2025-07-26@23:25:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4881
«yan bindiga sun»:
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da dashen itatuwa na shekarar 2025 tare da sabunta kudirin farfado da fiye da hekta 5,000 da ta lalace a fadin jihar. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da shirin da aka gudanar a shatale-tale na Pentagon da ke Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana aikin dashen itatuwan a matsayin ɗaya daga cikin alkawuran da gwamnatinsa ta ɗauka domin ci gaban al’umma, inda ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen raya muhalli da kare shi. Ya ce: “Wannan yana da alaƙa da manufofinmu da suka shafi ƙaddamar da tsare-tsare da suka dace da kare muhalli, da ƙarfafa juriya da dorewar muhalli, da kuma...
Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen nahiyar Afirika na mata bayan doke masu masaukin baƙi Maroko a wasan ƙarshe da ci 3 da 2. An buga wasan ne a daren ranar Asabar, wanda ya ƙayatar da masu kallo. Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya Ƙasar Moroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu a minti na 14 da minti 24. Amma Nijeriya ta farke duka ƙwallaye biyu kuma ta jefa ta uku a minti na 89 na wasan, da wannan sakamakon Nijeriya ta samu nasarar lashe gasar karo na 10 a...
Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen nahiyar Afirika na mata bayan doke masu masaukin baƙi Maroko a wasan ƙarshe da ci 3 da 2. An buga wasan ne a daren ranar Asabar, wanda ya ƙayatar da masu kallo. Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya Ƙasar Moroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu a minti na 14 da minti 24. Amma Nijeriya ta farke duka ƙwallaye biyu kuma ta jefa ta uku a minti na 89 na wasan, da wannan sakamakon Nijeriya ta samu nasarar lashe gasar karo na 10 a...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano. Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama na jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya shafi kudurori da sabbin batutuwa dangane da gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.” Sanata Barau ya tunatar da cewa Majalisar Ƙasa ta riga ta amince da gyaran kundin tsarin mulki sau biyar, da aka fi sani da alteration acts na farko zuwa na biyar. Ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da ke buƙatar ƙarin...
Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce Arewacin Najeriya na cikin mawuyacin hali, kuma jam’iyyarsu ce kaɗai za ta iya warware waɗannan matsaloli idan aka zaɓe ta. Ya bayyana hakan ne a taron jam’iyyar ADC da aka yi a Abuja Continental Hotel, inda mambobi da magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban suka halarta. Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN David Mark, wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne, ya gabatar da jawabi mai taken: “Haɗin kai da zaman lafiya su ne mafita ga matsalolin Arewa”. Ya ce Arewa na fuskantar matsaloli masu tsanani kamar su rashin tsaro,...
Kakakin rundunar tsaron Isra’ila ya ce suna aiki tare da la’akari da dokokin duniya, inda ya ce Hamas na boye “makamai” a cikin fararen hula, sannan suna “rusa gine-gine ne kawai idan ta zama dole.” An gani a zahiri yadda Rafah ya lalace a kusa da bakin iyakar Masar A ‘yan makonnin da suka wuce, sojojin Isra’ila da ‘yan kwangilar rusau sun sanya alamar rusau a gidaje da dama Nazarin masa irin su Corey Scher da Jamon Ban Den Hoek ya nuna cewa barnar da aka yi a Gaza tun daga watan Afrilu ya yi muni a yankin. Akwai manyan motocin katafila jigbe a yankunan A watan Yuli, ministan tsaron Isra’ila, Katz ya bayyana tsare-tsarensu na kafa abin da...
Sunana Yasar Sale Zareku Miga A Jihar Jigawa: Gaskiya aurar da yarinya ga mutum mai shekaru ya fi, dan shi zai fi kula da hakkinta ya san rayuwa, ni ban ga wata matsala ba dan mace ta auri mutum mai shekaru. Shawarata shi ne iyaye su san wanda ya kamata su aurawa ‘ya’yansu, domin aure muhimmin al’amari ne da ya kamata a zurfafa bincike kafin a gudanar, domin gudun yin kitso da kwarkwata daga karshe nake addu’ar Allah ya bawa mata miji nagari su ma mazan Allah ya ba su mata nagari. Sunana Rahama Bashir daga Jihar Katsina: Ni a gani na auren namijin da ya girmeka ya fi musamman idan shekarun da yawa, sabida kar ku tsufa...
Tsare-tsaren farko: Da yake su Turawan mulkin mallaka su riga sun kasance sun zauna daram a Arewacin Nijeriya, daganan sai suka aiwatar da tsare tsarensu wadanda sun bullo da su ne domin hana cinikin Bayi.Suka maida lamarin wanda a shekarun baya ba matsala bace,amma yanzu a shar’ance, an hana shi,sannan kuma naka samu damar ‘yantar da wadanda Iyayen su suka zama Bayi bayan wani lokaci. Yadda aka bullo ma lamarin: Yayin da ake ta kokarin hana cinikin Bayi, su Turawan mulkin mallaka sun,amince da yadda cinikin Bayi ya shafi lamarin zamantakewa da tattalin arziki a sashen na Arewacin Nijeriya. Don haka sai suka bi abin sannu- sannu, har dai suka samu damar kawo karshen lamarin, ta hanyar bada zabi...
Firai ministan kasar Burtaniya Keir Starmer ya bayyana cewa ya fara tuntubar wasu kasashen turai kan nshirin jefawa Falasdinawa abinci daga sama tare da taimakon kasar Jordan. Shafin yanar gizo na Arab News ya nakalto Starmer yana fadar haka a yau Asanar ya kuma kara da cewa ya yi magana da kasashen Faransa da Jamus kan wannan shirin. Labarin ya kara da cewa banda jefa masu abinci kasashen zasu sauka su dauki marasa lafiya musamman yara kanana don jinyarsu.. Tun kimani watanni 4 da suka gabata ne gwamnatin HKI ta rufe kofofin shiga zirin gaza ta kuma hana shigowar abinci da magunguna, da nufin kashe dukkan falasdinawa kimani miliyon biyu a Gza, don ginawa yahudawa matsugunai a yankin. Tun fara...
Shuwagabannin kungiyoyin musulmi a kasar Amurka sun fara daukar matakan tsaro a masallatai da wuraren taro da kuma makarantun musulci saboda yawan samun wasu magoya bayan yahudawa suna yawaita shiga irin wadannan wurare suna lalatasu. Shafin yanar gizo na labarai ‘ArabaNews” ya bayyana cewa a jihohin Texas da Califonia, masu goyon bayan yahudawan sun lalata masallatai da dama sun kuma sace abubuwa da dama a cikinsu. Edward Ahmed Mitchell, mataimakin sakataren kungiyar ‘ Council on American-Islamic Relations’ wata kungiyar kare hakkin musulmi a Amurka ya shaidawa Arabnew kan cewa tun bayan fara yaki a Gaza shekaru kimani biyu da suka gabata, musulmi a Amurka suka fara fuskantar sabon kiyayya daga wadanda basa son musulmi a kasar. Edword yace abu mafi...
Wasu yan bindiga wadanda ake dangantasu da kungiyar Jaishul-Zulum sun dauki alhakin kai hare-hare a cikin wata kotu a birnin Zahidan babban birnin lardin Sistab Baluchistan a yau Asabar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yan ta’addan sun shigo da motarsu har zuwa a wata kotu a garin da Zahidan, sannan suka sauka suna son shiga kotun amma jami’an tsaro a kotun suka hanasu shiga. Daga nan kawai suka fara jefa nakiya irin da yaki a kansu. An yi ta musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro zuwa wani lokacin suka sami nasarar halakasu. Amma kuma sun kai mutane 6 ga shahada uku daga cikinsu jami’an tsaron kotun da kuma wani yaru da kuma wata mata yar...
Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa JMI zata gaggauta ci gaba a fasahar tsaron kasa da kuma fasahar zamani a dukkan fagage bayan yakin kwanaki 12 da HKI da Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a cikar kwanaki 40 da shahadar manya-manyan kwamandojin sojojin kasar da kuma masana fasahar Nukliya a kasar. Jagoran ya kara da cewa dukkan ilmomi tsaron kasa da kuma fasaha za su cilla da saura don samun ci gaba. A sakon da jagoran ya aikawa mutanen kasar ya yi tir da hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar Iran, sannan yay aba da sojojin kasar Iran kan duka mai karfin...
3- Shan miyagun kwayoyi, jike-jiken magungunan karfin maza da sauran nau’o’in kayan karfin maza da ake amfani da su yau da kullum. Don haka, akwai bukatar a lura da hadarin da zuciya take shiga; bayan shan ire-iren wadannan magunguna na karfin maza. A nan, ana tursasa zuciya ne tare kuma da tunzura ta ta yi aiki tukuru fiye da ikon da take da shi na lafiyarta, wanda hakan ko shakka babu, zai haifar mata da gagarumar matsala. Haka zalika, bugun zuciya yana kara sauri tamkar gudun doki, jini kuma yana hauhawa fiye da lafiyayyen hawa yayin saduwa da iyali. Kazalika, bugun numfashi yana karuwa; domin musayar iska fiye da ikon lafiyar da huhu da jijiyoyin jinni suke da shi, sannan...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce sake gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 dole ne, ya taimaka wajen haɗa kan ƙasa, kyautata mulki, da bunƙasa tattalin arziƙi. Ya buƙaci a gudanar da wannan aiki cikin adalci, gaskiya da kuma bisa ra’ayoyin jama’a gaba ɗaya. HOTUNA: Shugaban Gambiya ya kai wa iyalan Buhari ziyarar ta’aziyya a Daura Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN Gwamna Abba, ya bayyana haka ne ta bakin Shugaban Ma’aikatansa, Sulaiman Wali. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da saƙon maraba da baƙi a wajen Taron Sauraron Ra’ayoyin Jama’a na Yankin Arewa maso Yamma kan sake gyaran kundin tsarin mulki, da aka gudanar a Kano ranar Asabar....
Don haka nema tayi kira da jama’a kada suyi amfani da shi labarin daya zaman a kanzon kurege da ake ta yadawa,idan wani bayani suke bukata su tuntubi kafa da suka san ba zata yi zuki ta malle ba,ko kuma jami’an ma’aikatar ilimi ta kafar sadarwarsu ko kuma na, WAEC, da NECO. “An ja hankalin ma’aikatar ilimi ta tarayya akan wani labara ko rahoton da ya karade kafafen sadarwa na zamani,inda aka yi maganar cewar ban soke jarabawar WAEC ta shekarar 2025 da aka yi saboda an samu laifin aikata magudi lokacin da ake yin ta. “Ma’aikatar tace don haka tana sanar da jama’a cewa ta yi nesa da kanta,dangane da ita sanarwar ko labarin saboda kuwa ai na kanzon...
Shugaban Ƙasar Gambiya, Adama Barrow, tare da matarsa Fatoumata Barrow, sun ziyarci Jihar Katsina, inda suka yi ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari. Sun kai ziyarar ne a ranar Juma’a domin jajanta wa iyalan marigayin game da rashin da suka yi. Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN Wani mutum ya buɗe Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a ƙasar Sun sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Faskari, ya tarbe su a madadin Gwamna Dikko Umar Radda. Bayan sojoji sun yi wa Shugaba Barrow faretin ban girma, sun wuce Daura kai-tsaye, inda suka yi wa iyalan marigayin da kuma Mai Martaba...
Wannan yana cikin wani tsari na noma da aka kirkiro musamman don masu bukata ta musamman domin su dogara da kansu maimakon rokon hatsi ko neman taimako. Wannan yana cikin wani tsari na noma da aka kirkiro musamman don masu bukata ta musamman domin su dogara da kansu maimakon rokon hatsi ko neman taimako. Wakilinmu ya ziyarcj wata kebabbiyar gona dake cikin garin Kaduna, inda gungun wasu manoma da ke fama da lalurori daban-daban irin su makanta da gurguntaka da kurma, suka rungumi sabbin dabarun noma na zamani domin tallafawa rayuwarsu, musamman a wannan damina da aka shiga. Gonakin da wadanda makafi da guragu ne suke nomawa a duk shekara Sun bayyana cewa suna gudanar da nomansu ne ba tare...
Wasu yankuna a Jihar Legas, na iya fuskantar rashin wuta na tsawon kwanaki 25, yayin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), zai fara gyaran layin lantarkin Omotosho zuwa Ikeja ta Yamma mai ƙarfin 330kV. A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, aikin zai gudana kowace rana daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma, kuma za a kammala aikin a ranar Alhamis, 21 ga watan Agustan 2025. Wani mutum ya buɗe Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a ƙasar Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji Kamfanin, ya bayyana cewa gyaran zai shafi raba wutar lantarki a wasu wurare, kuma hakan na iya janyo ɗaukewar wuta. Sanarwar ta ce: “Abokan...
Ƙungiyar Rotary Club ta Kaduna Metropolitan ta raba kayan haihuwa fiye da 70 ga mata masu juna biyu a cibiyar kiwon lafiya ta Mando, Afaka. Da yake jawabi a wajen taron, shugaban Rotary Club na Kaduna Metropolitan kuma shugaban Rotary Action Group for Peace, Rotarian Luqman Babatunde, ya jaddada cewa kayan haihuwar ba na siyarwa ba ne, kyauta ce don tallafa wa mata masu juna biyu musamman marasa ƙarfi. Ya ce wannan tallafin ana gudanar da shi ne a wurare daban-daban a jihar Kaduna, yana mai jaddada cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya yin komai ba, shi ya sa ake buƙatar goyon bayan ƙungiyoyin sa-kai da na taimakon jama’a irin su Rotary. Ya bayyana cewa...
A wani lamari makamancin haka da ya faru a Jihar Taraba, a watan Yuli, 2025, da misalin karfe 11:45 na rana, jami’an ‘yansanda sun amsa kiran da aka yi musu na satar mutane a hanyar Wukari, jim kadan a bayan jami’ar tarayya ta Wukari. Wata farar mota kirar Toyota bas dauke da fasinjoji 17 daga Enugu zuwa Yola, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi musu kwanton bauna. Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi gaggawar kai farmaki inda lamarin ya faru. Da ganin tawagar jami’an tsaro na zuwa, sai masu garkuwar suka yi bar wadanda abin ya shafa suka gudu cikin daji. An ceto dukkan fasinjoji 17 ba...
Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) za ta buga wasan ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Afirika yau da ƙasar Moroko a filin wasa na Olympique da ke birnin Rabat na ƙasar Moroko, za a buga wasan da misalin ƙarfe 9 na dare agogon Nijeriya. Wannan ne karo na biyu da ƙasashen biyu za su haɗu a tarihi, sun haɗu a karon farko a shekarar 2022 a wasan kusa da na ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Afirika na mata, inda Moroko ta fitar da Nijeriya bayan bugun Fenarati, a wannan karon duka ƙasashen biyu na daga cikin waɗanda ake hasashen za su iya lashe kofin, duba da cewa babu kanwar lasa a cikinsu. Kano Pillars: Yaushe Kungiyoyin Kwallon...
Mujallar New York Times ta Amruka ta ce, harin da Iran ta kai wa sansanin sojan Amurka na Udaid, ya jazawa Amurkan asarar kudin da sun kai dala miliyan 111. Mujallar ta kuma ce; harin ya sa Amurka ta koyi darussan akan abinda zai iya faruwa idan har fada ya barke a tsakaninta da China ko Korea Ta Arewa.
Mataimakin shugaban kasar Rasha Nikolai Patrushev ya bayyana cewa; duk wani hari da za a kai wa yankin Kalligrad to zai fuskanci mayar da martani mai tsananin gaske. Mataimakin shugaban kasar ta Rasha ya kuma ce; A bisa akidar tsaro ta Rasha duk wani hari da za a kai mata, to zai sa kasar ta yi amfani da dukkanin makaman da take da su, domin mayar da martani akan abokan gaba, daga ciki har da makaman Nukiliya idan bukatar haka ta taso. Nikolai Patrushev wanda kamfanin dillancin labarun Sputnik ya yi hira a shi, ya ce;yankin Kallingrad kasar Rasha ne, don haka duk wani hari da za a kai masa zai sa su yi amfani da dukkanin karfin da suke...
Da yake bayar da cikakken bayani kan lamarin, Afolabi ya ce, “Wacce ake zargin, Abigail Brains Timothy, ta yi zargin cewa ta yaudari Fasto Adewusi ta hanyar karyar cewa tana da karfin da alaka da sayen biza da takardun aiki ga mutane 65, wadanda Fasto ya gabatar da ita a matsayin abokan huldarsa. “A karkashin wannan wakilcin na karya, ta sa shi ya sake mata kudaden da aka ambata na tsawon wani lokaci da nufin biyan kudin biza mai dauke da izinin aiki. “A ranar 25 ga Mayu, 2025, jami’an NSCDC, reshen Jihar Ekiti, da ke aiki bisa wani korafi da kuma tattara bayanan sirri, sun kama wadda ake zargin a garin Benin bayan da suka yi ta nemanta, bayan...
An kama wani matashi da ake zargi da tono gawar kakarsa ta ɓangaren uwa tare da sare kanta da nufin yin tsafin kuɗi a Jihar Naje. Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama mutumin mai shekaru 31 ne bayan dubansa ta cika a yankin. Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya cewa wanda ake zargin tare da abokansa da suka taimaka masa ya tabbatar musu cewa zai yi tsafin kudi ne da ƙwarangwal din tsohuwar. A cewar kakakin rundunar wanda ake zargin ya furta cewa yana neman tsafin ne don biyan bashin da ya kai sama da Naira miliyan biyu. Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato A ranar 19...
’Yan sanda sun kama wani mutum da ya buɗe Ofishin Jakadancin Ƙasar Indiya na bogi wani gidan haya, kuma yake gabatar da kansa a matsayin ambasadan ƙasar. Jami’an tsaron sun kama mutumin mai suna Harshvardhan Jain ne a ofishin nasa da ke kusa da Delhi, babban birnin ƙasar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito. Sushil Ghule, Babban Jami’in Rundunar ’Yan Sanda ta Musamman a yankin Uttar Pradesh, ya ce an ƙwace motocin alfarma masu ɗauke da lambar Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a hannun mutumin mai shekara 47. Ya bayyana cewa ambasadan bogin yana damafarar mutane da alƙawuran samun aiki a ƙasashen waje; musamman inda yake iƙirarin zama Jakada ko Mashawarci ga ka kamfanoni irin su “Seborga”...
A daidai lokacin da aka cika kwanaki 659 daga fara kisan kiyashin Gaza, sojojin Sahayoniya suna ci gaba da killace yankin da hana shigar da abinci da magani. Ma’aiktar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa ya zuwa wannan lokacin jumillar wadanda yunwa ta kashe sun kai 122 daga cikinsu da akwai kananan yara 83. Da jijjifin safiyar yau Asabar, majiyar asibitin “Nasr’ ta sanar da cewa wata jaririya ta yi shahada saboda rashin abinci mai gina jiki. Haka nan kuma ta ce, jaririyar ‘yar watanni 6 da haihuwa ta yi shahada ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma magani saboda takunkumin da HKI ta kakabawa yankin na Gaza. Babban jami’iin gudanarwa na ma’aikatar kiwon lafiya a...
A yayin da ‘yan sandan ke gudanar da bincike a yankin, rahotanni sun ce jami’an sun gano wata mata ‘yar Nijeriya a Coach A-2, Seat No. 27, tare da wani yaro da wata jakar balaguro kala-kala. Rahoton ya bayyana cewa bayan an yi mata tambayoyi, ta bayyana sunanta Doris daga Nijeriya kuma ta ce yaron da ke tare da ita, wanda ta bayyana sunansa Miracle, nata ne. RPF ta lura cewa “da aka yi mata tambayoyi a gaban shaidu masu zaman kansu, matar ta amsa cewa tana dauke da kayan maye.” Daga baya an kai ta zuwa gidan RPF a Panbel domin cikakken bincike. Rahoton ya lura cewa a cikin jakar balaguron, jami’an sun gano bakaken fakiti guda biyu da...
An kama wani matashi da ake zargi da tono gawar kakarsa ta ɓangaren uwa tare da sare kanta da nufin yin tsafin kuɗi a Jihar Naje. Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama mutumin mai shekaru 31 ne bayan dubansa ta cika a yankin. Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya cewa wanda ake zargin tare da abokansa da suka taimaka masa ya tabbatar musu cewa zai yi tsafin kudi ne da ƙwarangwal din tsohuwar. A cewar kakakin rundunar wanda ake zargin ya furta cewa yana neman tsafin ne don biyan bashin da ya kai sama da Naira miliyan biyu. Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato A ranar 19...

Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincikar Kwamishinan Sufuri Kan Karɓar Belin Dilan Miyagun Kwayoyi A Kano
Mambobin kwamitin sun haɗa da: 1. Barr. Aminu Hussain – Shugaba 2. Barr. Hamza Haladu – Mamba 3. Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba 4. Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba 5. Manjo Janar Sani Muhammad (Rtd.) – Mamba 6. 6. Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba 7. Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya Yayin da yake sanar da kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna matuƙar damuwarsa game da zargin da ke kan jami’in gwamnati, tare da jaddada aniyarsa ta yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da duk wasu munanan ɗabi’un da ba su dace ba a fadin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Wani abin karin farin ciki shi ne, yadda masu rauwa da tsaki a fannin, suka jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan yadda ya zabo ya kuma nada Dantsoho, a matsayin shugaban NPA, inda akasarin su, suka yi ittifakin cewa, zabo, bai zama zabar Tumun dare ba, musamman duba da irin dimbin ci gaban da yake ci gaba da samar wa a fannin, a cikin shekara daya kacal. Gyaran Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar: Tun bayan da ya dare karagar shugabancin NPA Dantsho ya lashi Takon, inganta ayyukan Tashoshin, inda ka fara da tattara bayanan ayyukan da ya kamata ayi da kuma fara yin aikin gadan-gadan, inda aka ware dala bilyan daya, domin fara gyran Tashar Tincan Island, ta Apapa, ta...
Duk da alƙawuran sojoji na kama fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji domin hukunta shi kan laifunan ta’addanci, har yanzu ɗan ta’addan bai daddara ba, a yayin da suke ci gaba da farautar sa shi da sauran manyan shugabannin ’yan bindiga da ke addabar ’yan Nijeriya. Dakarun sojin da aka tura ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma da sauran ayyukan soji a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Tsakiya, sun yi nasarar halaka manyan jagororin bindiga da dama, ciki har da wasu na hannun daman Turji a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, amma dai har yanzu Turji, wanda ke gudun ɓuya bai shiga hannu ba, duk kuwa da neman sa ruwa a jallo da jami’an...
Duk da alƙawuran sojoji na kama fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji domin hukunta shi kan laifunan ta’addanci, har yanzu ɗan ta’addan bai daddara ba, a yayin da suke ci gaba da farautar sa shi da sauran manyan shugabannin ’yan bindiga da ke addabar ’yan Nijeriya. Dakarun sojin da aka tura ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma da sauran ayyukan soji a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Tsakiya, sun yi nasarar halaka manyan jagororin bindiga da dama, ciki har da wasu na hannun daman Turji a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, amma dai har yanzu Turji, wanda ke gudun ɓuya bai shiga hannu ba, duk kuwa da neman sa ruwa a jallo da jami’an...

Araqchi Ya Jaddada Cewa; Karfin Kariya Da Makamai Masu Linzamin Iran Ne Suka Tilastawa Makiya Neman Tsagaita Wuta
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin kariya da makamai masu linzami na Iran ne suka tilasta wa abokan gaba neman tsagaita wuta Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Karfin kariya da makamai masu linzami na Iran, sune suka tilasta wa makiya neman tsagaita wuta. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen kasar ta Iran Abbas Araqchi ya fitar a lokacin da ya ziyarci gidan tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci nak are tsaron sararin samaniyar Iran, Manjo Janar Amir Ali Hajizadeh, inda ya mika ta’aziyyarsa da taya shi murnar rabauta da shahada tare da nuna girmamawa ga daukakarsa. Araqchi ya yi ishara da irin kokarin...
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Siriya ta tattara bayanan mutuwar mutane 1,400 a loardin Sweida na Siriya Siriya, Faransa da Amurka sun sanar da wata taswirar hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a Siriya, bayan tattaunawar da ba a taba ganin irinta ba a birnin Paris na Faransa, wadda ta hada ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya na Siriya Asaad al-Sheibani, da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot da manzon Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack. Sanarwar ta hadin gwiwa da aka fitar bayan taron na bangarorin uku, ta tabbatar da goyon bayan shirin mika mulki ga gwamnatin kasar Siriya da karfafa hadin kan al’umma, musamman a birnin Sweida da ke arewa maso...
Ya zargi gwamnatin da cewa ba ta dauki kwararan matakai na kawo babban gyara a fannin wutar lantarki ba, sannan ta gaza wajen nuna wani hobbasa game da lamarin ballantana har kuma ta dauki matakin gaggawa a cikin shekaru biyu da ta kwashe tana mulki. “Mun wuce rabin lokacin wannan gwamnatin, kuma miliyoyin ‘yan Nijeriya na ci gaba da caji wayoyinsu a tashoshin caji na hannu, suna kashe dubban naira wajen sayen man fetur na janareta domin samun wutar lantarki. “Ina hasken wutan lantarkin da aka yi wa ‘yan Nijeriya al’kawari? Me ya faru da alkawarinku? Kuma har yaushe ‘yan Nijeriya za su ci gaba da zama cikin duhu?” Ya sake dawo wa da alkawarin Tinubu a lokacin yakin neman...

‘Yan Jarida Da Suka yi Shahada A Gaza Sun Kai 232, Yayin Da Wadanda Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Yunwa Suka Kai 122
‘Yan jarida akalla 232 suka yi shahada sannan wasu 122 sun rasa rayukansu sabaoda masifar yunwa a yankin Zirin Gaza! Yakin kisan kare dangi da ake yi a zirin Gaza yana ci gaba da lakume rayukan Falasdinawa da dama a kowace rana, manya da kanana…ta hanyar jefa bama-bamai, kisa, killace yankin da kakaba masifar yunwa. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu daruruwa, ciki har da masu neman agaji, sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar al-Rimal da gidaje da sansanonin ‘yan gudun hijira a yankunan al-Amal, al-Tuffah, da al-Nasr, dake gabashi, arewacin Gaza. Hakazalika an sha kai...
Shugaban kasar Ukraine ya nuna sha’awar ganawa da shugaban Rasha kan neman hanyar warware rikicin da kasashen biyu ke fama da shi Ana ci gaba da yakin Ukraine musamman ta hanyar kai hare-hare da jiragen sama marasa matuka coiki. Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuka ciki guda 105 na Ukraine da aka harba zuwa yankuna tara, a tekun Azov, da kuma cikin kasar Rasha a daren jiya. Shugaban kasar Ukraine Zelenskyy ya ce: Kasarsa tana da kudade don sarrafa tsarin makamai masu linzami na Patriot guda uku kuma yana neman samar da karin kudade don sarrafa wasu bakwai na daban, gami da taimakon abokan huldarsa na kasashen Turai. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya...
Duk da cewa yanayin duniya ya yi babban sauyi, kamata ya yi a mayar da hankali ga hadin gwiwa, yayin da ake raya dangantaka tsakanin Sin da EU, kana bangarorin biyu su bi hanya mafi dacewa, da samun kyakkyawar makoma a shekaru 50 masu zuwa, da kuma kara samar da gudummawa ga dukkanin sassan duniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai magana da yawun jam’iyyar na wucin gadi ya ki janye ikirarinsa na cewa ADC na fuskantar manyan matsaloli a bangaren shari’a. “Muna da tabbaci kan doka a kowane mataki da muka dauka. Mun tabbatar mun rufe duk wata baraka da jam’iyya mai mulki za ta iya amfani da ita a kanmu,” ya kara da cewa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ficewar Amurka daga yarjejeniyoyin kasa da kasa da hukumomin duniya ba sabon labari ba ne, don haka mene ne abun mamaki idan ta bar UNESCO a karo na uku? Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar ya nuna cewa kashi 84.2 cikin dari na wadanda suka bayyana rayoyinsu ba su yi mamakin wannan matakin ba, lamarin da ke nuni da cewa, kasashen duniya sun saba da halayyar “kauracewar” Amurka. Wannan mataki na “Amurka ta zamanto farko” yana kara ingiza bukatar tsarin damawa da mabambantan bangarori na hakika cikin hanzari. Hujjar gwamnatin Amurka a wannan karon ta kasance a sarari, watau ta zargi UNESCO da ci gaba da zurfafa tabbatar da “mabambantan tsarin zamantakewa da al’adu” wadanda suka ci...
Yau Juma’a, 25 ga Yulin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karbi takardun nadi daga sabbin jakadun kasashe 16 da suka hada da Angola, da Benin, da Sudan ta Kudu, da Amurka, da Iran, da Chile da sauransu a Babban Zauren taruwar Jama’a dake nan birnin Beijing. Shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin tana darajanta dangantakar abota da al’ummomin duniya, kuma tana fatan kara hadin gwiwa a mabambantan bangarori, da kowace kasa bisa mutunta juna, da daidaito da samun moriyar juna. Ya ce Sin za ta ci gaba da fadada budadden tsarin tattalin arzikinta mai zurfi, tare da ba da damar yin amfani da babbar kasuwarta, ta yadda sabon ci gaban kasar zai zama dama ga kasashen duniya, kuma...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara aikin gina shaguna guda dubu daya a cibiyar kasuwanci ta Farm Centre da ke Kano, wanda zai lakume kudi Naira Biliyan Uku da rabi (N3.5bn), domin bunkasa kudaden shiga na cikin gida na jihar. Shugaban Kungiyar Hadaka kan Tsaro, Zaman Lafiya da Warware Rikice-rikice a Jihar Jigawa, Muhammad Musbahu Basirka, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a sakatariyar NUJ da ke Dutse, babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, hukumar EFCC ce ta mika filin hannun gwamnatin jihar Jigawa a matsayin wani bangare na dawo da kadarorin da jihar ta gada daga tsohuwar jihar Kano. Ya ce: “Wannan fili da ke a tsakiyar birnin Kano, na daga cikin...
Tsofaffin shugabannin da suka rasu bayan kammala wa’adinsu Nnamdi Azikiwe An haife shi a ranar 16 ga Nuwamba, 1904, Dakta Nnamdi Azikiwe, wanda aka fi sani da “Zik of Africa,” fitaccen dan siyasar Nijeriya ne kuma mai kishin kasa wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samun ‘yancin kai. Ya zama shugaban kasa na farko a Nijeriya daga 1963 zuwa 1966, bayan ya zama Gwamna-Janar a 1960 tare da Firai Minista Abubakar Tafawa Balewa. Azikiwe ya rasu yana da shekaru 91 a duniya a ranar 11 ga Mayu, 1996, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nijeriya, Enugu, bayan ya sha fama da rashin lafiya. Bayan shugabancinsa, Dakta Azikiwe ya kasance dan jarida na farko, haziki, kuma daya daga cikin wadanda suka...
Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta bayar ta yanke wa fitaccen ɗan Tiktok, Al-Ameen G-Fresh da mawaƙi Hamisu Breaker, hukuncin ɗaurin wata biyar a gidan yari bayan samun su da laifin wulaƙanta takardun Naira. Mai shari’a S.M. Shuaibu ne ya yanke hukunci, inda ya yi musu ɗaurin wata biyar a gidan yari, bayan sun amsa laifin da ake tuhumarsu a gaban kotu. Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Gusau Hukuncin ya biyo bayan tuhumar da Hukumar EFCC ta shigar da su a gaban kotu, bisa laifin wulaƙanta Naira. A cewar ƙarar, G-Fresh ya watsa kuma ya taka takardun Naira 1,000 har na Naira 14,000 yayin da...
A kokarin ta na inganta jin dadin al’umma, Gwamnatin jihar Jigawa ta gudanar da aikin tantance masu bukata ta musamman 200 a yankin Karamar Hukumar Birnin Kudu. A jawabin daya gabatar, shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba ya godewa gwamnatin jihar bisa kula da jin dadin masu bukata ta musamman a yankin da ma jihar baki daya. Dr. Builder Muhammad, yace a baya akwai masu bukata ta musamman mutum 61 da ke con gajiyar shirin a yankin amma a yanzu kuma gwamnatin jihar ta amince a kara 139 da za a zabo daga mazabu 11 na yankin. Builder, wanda ya sami wakilcin Kansila mai kula da shirin walwalar jama’a na yankin, Alhaji Ahmed magaji Bashir, yace Karamar Hukumar za...
Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta bayar da belin fitaccen ɗan Tiktok, Al-Ameen G-Fresh da mawaƙi Hamisu Breaker, bayan samun su da laifin wulaƙanta takardun Naira. Mai shari’a S.M. Shuaibu ne ya yanke hukunci, inda ya yi musu ɗaurin wata biyar a gidan yari, bayan sun amsa laifin da ake tuhumarsu a gaban kotu. Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Gusau Hukuncin ya biyo bayan tuhumar da Hukumar EFCC ta shigar da su a gaban kotu, bisa laifin wulaƙanta Naira. A cewar ƙarar, G-Fresh ya watsa kuma ya taka takardun Naira 1,000 har na Naira 14,000 yayin da yake rawa a shagon wata mai suna Rahma...
JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar Rasha mai suna Vostochiny Cosmodrome don isar da tauraron zawa inda take so a sararin samaniya, a yau Jumma’a 25 ga watan Yulin shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa kombon kasar Rasha a wannan cillawar ta isar da taurarin dan’adam da dama zuwa sararin samaniya. Banda tauraron dan’adam na kasar Iran ita ma kasar Rasha tana da taurarin dana dam guda biyu a cikin kumbon wato Ionosfera-M3 da M4, sannan da wasu 18 na wasu kasashe. Kafin haka dai wannan kumbon na kasar Rasha ya taba aika...
An takaita taro tsakanin kasashen turai da China a birnin Beijin zuwa ranar Alhamis kadai bayan da bangarorin biyu sun sami sabani a tsakaninsu kan al-amuran kasuwanci. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa an shirya gudanar da taron har na tsawon kwanaki uku amma kwotsom sai kasar China ta bukaci a takaita taron zuwa jiya Alhamis kadai. A nata bangaren shugaban tarayyar ta turai Ursula von der Leyen ta bayyana cewa, kasat China ce kadai take amfani da tsarinn kasuwancin da ke tsakanin bangarorin biyu, ta bada misali da cewa bambancin ribar da china take samu a cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai Euro biliyon 305.8 ko dalar Amurka biliyon 360 a shekarar da ta gabata...
Dakarun Runduna ta 3 ta ‘Operation Safe Haven’ masu wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun ceto wani yaro ɗan shekara 12 a Ƙaramar hukumar Riyom da ke jihar. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Manjo Samson Zhakom ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a. An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo A cewar rundunar, kawun yaron ne ya sayar da shi shekaru uku da suka wuce. Rundunar ta ce, an kuɓutar da yaron ne bayan wani samame da sojoji suka kai a maɓoyar miyagun da ke a Ƙaramar hukumar Riyom. Da yake...
Kamfanin kera manyan motocin dakon kaya na kasar Sin Sinotruk ya kaddamar da motocinsa kirar H2 mai dakon kaya marasa nauyi da ta H3 ta dakon kaya masu matsakaicin nauyi a kasar Kenya, tare da kamfanin CFAO Mobility a matsayin mai rarraba motocin a cikin gida. Babban manajan kamfanin CFAO Mobility na Sinotruk Sarfraz Premji, ya shaida wa manema labarai a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, an kera samfuran motocin ne ne don kawo sauyi ga masana’antar sufuri saboda suna iya daukar kaya masu nauyi, sannan an sa musu manyan tankunan mai, inda hakan zai rage bukatar yawan zuwa shan mai da kuma ba da damar daukar dogon lokaci ana tafiya, kana wannan zai rage yawan kudin da ake...
Bayan wannan mataki kuma, jihohi bakwai da suke da ruwa da tsaki kan harkokin wutar lantarkinsu, karkashin dokar 2023; na fuskantar matsin lamba a kan su sake duba kudaden da ake biya na wutar lantakin, bayan hukumar EERC ta fitar da wani muhimmin mataki na rage farashin wutar lantarkin na sashen Rukunin A (Band A), da kashi 24 cikin 100; wato daga Naira 209 zuwa Naira 160, tun daga 1 ga watan Agustan 2025. Da yake zantawa da LEADERSHIP, mai bai wa ministan wutar lantarki shawara na musamman kan dabarun sadarwa da kafafen yada labarai, Bolaji Tunji ya ce; idan jihohi suka zabi rage kudin wutar lantarki, ya zama wajibi su kasance cikin shiri, don samar da kudaden tallafin da...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gusau, Dokta Ibrahim Bello na Jihar Zamfara. Sarkin ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 71. An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe HOTUNA: Yadda Kwankwaso ya karɓi ’yan APC zuwa NNPP a Kano Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Ya ce Sarkin mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa don hidimta wa al’ummarsa. Shugaba Tinubu ya ce rasuwar Sarkin babban rashi ne, ba wai kawai ga mutanen masarautarsa ba, har da ƙasa baki ɗaya. Ya yaba da jajircewarsa, kyakkyawan shugabancin da sadaukarwarsa ga jama’a. Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyyarsa ga...
A ranar Alhamis 24 ga watan nan ne aka tantance tare da amincewa da biranen kasar Sin guda tara a matsayin biranen dausayi na kasa da kasa, yayin bude taron bangarorin da suka kulla yarjejeniyar Ramsar kan filayen dausayi karo na 15 (COP15), da aka gudanar a birnin shakatawa na Victoria Falls na kasar Zimbabwe, inda hakan ya kara adadin wadannan biranen a kasar Sin zuwa 22. Sabbin biranen tara da aka amince da su sun hada da Chongming na Shanghai, da Dali na lardin Yunnan, da Fuzhou na lardin Fujian, da Hangzhou na lardin Zhejiang, da Jiujiang na lardin Jiangxi, da birnin Lhasa na jihar Xizang mai cin gashin kanta, da Suzhou na lardin Jiangsu, da Wenzhou na lardin...
Babbar Kotun Jiha a Gombe mai lamba ta 3 ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutum uku bisa laifin haɗa baki da kuma kisan kai. Alƙalin kotun Mai shari’a Haruna Kereng ne ya jagoranci shari’ar, inda ya ce kotu ta sami Dauda Mohammed Abubakar (wanda aka fi sani da Agenda) da Kabiru Abubakar (Gwarei) da Ibrahim Suleiman da laifi a kan dukkanin tuhume-tuhumen da ake musu dangane da kisan Ibrahim Yahaya a unguwar Herwagana da ke Ƙaramar Hukumar Gombe a ranar 22 ga Afrilu, 2022. An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo An kashe mata da yara a sabon harin Filato Kotun ta ji cewa, mutanen ukun sun kai wa Ibrahim Yahaya...
Kwamitin ya nemi a mayar da sama da Naira miliyan 124, kusan dala 795,000 zuwa asusun gwamnatin tarayya, an kuma bayar da karin wasu kudade da suka hada da Naira miliyan 31.7 da dala 155,923.00, a matsayin wadanda aka kashe ba bisa ka’ida ba. An umarci ma’aikatar da ta kwato Naira miliyan 49.4 da aka biya, domin yin gyaran ba tare da bin ka’idojin sayen kayayyakin ba. Kazalika, an raba Naira miliyan 9.2 ga jami’an ofishin jakadancin, ba tare da cikakkiyar shaida ba. Haka nan kuma, an binciki bankin noma; kan basussuka kimanin Naira biliyan 75.6. Kwamitin ya umarci hukumar da ta buga jerin sunayen wadanda ake bi bashi a akalla a jaridu guda uku na wannan kasa tare da...
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023, ya karɓi ’yan APC zuwa jam’iyyar NNPP a Jihar Kano. Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta shafinsa na X, inda ya ce waɗanda suka sauya sheƙar ’yan jam’iyyar APC ne. An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo An kashe mata da yara a sabon harin Filato “Jiya rana ce mai muhimmanci,” in ji shi. “Na karɓi dubban mutane da suka bar jam’iyyar APC suka dawo NNPP.” Ya ce taron ya gudana ne a gidansa da ke Kano, inda ya yi wa sabbin mambobin maraba da kuma alƙawarin adalci da haɗin kai a cikin jam’iyyar. An wallafa hotunan taron a shafukan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Juma’a wasu ’yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka uku na Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie a garin Arondizogu, a Ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a Jihar Imo, inda suka kashe aƙalla mutane bakwai. An samu rahoton cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sun yi ta harbin mutanen yankin a ƙauyukan Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da dama. An kashe mata da yara a sabon harin Filato Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Waɗanda harin ya rutsa da su, masu shaguna ne da kwastomominsu da kuma masu wucewa. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa majiyarr PUNCH cewa, waɗanda lamarin ya...
Sai dai Sanatoci sun yi watsi da bayanin, inda suka zargi Ojulari da yin watsi da Majalisar. Kwamitin yana binciken tambayoyin tantancewa daga shekarar 2017 zuwa 2023, wanda ya nuna sabanin da ya kai Naira tiriliyan 210, ciki har da bashin da ba a tabbatar da shi ba na Naira tiriliyan 103. ‘Yan majalisar sun firgita cewa Naira tiriliyan 3 zuwa 5 ne kawai aka rubuta a cikin asusun ribar da kamfanin ya samu a cikin shekaru shida. “Wannan gayyatar ba tilas bace,” in ji Wadada. Ya kara da cewa kwamitin ba yana zargin hukumar ta NNPC da laifin sata bane amma ya jaddada cewa girman sabanin ya bukaci a yi karin haske kai tsaye. Ya bayyana rashin bayyanar Ojulari...
Aƙalla mutum 14; ciki har da mata da ƙananan yara ƙanana ne, suka rasu a wani sabon hari da aka kai a Jihar Filato. Harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a Gundumar Mangor da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos. Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu Waɗanda aka kashe suna kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar mako-mako da ke garin Bokkos, lokacin da wasu ’yan bindiga suka buɗe musu wuta. Wannan hari na zuwa ne wata guda bayan wani hari da aka kai wa wasu ‘yan ɗaurin aure daga Zariya a Jihar Filato, inda aka kashe su. Ƙungiyar Bokkos Cultural Development Forum (BCDF), ta tabbatar da faruwar...
Koda ya ke dai, a lokacin ‘yansanda sun yi nisa ban gudanar bincike, amma babu wanda suka iya kamawa, kuma ba a kara shigar da wata sabuwar kara a gaban kotu ba, duk tsawon wadannan shekarun. Wannan bukatar da Muyiwa ya biro da ita, tamkar bude wani sabon babi ne, kan batun hallaka manyan mutane a kasar, wadda za a iya cewa, tun daga 1999, har zuwa yau, amma shiru ake ji, kan daukar wani kwakwaran mataki. A wani taro a kwanan baya, babban Lauya SAN Cif Kanu Agabi, ya bijiro da zargin yadda ake gaza hukunta masu aikata manyan laifuka a kasar, inda kuma ake samun dogon jan kafa, kan shari’ar da ta shafi, marasa karfi a kasar. Wannan...
“Sauran su ne Lawan Haruna, Opurum Patrick, Agbo James da Georgewill Onwubiko da sauransu. “Shugaban PSC ya ce su tuna cewa su abokai ne ga kowa, kuma ya kamata a kowane lokaci su yi daidai da abin da ‘yan Nijeriya ke bukata. Ya kuma ba su tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da yin iya kokarinta don ganin an inganta yanayin aikinsu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa. Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya. Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi da kashe yara 2 a Bauchi Marigayin, wanda shi ne Sarkin Gusau na 16, ya ɗare kan karaga ne a shekara ta 2015, bayan rasuwar mahaifinsa. Gogaggen ma’aikacin gwamnati, Dr Ibrahim ya taɓa zama Babban Sakatare a tsohuwar jihar Sakkwato da ma jihar Zamfara. Ya yi mulkin ne na tsawon shekara 10 da ’yan watanni kafin rasuwar tasa. Da yake tabbatar da rasuwar, Kakakin Gwamna...
Ya ce tituna a Arewa sun lalace kuma gwamnati tana nuna rashin kulawa ga yankin. “Jiya da jirgi zan biyo na taho, amma aka ɗage jirgi daga ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare, sai na taho ta mota. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano abin takaici ne. Wannan aikin titi tun lokacin farkon hawa gwamnatin APC ake yinsa.” Kwankwaso ya kara da cewa ana gudanar da manyan ayyuka a Kudu cikin hanzari, amma an bar ayyuka masu mahimmanci a Arewa babu kulawa. “Muna jin ana gina titi daga Kudu zuwa Gabas. Muna maraba da ci gaba a ko’ina a Nijeriya. Amma gwamnati tana ɗaukar duk arzikin ƙasa ta zuba a ɓangare ɗaya kaɗai, ba ta yin aiki da...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin dakatar da kisan kare dangi a Gaza Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Aref ya jaddada cewa: Dole ne a kawo karshen kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankin Zirin Gaza cikin gaggawa ta hanyar daukar matakai na zahiri da kuma dauri daga kasashen duniya. Aref ya rubuta a shafinsa na X a jiya Alhamis cewa: “Mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba saboda yunwa sakamakon hana isar da abinci ga al’ummar Gaza da aka zalunta ya kasance tare da yin shiru na kunya daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.” Ya kara da cewa: “Dole...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Babu shakka Iran za ta ci gaba da inganta sinadarn Uranium Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana a jiya Alhamis dangane da tattaunawar da Iran za ta yi da kungiyar kasashen Turai da za a yi a yau Juma’a a birnin Istanbul na Turkiyya cewa; Za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a cikin kasar Iran, kuma kasar ba za ta yi watsi da wannan hakkin na al’ummar Iran ba. A cikin bayanin da ya yi a gefen ziyarar da ya kai ga iyalan shahidan Laftanar Janar Baqiri, Araqchi ya kara da cewa; Ko da yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da shirinta...
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace yara da yin garkuwa da su sannan ta kashe su. Rundunar ta ce wadannan kananan yara biyu mata ne ‘yan shekara bakwai, lamarin da ya jawo tarzoma da kona coci. Kakakin Rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya shaida wa manema labarai haka a Bauchi ranar Alhamis. NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso Wakil Ya bayyana cewa an samu rahoton faruwar lamarin ne a ranar 22 ga watan Yulin 2025, da misalin karfe 3:00 na rana. Ya...
Ya ce, nan da shekarar 2030 za a bukaci hekta miliyan 300 domin samar da bukatar abinci. Don haka ne ya ce taken taron ranar yaki da kwararowar hamada na 2025 na da matukar tasiri domin tabbatar da daukan matakan da suka dace wajen kiyaye hamada da gurbacewar muhalli. A cewarsa, yunkurin zai tunkari manyan kalubale kamar matsalar tattalin arziki da karancin abinci, karancin ruwa, da sauyin yanayi. Lawal ya jaddada cewa cimma muradun ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya ba zai yuwu ba idan ba tare da kare muhalli da kuma kula da filaye da albarkatun kasa ba. Ya kara da cewa gwamnati na ba da fifiko ga al’amuran muhalli kuma ta samar da cibiyoyi, manufofi, tsare-tsaren ayyuka,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati. Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun jari a inda aka tura su, wasu kuwa komawa garuruwansu suke yi bayan sun kammala. NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga jikin mutum DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan irin damar da masu yi wa kasa hidima suke da ita a garuruwan...
Kashe- Kashen 2025 Ya Fi Na 2024 Alkaluman bincike sun bayyana cewar ‘yan ta’adda sun dauki rayukan mutane a rabin wannan shekarar fiye da na shekarar 2024 da ta gabata kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yancin Dan- Adam ta kasa ta bayyana a wannan watan. Kamar yadda alkaluman suka nuna, akalla mutane 2, 266 ne suka bakunci lahira a hannun ‘yan ta’adda a rabin shekarar 2025, idan aka kwatanta da mutane 1, 083 a rabin farko na shekarar 2024 da kuma mutane 2, 194 a bakidaya shekarar. Rundunar sojojin Nijeriya na fafatawar yaki da mayakan Boko- Haram da sauran ‘yan ta’adda a Arewa Maso- Gabas, ta’addanci da garkuwa da mutane a Arewa Maso- Yamma, hare- haren makiyaya da manoma...
Kasashen Iran da Bangaladesh sun yi kakkausar suka ga cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, tare da yin kira ga al’ummar musulmi da su dauki matakin gaggawa na dakatar da yakin kisan kare dangi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi wa al’ummar Palasdinu. A wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya Alhamis, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Bangladesh Md. Touhid Hossain sun yi musayar ra’ayi kan halin da ake ciki a yankin. Araghchi ya yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila take tabkawa, musamman manufofinta na hana Falasdinawa abinci da Ruwan sha. Ya kuma jaddada muhimmancin kiran taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kuma samar...
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fada a wannan alhamis cewa yana shirin aikewa da tawaga zuwa kasar Senegal a cikin watan Augusta domin tattauna yadda aza magance matsalar basussukan da ke kan kasar da kuma fara tattaunawa kan tsarin sabon shirin lamuni. Kasar Senegal na fama da bashin biliyoyin daloli da gwamnatin da ta shude ta karba, lamarin da ya sanya asusun lamuni na duniya IMF ya dakatar da shirin ba da lamuni ga kasar. A nasa bangaren kuma, wani mai magana da yawun IMF ya ce, “Asusun na bukatar karin bayanai kafin ya karfafa kimanta halin da ake ciki na basussukan kasar Senegal, sannan yana bukatar yarjejeniya kan muhimman matakan gyara.” Ya kara da cewa, “Da...

Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
Da yammacin yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya shugabanci taron tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da EU karo na 25, tare da shugaban majalisar EU Antonio Costa, da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen a nan birnin Beijing. A yayin taron, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da EU suna da moriya iri daya wadda babu rikici a cikinta. Bisa yanayin sauyi da ake ciki a halin yanzu, ya kamata Sin da EU su kara yin hadin gwiwa. Kuma kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da bangaren EU a fannonin cinikayya, da zuba jari, da kiyaye muhalli, da kimiyya da fasaha da sauransu, don tabbatar da samar da kayayyaki a tsakaninsu yadda ya kamata, da...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa yana yawan karanta rantsuwar kama aiki da ya yi domin tunatar da kansa nauyin da ya dauka na yi wa al’umma hidima bisa gaskiya da amana. Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba bayan nadin sabon shugaban karamar hukumar Gumel. A wajen bikin da aka gudanar a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Dutse, Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa rayuwa na da kurarran lokaci, don haka ya kamata shugabanni su kasance masu tsoron Allah da kuma sanin nauyin da ke kansu. “Rayuwa ba ta da tabbas, hakazalika shugabanci ba wasa ba ne”....
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali wajen gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar. Kwankwaso ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen taron bana kan shawarwari na masu ruwa da tsaki a Jihar Kano. Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71 A cewarsam Tinubu ya yi watsi da halin da yankin arewacin ƙasar ke ciki wajen gina Kudancin Najeriya da kuma samar musu da kayan more rayuwa. “Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa...
Gwamnatin Jihar Yobe ta raba tallafin kuɗi ga iyalan ’yan banga da suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka samu raunuka a bakin aiki. Kuɗaɗen wanda Daraktan ayyuka na musamman, Muhammad Alhaji Baba ya miƙa a madadin sakataren gwamnatin jihar sakamakon umarnin da Gwamna Mai Mala Buni ya bayar na a yi hakan. Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71 An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa Wannan shiri dai wani ɓangare ne na shirin jin daɗin jama’a na jaha ga jami’an tsaro domin tabbatar da cewa, iyalan ’yan banga da abin ya shafa sun samu tallafi. A ƙarƙashin shirin, kowane dangin ɗan banga da ya rasu ya karɓi Naira dubu ɗari ₦500, yayin da waɗanda suka jikkata...

Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar
A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, bisa hadarin jirgin saman fasinja da ya auku a kasar, wanda ya haddasa rasa rayuka da dama. Kafar dillancin labarai ta “The Russia Today”, ta hakaito kwamitin binciken hadarin na cewa, dukkanin mutanen dake cikin jirgin saman mai lamba An-24 da ya yi hadari a yau Alhamis a yankin Amur na kasar Rasha sun rasu. An ce, jirgin na dauke da fasinjoji 43, da kuma matuka da masu bayar da hidima 6. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Idan har aka samu nasarar karɓar wannan gasa, za ta buɗe sabon babi a harkar wasanni da kasuwanci a Nijeriya, tare da samar da damammaki ga matasa da masu sana’o’i, da kuma ƙara haskaka ƙasar a idon duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta yi kira ga gwamnatin sojan jamhuriyar Nijar da ta saki tsohon shugaban kasar Muhamad Bazum, wanda ake tsare da shi tun lokacin juyin mulkin watan Yuli na 2023. Kungiyar ta kuma ce, ci gaba da tsare Muhammad Bazum da ake yi ba tare da yi masa shari’a ba, ya sabawa doka da kuma take dokokin kasa da kasa na sharia. Bayan juyin mulkin na 2023, shugabannin soja sun yi alkawalin gabatar da Bazum a gaban kotu domin yi masa shari’a bisa zargin cin amanar aksa. A 2024, kotun musamman da aka kafa ta cirewa tsohon shugaban kasar rigar kariya, da hakan ya zama tamkar share fage domin yi masa sharia,sai dai...
Kafafen watsa labarun HKI sun ce wani mutum a cikin motar da yake tukawa ya nufi kan ‘yan sahayoniya a mahadar “Hahsrun” a kusa da “Kafar-Yona”dake yammacin Tul-Karam. Bayan da matumin ya take ‘yan sahayoniyar ya fice daga yankin ba tare an iya tsayar da shi ba. Majiyar ta kara da cewa; 9 daga cikin ‘yan sahayoniyar da su ka jikkata sojoji ne. Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; Wanda ya take sojojin ya iya gudu daga wurin, ba tare da an tsayar da shi ba. Ita kuwa jaridar ‘ Yasrael Home” ta bayyana cewa; An baza ‘yan sanda a wurin da aka kai hari, domin gano inda maharin yake. Kungiyoyin Falasdinawa sun yi maraba da wannan harin,...
Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen dabbobi. Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da nono ta hanyar kyautata da kula da lafiyarsu, domin rage dogaro da waje samar da nama da kuma nono.” Haka nan kuma ministan na noma ya kara da cewa; Kara yawan dabbobin da ake samarwa a cikin gida,wata lalura ce ta tattalin arziki, da kuma kishin kasa. Ministan Noma na Iran ya kuma kara da cewa, ma’aikatar tasu tana kokarin ganin mayar da Iran zama cibiyar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin. Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.” Motocin suna dauke da kayan abinci, ruwa da magani a cikin kasashen Jordan da Masar. A wani bayani da ofishin gwamnatin Gaza ya fitar a yau Alhamis, a cikin yankin Gaza duk wani abinci, ruwa da magani duk sun kare, don haka a halin yankin yankin yana da bukatuwa da buhunan filawa 500,000 a kowane mako. An shiga kwanaki 145 da HKI ta rufe dukkanin mashigar...
Shahararren ɗan kokawa ɗan ƙasar Amurka mai ritaya Terry Gene Bollea wanda aka fi sani da Hulk Hogan ya rasu yana da shekara 71 a duniya. A cewar TMZ da sauran rahotanni, likitoci sun mayar da martani a gidansa na Clearwater, da ke Florida da sanyin safiyar Alhamis kan Hulk Hogan ya kamu da bugun zuciya da ya yi ajalinsa. An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Daga nan an ɗauki Hogan da wuri aka saka shi cikin motar ɗaukar marasa lafiya. Duk da damuwa na kwanan da aka bayyana game da lafiyarsa – ciki har da larurar wuyansa a farkon wannan shekara, matarsa Sky ta...

Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
Kwanan nan, darektar zartaswa ta hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD, Anacláudia Rossbach, ta yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a hedkwatar hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD dake Nairobi, babban birnin Kenya. Yayin da aka ambato sakamakon da ya fi jawo hankali da Sin ta samu yayin kyautata kauyuka zuwa matsayin birane da garuruwa, Rossbach ta bayyana cewa, Sin ta cimma nasarar kawar da talauci ga mutane miliyan 800, da kuma tafiya a kan hanyar kyautata kauyuka zuwa birane da garuruwa, kuma wannan darasi ne da ya cancanci kasashen Afirka wadanda suke fuskantar kalubalen kyautata kauyuka zuwa birane su yi koyi da shi. Ta ce, nan da...
A cewar ministan, shi da sauran abokan aikin sa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin ƙaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a Jihar Katsina. Cibiyoyin da aka ƙaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sababbin cibiyoyin maganin ciwon daji guda shida a manyan Asibitocin Koyarwa na Tarayya a ƙasar nan. Wannan cigaba wani muhimmin mataki ne wajen rage wahalar da marasa lafiya ke fuskanta wajen samun ingantacciyar kulawa, da kuma hana fita ƙasashen waje don neman magani. Gwamnatin ta tabbatar da cewa sauran cibiyoyin da suka rage za su kammala nan ba da jimawa ba domin cika alƙawarin samar da ingantaccen tsarin...
Aikin gina tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin ya samu gagarumin ci gaba sosai, inda gwamnatin kasar Sin ta sanar a jiya cewa, a ranar 18 ga watan Disamban bana, za a kaddamar da manufar kafa “kwastam mai zaman kansa a duk faɗin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan” a hukumance, wadda ke nufin saukaka bincike da ragewa ko soke haraji. “Ana iya cin moriyar manufofin ba da fifikon harajin kudi a tsibirin Hainan”, sannan “mu’amalar Hainan da kasashen duniya za ta kasance cikin ’yanci da lumana”. A ra’ayin jama’a na kasa da kasa, wannan wani muhimmin mataki ne ga kasar Sin na kara fadada bude kofa ga ketare, wanda ba bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar...
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa. Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Majiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin...
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa. Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Majiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin...
An cimma matsaya kan zaɓensa bayan wata ganawa da aka yi a Abuja tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC. Ana sa ran manyan shugabannin jam’iyyar za su tabbatar da naɗinsa a yau Alhamis. Farfesa Yilwatda, ya fito ne daga Jihar Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da suke da alhakin riƙe kujerar shugabancin jam’iyyar. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar sun ce kasancewarsa Kirista zai taimaka wajen daidaita shugabanci, duba da cewa shugaban ƙasa da mataimakinsa Musulmai ne. Shugabannin jam’iyyar na fatan Farfesa Yilwatda zai kawo sabon salo, tare da haɗa kan jam’iyyar kafin tunkarar zaɓe mai zuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Wani jrigin saman fasinjoji mallakin kasar Rasha da ke dauke da mutum 50 ya yi hatsari a kusa da yankin Amur na kan iyakar kasar China. Kafar yada labarai ta Sky News ta rawaito cewa jirgin wanda ke dauke da fasinjoji, ciki har da kananan yara biyar da kuma ma’aikatan jirgi su shida, ya fadi ne ranar Alhamis ba tare da ko mutum daya ya rayu ba. “Ma’aikatan ceto sun gano wasu sassan jirgin na ci da wuta,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito jami’an ceton na cewa. Reuters ya kuma ce jirgin wanda mallakin kamfanin Angara Airlines ne, ya fadi ne a kusa da Tyndra, wani gari da ke yankin na Amur, bayan hanyar da yake...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe. Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu. Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi 48 ne a fadin kananan hukumomin da lamarin ya faru. Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Dr Goje yan kuma ce bala’in ya shafi gidaje 1,264, tare da raba mutum 5,022 da muhallansu. Shugaban ya kuma ce hukumarsa tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da tallafi...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe. Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu. Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi 48 ne a fadin kananan hukumomin da lamarin ya faru. Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Dr Goje yan kuma ce bala’in ya shafi gidaje 1,264, tare da raba mutum 5,022 da muhallansu. Shugaban ya kuma ce hukumarsa tare da hadin gwiwar kungiyar bayar da tallafi...
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza. Mataimakin babban...

Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF a Falasdinu, ya tabbatar da cewa: Abin da ke faruwa a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar wasu ma’aikatan jin kai da dama da suka yi balaguro zuwa yankunan da ake fama da rikici, da bala’o’i, da wuraren yaki a duniya, kuma dukkansu, ba tare da togiya ba, sun amince cewa, ba su taba ganin wani yanayi mai kama da abin da ke faruwa a Gaza ba. Abu Khalaf ya yi nuni da cewa: Mutanen yankin Zirin Gaza sun fara fama da yunwa, sannan...

Ministan Lafiya Na Kamaru: Hadin-Gwiwa Ta Fuskar Kiwon Lafiya Ta Shaida Zumunci Mai Karfi Tsakanin Kamaru Da Sin
Ministan lafiya na kasar Kamaru, Manaouda Malachie ya bayyana jiya Talata 22 ga wata a Yaounde cewa, hadin-gwiwar Kamaru da Sin a bangaren kiwon lafiya ta haifar da babban alfanu ga jama’ar Kamaru, kana alama ce dake shaida dangantakar kut da kut gami da dadadden zumunci tsakanin jama’ar kasashen biyu. A wajen bikin cika shekaru 50 da kaddamar da hadin-gwiwar Sin da Kamaru ta fuskar kiwon lafiya wanda aka yi a jiya Talata a birnin Yaounde, minista Malachie ya gabatar da jawabi yana mai cewa, hadin-gwiwar kasashen biyu ta fuskar kiwon lafiya ta shaida cewa, kwalliya za ta iya biyan kudin sabulu, idan aka raya hulda mai aminci, da sahihanci kuma bisa muradu iri daya tsakanin kasa da kasa. Gwamna...
Wani mummunan al’amari ya faru a Ƙaramar Hukumar Fika da ke Jihar Yobe, inda wata mata mai shekara 35, ta kashe mijinta da itace bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu a kan abinci. Rahotanni sun nuna cewa matar wacce ’yar garin Abba ce, ta ɗauki katon itacen girki ta rafka wa mijinta bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan sama da mutum 100 Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Dungus Abdulsalam, ya ce bayan faruwar lamarin, an sanar da ’yan sanda kuma nan take suka kama wacce ake zargi. Marigayin ya rasu nan take, kuma ya bar mata biyu da...

Gwamantin Kasar Siriya Ta Rufe Hanyoyin Shiga BirninSiweida Na Kasar Saboda Ci Gaba Da Bullar Rikici
Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun rufe hanyoyin zuwa birnin Sweida bayan sake bullar wani tashin hankali Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin Sweida da ke kudancin kasar tun daga wayewar garin ranar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin. A halin da ake ciki, ana ci gaba da kokarin da ake yi na cikin gida da waje na wanzar da tsagaita bude wuta da kare fararen hula. Ana zaman dar dar a lardin Suwayda da ke kudu maso yammacin kasar Siriya, inda dakarun gwamnati ke ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin tun da safiyar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza...
Gwamnatin Borno na ci gaba da ƙoƙarin ganin ta samo mafita domin iya biyan sabon albashin ma’aikata kamar yadda aka tsara a matakin ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp