Yunkurin Philippines Bai Kai Gaci Ba A Tekun Kudancin Kasar Sin
Published: 29th, May 2025 GMT
Kwanan baya, a yayin da ake gudanar da taron kolin ASEAN karo na 46, wasu jami’an diplomasiya na kasar Philippines sun yi shelar daddale wasu yarjejeniyoyi tare da kasar Sin don kiyaye zaman lafiya a tekun kudancin kasar Sin. Duk da haka Philippines ta rika daukar matakan takala a zahiri. Kuma abun da kasar ta Philippines ta yi ya saba da ma’anar zaman lafiya.
Bayan da gwamnatin Marcos ta zartas da shirin doka na wai dangane da tekun kudancin kasar Sin daga bara zuwa yanzu, ta kasance a matsayin dillaliyar Amurka da wasu kasashen da ba su cikin yankin. Ta dauki matakan kashi kai don tada zaune tsaye a tekun kudancin kasar Sin da kirkira labarun shafa wa kasar Sin kashin kaji, ta kuma yunkura don tabbatar da hukuncin da aka yanke ba bisa doka ba game da tekun kudancin kasar Sin, ta hanyar kafa dokokin cikin gida. Amma a karshe dai ba ta cimma burinta na sake mulkin tsibirin Huangyan da sauran tsibiran Zhongsha ba, haka kuma ba ta cimma burinta na mamaye sashen tudun teku na Xianbin Jiao da na Tiexian Jiao da na Ren’ai Jiao karkashin inuwar tsibiran Nansha, inda babu wani dan Adam da ke da zama a wuraren.
Yau mako guda da ta wuce, kasar Sin da kungiyar ASEAN sun kammala tattaunawa kan yankin ciniki cikin ’yanci karo na 3, lamarin da ya samar da sabuwar dama wajen raya yankin. A daidai wannan muhimmin lokaci, Philippines ta yi takala da yunkurin danne kasar Sin bisa taimakon Amurka, kuma abin da ta yi bai dace da fatan al’ummar Philippines ba, kana ba zai samu goyon baya daga sauran kasashen da ke tekun kudancin kasar Sin ba, kana ba ya tafiya tare da kokarin yankin na samun zaman lafiya da ci gaba. A karshe dai, Philippines ba za ta samu kome ba sai dai salwantar da kanta cikin takarar da Amurka da sauran manyan kasashe suke yi. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a tekun kudancin kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Tace Tawagar Kwararru Daga Hukumar IAEA Zata Ziyarci Kasar Nan Ba Da Dadewa Ba
Tawagar kwararru daga hukumar makamashin Nukliya IAEA zata ziyarci kasar Iran nan ba da daewa ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar a bangaren sharia da kuma harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka.
Ya kuma kara da cewa tawagar zata tattauna da Jami’an gwamnatin kasar Iran kan yadda mu’amalar hukumar zata kasance da Iran. Gharibabadi ya bayyana cewa idan kasashen yamma sun yi kokarin amfani da shrin SnapBack na yarjeniyar JCPOA zasu gamu da maida martani mai tsanani, sannan ya kara da cewa mu’amala da hukumar IAEA da kasar Iran zata sauka saboda amfani da karfi kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran wanda Amurka da HKI suka yi a kallafeffen yaki na kwanaki 12 a cikin watan yunin da ya gabata.
Mataimakin ministan ya bayyana cewa, Iran zata ci gaba da kasancewa cikin yarjeniyar NPT mai hana yaduwar makaman nukliya a duniya. Amma dokar da Majalisar dokokin kasar Iran ta kafa ta jingine hulda da hukumar IAEA ya sa Iran za ta sanya hulda da hukumar takaitacce shi dimma tare da wasu sharudda guda biyu. Gharib abada ya fadawa yan jaridu a birnin NewYork a ranar Laraban da ta gabata kan cewa tawagar ba zata kai ziyara cibiyoyin makamashin nukliya na kasar ba. Sannan ya kammala da cewa hukumar makamashin nukliya na kasar Iran na lissafin irin asarorin da hare-hare Amurka suka yiwa cibiyoyin Nuklkiyar nkasar A Esfahan, Natansa da kuma Fordo.