Yemen: Wuce Gona Da Irin HKI Ba Zai Sauya Mana Ra’ayi Akan Ci Gaba Da Taimaka Wa Gaza Ba
Published: 29th, May 2025 GMT
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.”
Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa; Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai yi tasiri akan matsayarmu ta taimakawa Gaza ba,sannan kuma ya kara da cewa; Abinda Isra’ila makiya ke son yi, shi ne a kyale ta yi yadda take so da Falasdinawa ba tare da an mayar mata da martani ba daga kowace kasa ta musulmi.
Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Matsayar da kasar Yemen take dauka na taimakawa Falasdinawa, matsaya ce ta addini.”
Haka nan kuma ya kara da cewa; Daga cikin manufofin harin na Isra’ila a filin saukar jiragen sama na Sanaa da akwai dakatar da jigilar mahajjata, amma ba za su yi nasara ba.”
Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya yi ishara da wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki,sannan kuma ya ce; A wannan lokacin wahalhalun na mutanen Falasdinu sun fi na baya, domin suna fuskantar yunwa da kuma ci gaba da kai hare-hare da Isra’ila take yi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi tsohon shugaban kasar Barack Obama da cin amanar kasa tare da yin kira da a yi masa shari’a
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi magabacinsa, Barack Obama da cin amanar kasa, inda ya bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya kan wani rahoton sirri da ya nuna cewa; Jami’an gwamnatin Obama sun murguda bayanai game da katsalandan din Rasha a zaben Amurka na shekara ta 2016.
Kalaman na Trump sun zo ne yayin wani taron manema labarai a ofishin Oval, wanda shugaban kasar Philippines Ferdinand Marcos ya halarta. Yana cewa:”Bisa ga abin da ya karanta…tsohon shugaba Obama ne ya fara wannan badakalar,” ya kara da cewa Obama shi ne “shugaba” na abin da ya bayyana a matsayin “gungun maciya amana.”
An karfafa wadannan zarge-zarge ne bayan da Daraktar hukumar leken asirin kasar Tulsi Gabbard ta aike da masu gabatar da kara ga ma’aikatar shari’a dangane da wani rahoto da aka fitar a ranar Juma’ar da ta gabata da ke tabbatar da cewa jami’an gwamnatin Obama na da hannu wajen kirkirar bayanan sirri da nufin share fagen juyin mulki na tsawon shekara daya kan shugaba Trump.