Shugaban Kasar Iran Ya Kai Ziyara Zuwa Kasar Oman don Karfafa Kyakkyawar Alakar Kasashen Biyu
Published: 27th, May 2025 GMT
Kafin tashinsa zuwa kasar Oman shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna neman kyakkyawar dangantaka da maƙwabtansu
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar kafin ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Tehran zuwa birnin Muscat a yammacin yau Talata cewa: Makasudin ziyarar tasa zuwa kasar Oman ita ce kulla kyakkyawar alaka da kasashe makwabta, kuma alaka tsakaninsu tana bunkasa kowace rana.
Shugaba Pezeshkian da yake zantawa da manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Mehrabad ya bayyana cewa: A halin yanzu yawan ciniki tsakanin Iran da Oman ya kai dalar Amurka biliyan 2.3, yana mai jaddada bukatar ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Pezeshkian ya ce: Zai gudanar da wannan ziyara ce bisa gayyatar da Sultan Haitham bin Tariq Al Said ya yi masa a hukumance, kuma bisa ga dukkanin manufofin gwamnati da Jagoran juyin juya halin Musulunci, manufar wannan ziyara ita ce kulla alaka mai zurfi da kyakykyawan dangantaka da kasashen makwabta ciki har da masarautar Oman, haka kuma an shirya fadada dangantakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkanin bangarori na siyasa da tattalin arziki da zamantakewa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Sake Zaben Qalibof A Matsayin Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iran
Majalisar dokokin kasar Iran ta sake zaben Mohammad Baqir Qalibof a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar na wata shekara a zaben da aka gudanar a cikin majalisar a jiya Litinin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa ya sami kuriu 219 daga cikin Jimillan kuri’u 272, wanda ya bashi babban rnjaye a kan sauran wadanda suke takara da shi. Wannan kuma ya nuna cewa shugaban majalisar ya na da karbuwa a cikinta. Kuma yana da tasiri a cikin al-amuran gwamnati musamman a lokacinda kasar take fama da barazana a ciki da wajen kasar, musamman dangane da tattaunawa kan shirin makamashin Nukliyar kasar, wanda ake tattaunawa a kansa da Amurka.
An gudanar da wasu zabubbuka a cikin majalisar tare da fitar da yan majalisun da suka dace wajen rike su.
Akan gudanar da zabe don rike wasu mukamai a majalisar dokokin kasar Iran ne a ko wace shekara. Yan majalisa da dama sun bayyana gamsuwarsu da shugaban Qalibof na shekarar da ta gabata.