wannan yasa telaviv ta bukaci abokiyarta ta ci gaba da aiwatar da aniyarta. Ana sa bangaren jami’an gwamnatin falasdinu sun yi gargadin cewa duk wani mataki da zaa dauka na kokarin canza wani dan mamaya da wani,...
    Hukumar kula da aikin hajji ta kasar Iran ta bayyana cewa shugaban ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiya  Mohammad Bin Salman a wata ziyara da suka kai birnin Riyadh a baya bayan nan. Wannan sakon yana nuna irin kokarin da ake yi ne na ganin an daidaita da kuma  kara yin aiki tare tsakanin Riyadh da Tehran, bisa la’akari da irin tattaunawa da aka yi a shekarar bara, diplomasiya ta addinin dake kewaye da aikin hajji na shekara –shekara ta kasance mai muhimmanci don samar da zaman lafiya . Ali reza Rashidiyan shugaban hukumar aikin hajji ta kasar iran ya kai ziyara kasar saudiya ne domin rattaba hannu kan shirye- shiryen jerjejeniyar aikin hajji da zaa yi a...
    Ministan Tsaron nageriya, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa tare da shugabancin rundunar soji za su kare kowane jami’i da ke bakin aikinsa bisa doka. Badaru ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ma’aikatar tsaro kan bikin tunawa da Sojojin Nijeriya na shekarar 2026, wanda aka gudanarwa a Cibiyar Tsaron Ƙasa (National Defence College), Abuja, a ranar Laraba. Kalamansa na zuwa ne bayan rikicin da ya barke a bainar jama’a tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojan ruwa, Laftanar A. M. Yerima, kan wani fili da ke Abuja da ake zargin mallakar tsohon Shugaban Rundunar Sojan Ruwa, Vice Admiral Zubairu Gambo (mai ritaya) ne. Ya ce: “A Ma’aikatar Tsaro,...
    Kasashen Iran da Pakistan sun yi kira da a yi aiki tare da ya hada da kara dankon zumunci tsakanin yan majalisar domin tunkarar babban makiyinsu, kuma sun yi tir da matakin kai hare-hare da Isra’ila ke yi da kuma ta’adanci a yankin A wani bayani da suka fitar a wata ganawa da suka yi a bayan taron yan majalisu da aka gudanara a yau laraba a birnin Islam Abad, mataimakin kakakin majalisar dokokin kasar iran Ali Nikbad da takwaransa na kasar Pakistan sardar ayaz sadiq sun jadda game da matsayin kasashen na irin gudunmawa da suke badawa a yankin dakuma lammuran da suka shafi kasashen musulmi Nikbad ya bayyana gamsuwarsa game da sanin ya kamatan kasar Pakistan kuma yayi...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da twakaransa na kasar Rasha Sergei lavrov inda suka mayar da hankalin kan batutuwan da suka shafi yankin dama na kasa da kasa  Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta bayyana cewa Iraqchi ya jaddada game da muhimmancin zaman lafiya a yammcin Asiya lokacin da yake ishara game da rikicin baya bayan nan  da ya faru tsakanin Pakistan da Afghanistan, Da ya koma bangaren batun falasdinu kuma Araqchi ya soki matakin da Amurka da kasashen turai suka dauka a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na gabatar da daftarin kuduri na neman a tilasta tura dakarun kasa da kasa zuwa yankin gaza na falasdinu, yace wannan kuduri yayi hannun...
      Kafin ganawar ta su, shugaba Xi ya shiryawa sarki Felipe VI bikin maraba da zuwa. Kana bayan tattaunawar, shugaba Xi da sarki Felipe VI, sun halarci bikin sanya hannu kan takardun hadin gwiwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Kira Da A Inganta Mika Mulki Cikin Kwanciyar Hankali A Sudan Ta Kudu November 12, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam November 11, 2025 Daga Birnin Sin Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa November 11, 2025
    Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tare da shugabannin Rundunonin Sojin Najeriya, za su ci gaba da kare duk wani jami’i da ke gudanar da aikinsa bisa doka. Badaru, ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a taron da aka shirya domin bikin tunawa da Sojojin Najeriya na shekarar 2026 a Abuja. ’Yan sanda sun kama mutum 14 kan zargin ta’amali da miyagun ƙwayoyi a Jigawa MDD ta sanya Najeriya cikin ƙasashe 16 da ke fama da tsananin yunwa Wannan na zuwa ne bayan ce-ce-ku-cen da ya faru ranar Talata tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojan ruwa, Laftanar A. M. Yerima. An yi taƙaddama ne kan wani...
    A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Sakataren Yada Labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana lamarin a matsayin “cin amana a fili da direban da aka kama ya yi.”   “Ofishin Mataimakin Gwamna ya yaba wa binciken gaggawa da rundunar tsaron ta yi ta hanyar amfani da kaifin basira da kwarewa,” in ji sanarwar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12,...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutum 14 da ake zargi da ta’amali da miyagun ƙwayoyi da kuma aikata wasu laifuka daban. Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar. MDD ta sanya Najeriya cikin ƙasashe 16 da ke fama da tsananin yunwa DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu A cewar SP Shiisu, jami’an rundunar sun kama mutanen ne a wurare daban-daban da suka haɗa da Dutse, Guri, Babura, Kanya Babba, Bulangu da kuma ‘Yankwashe. Ya ce rundunar ta ƙwato miyagun ƙwayoyi iri-iri da suka haɗa da Exol guda 8,271, D5, Tramadol, Diazepam,...
    Mataimakin wakilin dindindin na Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da jawabi yayin taron kwamitin sulhu game da batun Sudan ta Kudu da aka gudanar jiya Talata, inda ya yi kira da a inganta mika mulki cikin kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu. Sun Lei ya ce, Sin ta bukaci dukkan bangarorin kasa da kasa da su mayar da hankali kan yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, kana su dakatar da ayyukan da ka iya haifar da tashe-tashen hankula, musamman ma a hana amfani da karfin tuwo da kuma guje wa karuwar rikice-rikice. Sun Lei ya kara da cewa, kasar Sin ta yi imanin cewa, mabudin warware matsalolin kasashen Afirka yana hannun Afirka. Duk wata mafita ya kamata ta...
    “Muna bincike wannan lamari, kuma muna tabbatar da cewa duk jami’in da yake aikinsa bisa doka, za a kare shi. Ba za mu bari wani abu ya same shi (Yerima) ba matuƙar yana aikinsa yadda ya kamata kuma yana yin aikinsa sosai.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025 Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025
    Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), ta ayyana Najeriya ɗaya daga cikin jerin ƙasashen da za su fuskanci matsananciyar yunwa. Ta kuma yi gargaɗin cewa ƙarin mutane a duniya na iya fuskantar yunwa saboda ƙarancin kuɗin tallafi. Rahoton da Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO) da WFP suka fitar, ya nuna cewa rikice-rikice da tashin hankali ne ke jawo matsananciyar yunwa a ƙasashen da ke cikin hatsari. DSS ta gurfanar da matashin da ya yi kira a yi juyin mulki a Najeriya a gaban kotu Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP Rahoton ya bayyana ƙasashen Haiti, Mali, Falasdinu, Sudan ta Kudu, Sudan da Yemen a matsayin waɗanda ke cikin mafi munin...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al`ummar jihar. Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim ya bada wannan tabbacin a dakin taro na ma’aikatar lafiya ta jihar a Dutse. Yace ayyukan da za’a gudanar a asibitocin sun hada da samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da ruwan sha. Sauran sun hada da kewaye asibitocin domin inganta yanayin aiki da al’amuran tsaro. Dakta Kabiru Ibrahim ya kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa kokarinta na tallafawa harkokin kiwon lafiya a jihar.  
    Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. A cewarsa, wannan mataki na daga cikin jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa ci gaban al’umma musamman a yankunan karkara. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, aikin na nuna kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da karin samun wutar lantarki, kara habakar tattalin arziki,...
    Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar wani matashi mai suna Innocent Chukwuemeka Onukwume, mai shekaru 27, bisa zargin kiran sojoji da su yi juyin mulki a Najeriya. Hukumar dai ta shigar da ƙarar matashin ne cikin tuhuma shida a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja. Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu An shigar da ƙarar ne mai lamba FHC/ABJ/CR/610/2025, dangane da wasu rubuce-rubuce da matashin ya wallafa a shafinsa na X a watan Oktoban 2025. A cewar DSS, waɗannan rubuce-rubuce sun nemi a kifar da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki tare da nuna goyon baya ga sojoji su karɓi mulki a ƙasar. Lauyan...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  Babban Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda mai kula da shiyya ta 8, da ke Lokoja, AIG Abubakar Zubairu, ya bukaci jami’an ‘yan sanda a Jihar Kwara da su ninka kokarinsu wajen karfafa hadin kai da kuma zurfafa dangantaka tsakanin ‘yan sanda da al’umma. A wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi ta fitar, ta ce AIG Zubairu  ya yi wannan kira yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kwara da ke Ilorin. Sanarwar ta yaba wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar ‘yan sanda da kuma kudaden da gwamnatinsa ke fitarwa domin inganta tsaro. Haka kuma, ta yi kira...
    Daga Khadijah Aliyu Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da Kwamitin Jagorancin Shirin Ilimi da Ƙarfafa Matasa a Arewa maso Yammacin Najeriya (EYEPINN) wanda kungiyar  Tarayyar Turai ke daukar nauyinsa domin fadada damar samun ingantaccen ilimi da kuma karfafa gwiwar matasa a yankin. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Kano, karkashin jagorancin Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda. Yayin jawabinsa, Dakta Makoda ya bayyana shirin EYEPINN a matsayin “Alƙawari mai Manufa”, yana mai cewa manufar shirin ita ce cike gibi a fannin ilimi, karfafa haɗin kai, da kuma baiwa matasa kwarewar da ta dace domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Ya ce sabon kwamitin da aka kaddamar zai yi jagoranci kan dabaru,...
    Matar tsohon shugaban kasar Gaba, Sylvia Bongo da kuma dansa Nuruddin Bongo za su yi zaman kaso na tsawon shekaru 20 saboda samunsu da laifin almubazzaranci da kudin kasa. Kotun da ta yi shari’ar ta yanke hukunci ne akan iyalan tsohon shugaban kasar Ali Bongo  ba tare da suna gabanta ba. Kotun dai an kafa ne domin yin binciken laifuka da suke da alaka da barnata dukiyar kasa. Kotun ta sami mai dakin tsohon shugaba Bongo, Sylvia Bongo Ondimba da laifin almundahana da dukiyar kasa da kuma yin takardu na jabu. Shi kuwa  Nuruddin Bongo an same shi ne da laifukan da su ka hada da runton bai wa kai mukamai,wanke kudaden haram da mayar da su halaliya, sannan da...
    Ya bayyana cewa mutanen sun fita da sassafe don wani aiki, amma ‘yan bindigar suka tare su suka kashe su tare da tserews da babur ɗinsu . Mista Ajeh, ya roƙi hukumomin tsaro da su gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu. Haka kuma, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a Jihar Nasarawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai...
    A jiya Talata ne dai MDD ta yi kira da a gudanar da bincke akan kashe-kashen da aka yi sanadiyyar zaben da aka yi a watan karshe. Wannan kiran na MDD ta zo ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar ta Tanzania su ka tuhumi wasu daruruwan mutane da cin amanar kasa saboda Zanga-zangar  kin amincewa da zabe da su ka yi. Shugaban hukumar kare  hakkin bil’adama a karkashin MDD Volker Turk ya ce; Da akwai Alamar cewa gwamnatin kasar ta Tanzania tana kokarin batar da dalilai abinda ya faru. Da akwai rahotanni da suke nuni da cewa jami’an tsaro suna kokarin dauke gawawwakin wadanda aka kashe daga dakunan ajiyar gawawwaki na asibitoci domin batar da su. Turk ya kira...
     A yau Laraba ne aka sanar da zaman Iran memba a cikin wannan kungiyar ta ( ISKO) wacce aka bude reshenta a cikin kasa tun a 2011. Farfesa Rahmatullah Fattahi ne ya bude reshen kungiyar ta ” Ilimomin Tattara Bayanai Da Kere-Kere” wacce kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa 2019. An sami tsaiko a yadda kungiyar take tafiyar da ayyukan nata, saboda bullar Korona, amma ta ci gaba da aiki a karkashin wani tsari na musamman  ( IranDoc.). Aikin wannan cibiyar shi ne tsara gudanar da nazarori da bincike na ilimomi mabanbanta da kuma hana yin maimaici akansa. A halin yanzu da akwai mutane 20 da suke aiki a karkashin wannan kungiyar daga asalin su 20...
    Ya ƙara da cewa rundunar ta samu nasarar ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka ceto daga hannun masu safarar mutane, inda aka miƙa su ga iyalansu. Kayan da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargi sun haɗa da bindiga AK-47 guda ɗaya, bindiga ta gida guda ɗaya, alburusai 183, motoci uku, babur mai ƙafa uku da keke napep ɗaya, da kuma dabbobi sama da 200 na sata. Haka kuma, ‘yansanda sun ƙwato tarin miyagun ƙwayoyi irin su Fentalin, Exol, Tramadol, da wiwi, tare da wayar wutar lantarki. Abubakar ya sake tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙari wajen tabbatar da tsaro, inda ya ce, “Duk da waɗannan nasarori,...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja November 7, 2025 Siyasa Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha November 4, 2025 Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump November 3, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025 Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025
    Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kano da Kewaye, Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi, ya bayyana ficewarsa a hukumance daga jam’iyyar NNPP. Ƙoƙ8 inda ya danganta hakan da rikicin shugabanci da ke kara tsananta a cikin jam’iyyar. PDP ta sha alwashin gudanar da babban taronta duk da umarnin kotu Abdulmumin Jibrin ya koma APC wata 2 bayan NNPP ta dakatar shi A cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 11 ga Nuwamba, 2025, wacce aka aika wa Shugaban jam’iyyar a Unguwar Zaitawa a Karamar Hukumar ta Birni, Koki ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa hakkin sa na kundin tsarin mulki na ’yancin shiga ko ficewa daga kowace jam’iyya. “Bisa ga hakkin da kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12, 2025 Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025
    Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya. Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka Gwada Don Samar da Abinci da Ƙara Darajar Kayayyaki a Najeriya”, da aka gudanar a Ilorin. Ya ba da shawarar kafuwar cibiyoyin injinan noma a kowanne yanki na ƙasa, domin horo, gyara, da tsara fasahohin aikin gona. A cewarsa, bayan samun injina, mafi muhimmanci shi ne kafa tsarin daidaitawa, haɗa na’urori a gida, da tsarin kulawa, domin tabbatar da cewa kowanne injin da aka tura...
    Hukumar Kula da jin dadin mahajjan Jihar Taraba ta bayyana 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe ga masu niyyar yin hajji don kammala biyan kuɗin tafiyar hajji ta shekarar 2026. A cewar wata sanarwa da Sashen Bayani na Hukumar ya fitar ta bakin Mataimakin Daraktan Hamza Baba Muri, an ƙayyade sabon kuɗin hajjin 2026 a Naira miliyan 7,630,000, kamar yadda Hukumar Hajj ta Kasa (NAHCON) ta amince. Hukumar ta yi kira ga duk masu shirin yin hajji ta wannan tsari su tabbata sun biya kuɗin gaba ɗaya kafin ƙarshen wa’adin domin samun tabbacin shiga cikin masu sauke farali shekara mai zuwa. Mai magana da yawun Hukumar ya jaddada cewa dukkan biyan kuɗi dole ne a yi su ta...
    Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na faɗaɗa gonakin shinkafar Jangwa daga hektar 3,300 zuwa hektar 5,000 a kakar noma mai zuwa, domin haɓaka samar da shinkafa da kuma ƙarfafa tattalin arziki a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin ziyarar duba girbin shinkafa a garin Jangwa, ƙaramar hukumar Awe. Gwamnan ya ce faɗaɗa gonakin zai ƙara hektar 3,000 daga yawan da ake da shi yanzu, domin inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar aikin gona. Ya kuma nuna yadda jihar ta samu ci gaba a fannin noma, inda gonar ta faɗaɗa daga hektar 2,000 a bara zuwa hektar 3,300 a wannan shekarar. Gwamna Sule ya sanar da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da kamfanin Silvex International, babban kamfani...
    A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni. Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da wakilan al’umma. Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda Mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya wakilta, ya tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen tabbatar da cewa kowane yanki a cikin karamar hukumar na da damar samun ingantacciyar kiwon lafiya mai sauƙin samu da araha. Ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokoki ta Gwarzo, Ahmad Shehu Sabon Birni, da sauran kansiloli bisa...
    Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar da horon cikin gida na farko ga ma’aikatanta, wanda ya mayar da hankali kan aiwatar da dokokin aikin gwamnati, kyawawan ɗabi’un aiki da kuma ingancin ayyuka. Wannan horo, wanda ya zama muhimmin mataki a shirin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata na hukumar, an shirya shi ne domin haɓaka inganci a ayyuka da ƙarfafa ƙwararru da tabbatar da bin ƙa’idojin aikin gwamnati yadda ya kamata. A jawabinta, Manajiyar Darakta ta KNUPDA, Arc. Hauwa Hassan Tudun-Wada, ta bayyana horon a matsayin muhimmiyar hanya ta gina al’adar ladabi da biyayya da nagarta a cikin ma’aikatan gwamnati. Ta yaba da jajircewa da himmar ma’aikata wajen halartar shirin, inda ta jaddada cewa fahimta da bin dokokin...
    Shugaban Hukumar Gudanarwa Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na dawo da tsohon martabar Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano. Dakta Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar duba aiki da ya kai filin jirgin a Kano. Ya jagoranci wata tawaga mai ƙarfi ta jami’an FAAN domin tantance halin da filin jirgin yake ciki yanzu, ciki har da ayyukan da ake gudanarwa da kuma waɗanda aka bari da nufin samar da cikakken tsari na zamani da dorewar ci gaba. Ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin tsofaffin filayen jiragen sama masu tarihi a Najeriya da yankin Yammacin Afirka, wanda a da yake ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin...
    Pars Today – Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan, yana Allah wadai da fashewar da ta faru a babban birnin Pakistan, ya ce ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin kuma fuskantar wannan mummunan lamari yana buƙatar haɗin gwiwa, ƙuduri, da haɗin kai daga dukkan ƙasashe. Reza Amiri-Moqaddam, Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan, a ranar Talata, yayin da yake Allah wadai da fashewar ta’addanci a birnin Islamabad – wanda ya kashe mutane 12 tare da raunata aƙalla wasu 30 – ya ce: “Ta’addanci makirci ne na matsorata waɗanda ke neman wargaza yankinmu da kuma sanya cikas a hanyarsa ta zuwa ga ci gaba mai ɗorewa.” A cewar jaridar Pars Today, jakadan Iran a Pakistan ya jaddada cewa: “Wannan...
    Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana kudurinta na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na kasa da aka tsara a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba. Hakan na zauwa ne duk da sabon umarnin kotun tarayya da ke hana ta ci gaba da shirya taron. Yadda muka daƙile yunƙurin tsige Akpabio daga shugabancin Majalisa – Orji Kalu DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma Mataimakin Sakataren Yada Labarai na kasa na jam’iyyar, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa hukuncin kotun da ke dakatar da taron “bata lokaci ne kawai,” yana mai jaddada cewa jam’iyyar na bin hukuncin da kotun koli ta yanke a baya wanda...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Sayyed Abbas Araghchi, ya ce masana’antar nukiliya yanzu ta zama babban fanni kuma tana kara samun ci gaba cikin sauri a fannoni daban-daban. Sabanin yadda ake ganin cewa wannan masana’antar ta takaita ne ga tace  uranium, ya kara da cewa ana gudanar da ayyuka da dama da suka shafi fannoni daban-daban na rayuwar mutane, ciki har da maguguna, fannin kiwon lafiya, muhalli, noma, da masana’antu a cibiyoyin Makamashin Nukiliya ta Iran. A lokacin ziyarar da ya kai wa Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Araghchi ya jaddada cewa fasahar nukiliya tana nan a dukkan fannoni tana ba da gudummawa ga ci gaban fannoni daban-daban. Ya kara da cewa wannan ilimi da fasaha suna hanzarta ci gaban kimiyya...
    Shugaban Majalisar Saukar da Mulkin Sudan, Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya tabbatar da zurfin dangantakar Sudan da Masar, yana mai nuni da dadadden zumunci da tarihi da ke tsakanin al’ummomin biyu. A lokacin ganawarsa da Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty, Burhan ya bayyana ” godiyarsa ga Masar, gwamnati da jama’a, saboda goyon bayan da suke bai wa Sudan a dukkan dandali na yanki da na duniya, da kuma jajircewarsu ga tsaro,  kwanciyar hankali da kuma ‘yancin kan Sudan,” yana mai jaddada “ra’ayin da kasashen biyu suka cimma na ci gaba da hadin gwiwa a dukkan fannoni.” A nasa bangaren, Abdel-Aty ya tabbatar da “cikakkiyar goyon bayan Masar, ta jagoranci da kuma ta jama’a, ga Sudan ‘yan uwantaka, bisa...
    Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya sanya hannu kan dokar kafa cikakkiyar rundunar tsaro ta kasa a wannan Laraba. Maduro ya jaddada bukatar kafa cikakkiyar rundunar tsaro, wacce ta hada dukkan cibiyoyin soja na gwamnati da kuma dakarun sa kai najama’a a safiyar yau Laraba. Dokar na da nufin tsara da kuma hada dukkan cibiyoyin gwamnati, kamar sojoji da ‘yan sanda, da kuma al’umma wajen  fuskar barazanar waje ko ta ciki, a karkashin ka’idar kare cikakken tsaro” na Venezuela daga duk wata barazana ga kasar. Mahimmancin wannan doka ya ta’allaka ne kan karfafa ikon shugaban kasa da na sojoji a cikin mawuyacin hali. Yana nuna yanayin da ake ciki na mayar da hankali kan ayyukan soja ga gwamnati da al’umma, kuma...
    UNICEF ta yi gargadin cewa  Isra’ila na hana shigar da muhimman kayan aikin da ake buƙata don  allurar rigakafi a Gaza, wanda hakan ke kawo cikas ga ƙoƙarin isa ga yara a yankin da yaƙi ya daidaita. Hukumar ta ce kayayyakin, ciki har da sirinji da ake amfani da su don allurar rigakafi na yau da kullun da kwalaben madarar jarirai, har yanzu suna nan a wuraren bincike, duk da ci gaba da tsagaita wuta da kuma ƙaruwar buƙatun jin kai. UNICEF ta bayyana cewa a halin yanzu tana gudanar da Shirin allurar rigakafi ga yara ‘yan ƙasa da shekara uku, waɗanda da yawa daga cikinsu sun rasa allurar rigakafi na yau da kullun a cikin shekaru biyu da suka...
    An kama diraben da ke jan motar Shafiu Sharp-Sharp, domin yi masa tambayoyi. “An riga an fara bincike. Ana yi wa direban tambayoyi, yayin da Babban Jami’in Tsaro (CSO) ke duba bidiyon CCTV,” in ji wata majiya. “An miƙa bayanan motar ga jami’an tsaro domin su gano motar da kuma kama ɓarawon.” Kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, bai amsa kiran waya da saƙonnin da aka tura masa ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025 Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya,...
    “Dukkanin bayanan da ake da su sun nuna cewa babu wani kisan gillar da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya… Wannan labarin ƙarya ne da ƙungiyoyi suka ƙirƙira, wanda Shugaba Trump ke ƙoƙarin yaɗawa. “Wannan magana za ta iya ƙara tayar da hankali a Nijeriya… ‘Yan ta’adda suna kai hare-hare a kasuwanni, coci-coci, da masallatai, kuma suna kashe kowa ba tare da bambance tsakanin Musulmi da Kirista ba,” in ji Bukarti yayin wata hira da gidan talabijin na Al-Jazeera. Masana da dama sun yi gargaɗin cewa irin wannan kalamai daga shugabanni na iya haddasa tashin hankali a ƙasar. Martanin Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Tarayya ta kuma mayar da martani ta hanyar ƙaryata batun cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar. A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu. Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu daidaikun mutane maimakon tsaron alummar kasa gaba daya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga...
    Laftanar Janar Shaibu ya bayyana cewa, bayanin da ya yi wa Shugaban Kasa, ya yi ne kan sakamakon rangadin aikinsa na yankin Arewa maso Gabas da kuma sabbin bayanai kan yanayin tsaro a fadin kasar.   “Na zo ne domin in yi masa bayani kan sakamakon ziyarar da na kai yankin Arewa maso Gabas sannan da kuma bitar wasu yanayin tsaro a fadin kasar, wanda hakan ya gamsar a wannan lokacin,” in ji Babban Hafsan Sojan Kasa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina November 11, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Sake Hana PDP Gudanar Da Babban Taronta Na Ƙasa November 11, 2025 Manyan...
      Ban da wannan kuma, game da batun cewa kasashen kungiyar EU suna shirin cire na’urorin kamfanonin sadarwa na kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin suna aiwatar da ayyukansu bisa doka a nahiyar Turai na dogon lokaci, wadanda suka samar da kayayyaki da hidimomi masu inganci ga jama’ar Turai, tare da samar da muhimmiyar gudummawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma da samar da ayyukan yi a nahiyar. Kasar Sin ta kalubalanci kungiyar EU da ta samar da yanayin gudanar da ciniki cikin adalci da rashin nuna bambanci ga kamfanonin kasar Sin don magance wargaza amannar da kamfanonin suka yi wa nahiyar Turai kan zuba jari. (Zainab Zhang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin...
      Bugu da kari, abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta ba da jagoranci ga kasashen duniya ta fuskar kara bude kofa ga waje. Ta hanyar shigowa da kayayyaki da fitar da kayayyaki, kasar Sin ta ba da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya, da kara yawan kayayyakin da kasashen duniya suke fitarwa, tare da ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen kyautata harkokin masana’antu. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta ba da taimako wajen shigar da mambobin WTO su 130 cikin yarjejeniyar samar da sauki a ayyukan zuba jari domin neman ci gaba, ta yadda kowa zai cimma moriyar sakamakon dunkulewar duniya cikin adalci. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Ya...
    Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya albarkacin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato Taken taron shi ne: “Shekaru 65 da samun ’yancin kai: Tafiyar Najeriya zuwa yanzu a ƙarƙashin Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda)”, inda aka haɗa...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15 November 11, 2025 Daga Birnin Sin Me Sabon Tarihin Da Aka Kafa A Baje Kolin CIIE Ke Nunawa? November 11, 2025 Daga Birnin Sin Jakadun Kasashen Waje: Shirin Raya Kasa Na 15 Na Sin Na Dauke Da Kyakkyawan Sako November 11, 2025
    An gudanar da taron karawa juna sani game da aikin watsa shirye-shiryen gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15 ta hanyar talabijin ta zamani, wato taron karawa juna sani na hada fasahohin yada labarai, a jiya Litinin a birnin Guangzhou dake lardin Guangdong na kasar Sin. A yayin taron, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da sabbin manhajoji guda 10 da ya kirkiro ta hanyoyin kimiyya da fasaha don watsa gasar wasannin motsa jiki ta kasar Sin karo na 15. CMG zai yi amfani da sabbin fasahohi, kamar kirkirarriyar basira ta AI da fasahar tsimin makamashi da kyautata ingancin hotuna da rediyo da dai sauransu, ta yadda zai samar da...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin. “Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu...
    An kama mutane 18 bisa laifin fashi da makami, mutane 28 bisa laifin kisan kai, mutane biyar bisa laifin yunkurin kisan kai, mutane 20 bisa laifin fyade da laifukan da ba su dace ba, da kuma mutane 28 bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.   Jami’in ‘Yansandan, ya kara da cewa, daga cikin jimillar kararrakin 120, an gurfanar da mutane 97 a gaban kotu, yayin da ake gudanar da bincike kan 22 a halin yanzu.   Bugu da kari, an ceto mutane 47 da aka yi garkuwa da su da kuma mutane 39 da aka yi safarar su amma tuni an hada su da iyalansu.   Jami’in ya kuma nuna wasu kayayyaki da aka kwato a hannun masu laifin da...
      Mun yi imanin cewa a nan gaba, karin kamfanonin Afirka za su ga fa’idar budaddiyyar kasuwar Sin ta CIIE, za su kuma kara zurfafa hadin gwiwa tare da Sin, da yin amfani da damammakin CIIE don samun moriyar juna. (Mai zane da rubutu: MINA) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari November 6, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki November 4, 2025 Ra'ayi Riga Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan November 4, 2025
    Kungiyar kasashe da cibiyoyin kasa da kasa ta fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa da ta yi Allah wadai da manyan laifukan da aka aikata a ƙasar Sudan bayan kwace El Fasher daga dakarn (RSF) suka yi, da kuma ƙaruwar tashin hankali a yankin arewacin Darfur da Kordofan. Wannan sanarwar, wadda ministocin harkokin waje da manyan jami’ai daga Australia, Belgium, Kanada, Denmark, Estonia, Hukumar Tarayyar Turai, Jamus, Iceland, Ireland, Luxembourg, New Zealand, Netherlands, Norway, Slovakia, Slovenia, Spain, Sweden, da Birtaniya, tare da goyon bayan Austria, Croatia, Cyprus, Czechia, Finland, Latvia, Poland, Romania, da Switzerland suka yi, ta nuna damuwa sosai game da rahotannin ta’asar da aka aikata a kan fararen hula. Wannan sanarwar haɗin gwiwa ta yi nuni da...
    Wannan shi ne baje koli na farko bayan taron kwamitin kolin JKS da ya amince da shirin raya kasa na shekaru 5-5 karo na 15, wanda ya jaddada kudurin Sin na fadada bude kofarta. Halartar kamfanoni da adadinsu ya kai 4,108, daga manya da matsakaita da kananan kasashe ya tabbatar da cewa, kofar Sin a bude take ga kasa da kasa su shigo, su yi cudanya da hadin gwiwa domin samun ci gaba na bai daya. Karuwar adadin mahalarta tamkar kira ne cewa, duniya ta amince kuma tana goyon bayan manufofi da tsare-tsaren kasar Sin. Haka kuma, goyon baya ne ga kiran kasar Sin na dunkule tattalin arzikin duniya da bunkasa cudanyar bangarori daban-daban domin samun ci gaba tare. Bugu...
    Ana fargabar cewa an yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara huɗu fyaɗe a ƙaramar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe. Da yake zantawa da manema labarai fyaɗe da safiyar Litinin, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta samu mummunan rauni a al’aurarta. John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda a Borno Mutumin da ake zargi da wannan aika-aikar mai suna Rabilu Sani, ɗan kimanin shekara 22, an gano cewa yana ɗauke da cutar kanjamau (HIV), kamar yadda mahaifin yarinyar ya tabbatar wa manema labarai. A wata hira da aka yi da mahaifin ta ta wayar tarho, ya bayyana cewa an kai yarinyar asibitin Jakusko tare da wanda ake zargi, inda...
    Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty ya karbi bakuncin Wakiliyar Musamman ta Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Hanna Tetteh, a matsayin wani bangare na ci gaba da hadin gwiwa da tattaunawa ta kut-da-kut da Majalisar Dinkin Duniya game da abubuwan da ke faruwa a Libya da kuma goyon bayan kokarin da ake yi na cimma matsaya ta siyasa. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Masar, Tamim Khallaf, ya bayyana cewa Minista Abdel-Aty ya tabbatar a lokacin taron cewa matsayin Masar kan rikicin Libya, ya dogara ne kan bin tsarin siyasa da Libya take a kai ba tare da wani umarni ko tsangwama daga waje ba, a matsayin hanya daya tilo ta dawo da tsaro da kwanciyar...
    Shugaban  tsaron kasar ta Iran ya yi watsi da rahotannin da ake yayatawa cewa  iran ta bude wasu hanyoyin tuntuba da Washington, yana mai jaddada cewa ba a isar da wani sabon sako ga Amurka ba. Ali Larijani ya jaddada cewa fifikon Iran a koyaushe shi ne dage takunkumin da aka kakaba mata, wanda ya bayyana a matsayin kokarin diflomasiyya na gwamnatin kasar. Duk manufofin gwamnati da kokarin diflomasiyya suna mai da hankali ne kan kawo karshen takunkuman,” in ji shi. Ya bayyana ce sakon da ake yayatawa ya samo asali ne daga shawarwarin da akayi a baya, amma Amurka ba ta nuna sha’awar cimma yarjejeniya ba. Wannan bayanin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da...
    Ofishin yada labarai na gwamnatin zirin Gaza ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ‘yan mamayar Isra’ila sun karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza sau 282 tun bayan aiwatar da ita. Sanarwar ta nuna cewa tun lokacin da aka fara yarjejeniyar tsagaita wuta, an kashe fararen hula 242 tare da raunata wasu sama da 620, wanda hakan ya zama keta dukkan ka’idoji da kudurori na kasa da kasa da aka amince da su. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Muna Allah wadai da karya wannan yarjejeniya da aka yi akai-akai kuma muna daukar ‘yan mamayar da alhakin sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro da na jin kai. Muna jaddada cewa ci gaba da wannan lamari yana barazana ga yarjejeniyar...
    ‘Yan Iraki sun kada kuri’a don zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki wadda za ta fayyace alkiblar siyasar kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Kimanin ‘yan kasar miliyan 21 ne aka tantance domin kada kuri’a ga ‘yan majalisar dokoki 329, Wadannan za su zabi shugaban kasa kuma su amince da sabuwar gwamnatin, wadda sabon firaminista zai kafa. A cewar jami’an zabe, za a sanar da sakamakon cikin sa’o’i 24 bayan kammala zaben. Firaminista Mohammed Shia al-Soudani ya bayyana zaben a matsayin wanda ya gudana “a cikin yanayi mai aminci da kwanciyar hankali,” yana yabon jami’an tsaro saboda kiyaye tsarin. Al-Soudani, wanda aka zaba a shekarar 2022, yana neman wa’adi na biyu kuma zai bukaci samun rinjaye a majalisar. A Iraki,...