Babu wanda ya tayar da bam a Abuja —Wike
Published: 29th, May 2025 GMT
Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya ce rahotannin da ya samu na nuna babu gaskiya a labarin da ake yaɗawa cewa mai ƙunar baƙin wake ne ya tada abu mai fashewa a barikin soji na Mogadishu da ke Abuja.
Wike ya bayyana hakan ne ga manema labarai, lokacin da ya kai ziyarar duba aikin titunan da za a ƙaddamar domin bikin cikar shugaba Tinubu biyu a kan karagar mulki.
Ministan ya kuma ja hankalin ’yan jarida kan yaɗa labaran da ka iya jefa firgici a zuƙatan al’umma.
Aminiya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a shingen bincike na barikin sojin Mogadishu, kuma hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce a ranar Talata ta ce harin ɗan ƙunar baƙin wake ne.
“Jami’an tsaro ba su ce harin ɗan ƙunar baƙin wake ba ne. Saboda haka kar ku je kuna tsorata mutane da maganganu marasa tushe. Ku dinga binciken ƙwaƙwaf kafin yaɗa labaranku. NEMA ba shugabar tsaro ba ce, ma’aikatun tsaro na wurin.
“Abin da ya faru shi ne wani ne ya je wuraren da muke fasa dutsuna. Sai ya ɗauki nakiyar da ake fasa dutse ya saka a aljihu wataƙila don bai san illar hakan ba. Shi ne ta fashe a jikinsa. Ka ga ai hakan ba yana nufin ɗan ƙunar baƙin wake ba ne,” in ji ministan.
Sai dai ya zuwa lokacin haɗa rahoton, daga rundunar soji har ta ’yan sanda, babu wacce ta ce komai kan hakan, sun dai ce suna gudanar da bincike.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kunar bakin wake Tsaro ƙunar baƙin wake
এছাড়াও পড়ুন:
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata
Shugabannin biyu sun yi nazari kan muhimman fannonin hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Faransa, inda suka amince da zurfafa hadin gwiwa don samun ci gaban juna da kwanciyar hankali a duniya.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa ba a bayar da wani dalili na sauya wannan hutun ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp